ZAN SOKA A HAKA

By queenbk2020

392K 23.9K 2.2K

#5 tausayi June 2020. #3 tausayi 20 June 2020. #1 munafurci #8 hausa novel. #2 tear drop june 2021. More

page 1
Page 2
page 3
page 4
page 5
Page 6
page 7
Page 8
Page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 1⃣4⃣
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
pahe 22
page 23
page 24
page 25
page 26
page 27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
Page 34
page 35
page 36
AUTHOR'S NOTE
page 37
page 38
page 39
page 40
page 41
page 42
page 43
page 44
page 45
page 46
page 47
page 48
page 49
page 50
page 51
page 52
page 53
page 54
page 55
page 56
page 57
page 58
page 59
page 60
page 61
page 62
page 63
page 64
page 65
page 66
page 67
page 68
page 69
page 70
page 71
Page 72
page 73
page 74
Page 75
Page 76
page 78
page 79
page 80
page 81
page 82
page 83
page 84
page 85
page 86
page 87
page 88
page 89
page 90
The end and thanks.

page 33

4K 239 0
By queenbk2020

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨






💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼








🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )






Page3⃣3⃣




*KAFIN KIYI RUBUTU KIYI NAZARI AKAI, KUMA KAFIN KIYI MAGANA KIYI TUNANI AKAI, YIN TUNANI ZAI RABA KI DA YIN ABIN DANA SANI A RAYUWA.*
                          QUEENBK.








Misalin ƙarfe 2:30pm zarah tazo gidan, tuni dama ta daɗe tana zuwa, bayan ta gaishe da Ammie dake falo, Ammie tace "kai kaji zarah sai kace baƙuwa ki wuce ciki mana suna ɗaki" ƴar dariya tai tace "to ammie".

Tashi tai ta wuce ɗakinsu mimi, mimi na zaune kan gado tana rubutu a littafinta, ita kuma Asmah na ƙasa tana cin ɗan wake, jefi jefi suna ƴar hirar su, zara ta turo ƙofa a hankali batai sallama ba saboda so take tayi suprising ɗinsu, tana leƙo kai da Mimi suka fara haɗa ido, Mimi har ta buɗa baki zatai magana zarah tai sauri tai mata alamun tai shiru da hannunta, ɗaga mata kai mimi tai tana murmushi, ita ko Asmah ba tasan meke wakana ba da yake ta juya ma ƙofar baya ne, ga ɗan wakenta yana kai mata karo, a hankali Zarah ta tako har inda take, tana zuwa ta daidaici bayan Asmah ta ɗaka mata duka.




Asmah ta saki wata ƙara tana dafe gurin, juyowa tayi tana kukan shagwaba ganin Zarah ce me wannan aikin, gaɓa ɗaya Zarah da Mimi suka sa dariya.




Asmah tace "Amman Allah sai ya bimun haƙƙi na wallahi, haka kawai dan mugunta ki wani dake ni, bayan na gaya maki banson duka, yanzu da kinsa na shaƙe fa kinga abinci nake ci ko, wai ke Zarah duk na kusa dake ne sai yasha wahalar wannan hannun naki mai shegen zafi, nikam ina tausaya ma mijinki"

Nan ma suka ƙara sa dariya,
Kana Zarah tace "kar ki tausaya mashi, shi ba zai ji komai ba duk cikin so ne ai"

Asmah ta cigaba " wannan matsalar kuce, ni dai bashi kika ci zan rama ne yarinya" sannan tayi ƙwafa ta haɗe rai ta cigaba da jefa ɗan wakenta.


Zarah ta zauna gefan gado ta cire gyalanta ta
aje jakar ta kana tace " ya haƙuri Asmah dan Allah, bansan zaiyi zafi sosai ba" ta faɗa tare da zaro halshe tana mata gwalo.


"Ba wani in banda iskanci kinsan da ƙarfi kika mun sannan ki wani ce baki son zai yi zafi ba ko? Rashin mutunci kawai"

"To ya haƙuri dan Allah, na tuba bazan kuma ba kinji?"
Mimi ma tace "ya haƙuri Asmah duk cikin wasa ne tunda kuma ta baki hakuri au shikenan"


Asmah tace "ai wannan bata son wasa ba, yanzu na mata haƙuri anjima karawa zatai a makaranta fa kullum sai tasa kafaɗata ciwo tsabar duka"
dariya Mimi tayi, Zarah kam hannu tasa ta kama kunnuwanta alamun ban haƙuri duk da tasan sarai Asmah cikin wasa take, can tace nasan yadda zan yi maki a ranta a fili kuma tace

"To Mimi ni bara na tashi na tafi dama ya Aliyu ne ya aiko ni, to naga wacce aka aikenin gunta she's not in the mood, so i better go" ta faɗa tare da ɗaukar gyalanta tana tashi, da sauri Asmah tasa hannu ta jawo ta inda take zaune tace

"Ina zaki dan Allah, dawo ƙawar arziƙi na yafe maida wuƙar plz"
gaba ɗaya suka sa dariya.


Zarah tace "hahahaah dama nasan lagonki"
Asmah ta ɗaka mata duka a cinya tare da faɗin "ba kare bin damo na rama, kinga anyi 1 1 kenan"
Zarah cikin ihun zafi tace "Amman Asmah naki yafi zafi"
Asmah tace "Ramuwar gayya ai tafi ta gayya zafi"
Mimi tai dariya.



Asmah tace
"yanzu dai kan wannnan zura hannunki muci" ta faɗa tare da kamo hannunta tana sa mata fork a ciki tace "ci",
ajewa tayi tana faɗin "ke a ƙoshe nake" wata uwar harara Asmah ta galla mata tare da faɗin "wasa kike wallahi, ke da na sanki da ɗan wake ai duk sona da ɗan wake kince mun kau nan, sannan kice bakici"

Tace "jiya da daddare shi naci, yanzu kuma ina ON ne kuma kinsan yadda in ina yi ban cika cin abinci ba ko?"


"Kyaji dashi ciwon ajali a ɗan yatsa, ke yau ko blood bank ne ya fashe ba damuwa ta bace all i know sai kinci ɗan waken nan" ta faɗa tare da maida mata fork ɗin a hannunta.



"Yau naga ƙarfin hali wai mai hali yana bara" Zarah ta faɗa tate da kallon Mimi.

Mimi tace "gwanda ma kici ni ba shigar maki zan ba, ki daina mun fuskar tausayi"

Suka sa dariya gaba ɗayan su ma maganar Mimin, Zarah tace " okay okay u've won the bet, i better eat if not this girl is gonna be the death of me" ta faɗa tare da nuna Asmah sannan ta fara cin abincin duk da bata so ci ba, dan bata yanaƴin cin abincin.



Bayan sun gama ci sun kwashe kayan sun wanke hannu suka dawo suka baje a tsakar ɗaki, kamar yadda suka saba Zarah ta fara basu labarin littafin da ta karanta, FULANIN DAJI, sun natsu suna sauraronta domin Zarah ta iya bada labarin littafi tana yi tana masu demostrating yadda za sufi ganewa, sun daɗe a haka har la'asar ta ƙarato, Asmah tace "kai gaskiya Joda ta birgeni" Ita kuna Mimi tace "ni soyayyar su da Mahmud yafi birgene Wallah" Asmah tace "uhm ni dai na gane tashar da kika dosa Mimi" Mimi ta kalleta tace "ban gane ba wace tasha kike nufi, yau kuji Asmah ta faɗa hausa na rasa gane inda ta dosa dako ko hausar kirki baki iya ba, hausar ƴan fulani ta iya" Zara ta kwashe da dariya tace " kash wallahi zan so inji kallar hausar da kike da" Mimi tace bari kiji sai dai kan ta buɗe baki Asmah ta bita da filo tana ƙwala mata.



Suna gama sallar la'asar, a tare Mimi da Asmah Suka hada baki wajen cewa "a cigaba da labari" wanda hakan ya basu dariya, Zarah ta katse masu dariya da faɗin "My time is off, dai dai lokacin da Mami ta ɗiɓar mun kenan"
Asmah tace " Da kinsani kinzo da ƴar lele Ikram"
Zarah tace "Ai tana makaranta kema kinsan da da ita zanzo, ko ba komai zan fake da ita"
Mimi tace "ƙarfe nawa ne Mami tace ki dawo?"
Zarah ta amsa da " ƙarfe 4:30" a tare sukai kai mata duka, Asmah ta kama kanta ta juya shi saitun agogo tana nuna mata da hannu tare da faɗin

"indai ba jan rai zaki mana a labarin nan ba, kalla lokaci ƙarfe 4:40pm, we still have 50 minutes to go"

"Ay jan ran zan maku, duk wanda keson labari ya biyoni har gidan mu, haka kawai san banza naku yayi yawa, inzo har gida sannan na baku labari" Cewar Zarah tana jujjuya idanu.


Mimi tace "ya hakuri Zarah wallah ba daɗi munsani za muzo, suprise visit zamu maki, kuma sai munyi wuni, yanzu dai a bar maganar nan mu koma kan labari"

Asmah ta amshe da "Kar ki wani lallaɓata Mimi" sannan ta juya ga Zarah tace "Wallah Zarah kar kiban haushi na fara Karanta Novel zakisha mamaki"

"Ayi mana, kullum maganar kenan ki fara mana, ni birge nima zakiyi"

" shikenan very soon kuwa zan fara"

"in zaki fi birgeni ki fara yau"

Hannu Asmah ta miƙo mata tana faɗin "Bani wanda zan faran"

Zarah ta juya idanu tace "angaya maki ɗan fashi bai yawo da makami ne"

"prove ur self" cewar Asmah

Mimi tace "kamar da gaske"

Zarah tai wata hamshaƙiyar dariya tare da janyo jakarta, ta fiddo wani littafi 1 to 3, ta damƙa a hannun Asmah, Asmah ta karanta sunan littafin "TAWA TA SAME NI" tace "daga ji zaiyi daɗi"
Mimi ta amsa tana dubawa tana faɗin "ni zan fara karantawa"

Zarah tace " wani abunma sai kun karanta"

"Shegiya  ashe kinsan abunda kike, da in ta ce maki karatun ɓata lokaci kawai kike" cewar Asmah.

Zarah tace "ke dai zaunanan ai ni ko yanzu a ɗaura mun aure wallahi, zama da miji practical ne kawai ya rage banyi ba"

Mimi tace "to wai littafin hausan yana koyar da zaman aure ne?"

"Kwarai ɗagaske Mimi kuma ba nan kaɗai ba har zama da mutane masu hali dabam dabam, ga darussa ga kara wayau da hikimomi, ga ilimi da yawa da zaki ƙaru dashi, ke har zama da kishiya, ni zan iya cemaki komai ma"

Asmah kam da tunda Zara tai maganar na farko (na aure) ta saki baki, da kyar ta samu ta tallafo bakinta tana faɗin " ɗadi na dake Zarah kunya tai maki ƙaranci, wato ko yanzu a maki aure a shirye kike ko?"

Zarah ta ƙarbe da "Faɗi da ihu ki ƙara da wayyo zama daram daƙau, uhmmm Asmah kenan ina rashin kunya a nace ina son aure haram nayi, ko wace mace ƙimarta da darajarta ɗakin mijinta kema nasan kinsan haka, rabin addini nafa bai cika sai nayi aure, a'a wallahi ba abunji kunya, ke ingaya maki kunyar mafa kala kala ce, akwai kunyar da zata ƙara maki ƙima akwai wadda in kinyita zata tauye maki wani sani ne na ilimin da zai amfaneki"


"Na lura dai Zarah zama zamuyi ki fara bamu lectures, ɗan fayyace mana kashe kashen kunyar da kika lissafo"  cewar Asmah.

"ƴan mata kuyi ladabi in ɗora ku a system, in baku sirrika, ko da yake na lura Mimi saliha ce"
ta faɗa maganar ta ta ƙarshe cikn zolaya tana kallon Mimi.

Asmah tace "A ganinki kenan, a inda ba salihai ne za akira Mimi saliha"

Mimi ta watso mata harara tana faɗin " ƙaryarki Asmah ni saliha ce kamar ta bakin zarah, amman dai yanzu a aje salihanci a gefe" ta faɗa tare da maida kallonta ga Zarah kana ta cigaba " bamu sirrinka ki ɗaura mu a system ƴar uwa" suka tafa da Zarah.

Asmah tace "Ahhhhaffff da ba'asan asalin balbela bane da sai ace madina garinsu ne, muda muka san komai shiru kawai muke, a dai bar kaza cikin gashinta tafi kyan gani"

Zarah tace "fige mana kazar ko kaɗan ne mana ai ba wani ɓoye ɓoye tunda mun zama ɗaya kinga kowa sai ƴa karu dana kowa"

Mimi ma tace " Ay faɗa ko ma meye"

Asmah tace "bari kuji kaɗan daga ciki" tashi tai ta figi gyalanta sai da ta kai bakin ƙofa kana tace "ya Mahmud mana ai nasani" sannan ta mata gwalo, yanzu Mimi ta gane meye dalilin Asmah na cewa ta gane tashar data dosa dan tace ita soyayyar Joda da Mahmud yafi birgeta a labarin, fulo ta ɗauka ta jefa ma Asmah tana ƙunshe dariya, Asmah ta kauce ma fulon tana ƙara sakin dariya tace "Zarah muje na rakaki ki ƙyale wannan love bird ɗin" Zarah tai dariya ta tashi, tagama kintsawa sai da ta kai bakin ƙofa tace "To Mimi ni na wuce yau dai na yafe rakiyar, fata dai Allah ya ɗaiyaba mana M&M musha biki" tayi dariya ta fice da sauri mimi ta aza hannu aka tana faɗin "ohhh ni ƴar mutum biyu jikar mutum huɗu, koya akai Asmah ta gano sirri da ke tsakanin mu da ya Mahmud daba wanda yasani, ko dayake na manta Asmah ce the clever one i can't hide anything from her, inaga tanajin mu da dare wayar da muke kenan" ta ɗauki filo ta rungume tana murmushi.


Zarah ko tana fita ta wuce gurin Ammie tai mata sallama, Ammie ta ɗauko turaren wuta mai yawan gaske tabata tace ta kaima Mami duk da basu san juna ba amman suna aiken abun arziki a tsakaninsu, wata sa'in In Zarah zata zo gidan su Asmah Mami takan bata abu tace ta kai ma mamar ƙawar tata duk da bata san cewa itace sirikar ta da Aliyu ke gaya mata ba, Zarah ta amsa tana jero godiya kana ta fita a waje ta iske Asmah tare suka jera har wajen gidan, Asmah na cewa " ina Mimi ko borin kunya Ya hana ta fito wane?"
"ba dole ba, kin gama kunyatatan" cewar Zarah suka sa dariya, Zarah ta fiddo wayarta ta kira direbansu akan yazo ya ɗauke ta, sannan ta kira ya Aliyu kamar yadda ya umarceta sai data fara ringing ta manna ma Asmah a kunnenta, da hannu Asmah tamata alamun waye? Zarah tace "oho kin fini sani" muryar ya Aliyu taji yana sallama, hararar Zarah tai sannan ta amsa salamar, wata ajiyar  zuciya Aliyu ya saki yana faɗin

"Alhamdullilah i've finally got to hear her voice, ohhh Allah i've missed this voice and the owner badly"

Dariya Asmah tayi kana tace "kai ya Aliyu duka duka yaushe ne mukai waya satin da ya wuce fa"

"kinsan yadda maganar ki ta soka mun Mashi a zuciya kuwa sati ɗaya fa kika ce, kina nufin kenan bakiyi missing ɗina ba kenan, kwana bakwai fa ni ina nan inajin kamar nayi shekara bakwai bangan ki ba"

"Ayyah ya Aliyu ba haka nake nufi ba"

"To yayane?"

"Nayi kewarka sosai"

"I know i trust u for that matter"

"Thank u that means alot yayana"

Sun gaisa sosai sannan ya gaya mata akan ran litinin ɗinnan manyanshi zasu zo, domin Abbansu baya gari sai ran asabar zai dawo tace " to Allah ya dawo dashi lafiya"

"yace ameen, yanzu sai yaushe kenan sweerie"

Tace "nami kenan"

"Don't act like u don't know, ofcourse sadda zamu ƙara waya mana"

"oh that" ta faɗa tana dariya dan sarai tasan akan me yake magana, tace "You decide"

"Owk zan kira ki ta wayar Mimi kinji"

"To"

"okay bye take care i love you"

Tayi dariya sannan ta kashe wayar,tasan in bata kashe ba sai Aliyu yasa ta faɗa mashi abunɗa bata shirya faɗi ba yanzu, ta juya gun zarah da ke ta masu dariya ta harareta tace "anshi wayar ki malama in kingama dariyar daban ma san dalilin ki nayinta ba"

Zarah ta amsa tana faɗin "ni dai ba daku nake dariyata ba"

"kyama faɗa gaskiyane, yanzu dai meye kika ce ɗazu ya Aliyu ne ya aiko ki"

"Ay ya aikoni" ta buɗe jakarta ta fuddo wata pink madaidaiciyar paper bag ta miƙa mata tare da faɗin "gashi shine aiken"

Amsa tai tace "wow ya Aliyu na Kenan, ke tsaya meyasa baki ban ba kafin muyi waya dan nayi masa godiya ba"


"kai Asmah garaje ko buɗawa baki yi ba kinga ko meye a ciki, kina maganar godiya"

"kafin nan ansa mun tamyata tukun"

"Okay okay sabida nasan ya Aliyu bai damu da godiyar ba"

"Dallah matsa ya gaya maki, it seems nafi ki sanin yayan naki ma, kuma maganar banga komai ba amman ina godiya nasan komeye a ciki yafi ƙarfin godiya daga gareni"

"ba dole ki fini sanin shiba tunda yana faɗa maki sirrikansa nifa?"

"Ni dai kice masa na gode sosai sosai i really apprieciate" ta faɗa tare da shinshina daddaɗan ƙamshin dake jikin paper bag ɗin tana furxar da iska daga bakinta.

Zarah ta ɗan daki kafaɗarta tare da faɗin "ƴar iska zaki wani ce banda kunya, to ga alamun kin fini rashinta, kece ma kesan auren"


"Habawa Zarah wallahi kinfini iskanci, ke da zaki tara ƴan matan aji kina basu lectures, in gaya maki ni da aure sai kin duro da ɗan dugui ɗaya sannan, dan naga Mustafa ya kunno kai da gaske yake"

"Hahaha haka kika ce Kenan, ke dai ki zauna nan, Allah sarki ya mustafa habibina"

Asmah ta bigeta tare da faɗin " ohhh ni Asmah, ai Zarah ki shirya ina nan zuwa shaida ma Mami aure kike so, kinga sai a gaggauta yi maki ko?"

"Kai Asmah wallahi dakin birgeni"

"uhmmm ni Zarah kinfi ƙarfina wallahi"

"Wallahi kiyi shiru kar kisa na maki baki"

"in kin fasa kina tsoro"

"insha Allah Asmah ba zaki ƙara wata ɗaya ba baki shiga gidan mijinki ba"

"Allah ya isa tsakani na dake ban shirya ba tukun, sannan kuma is imposible"

"Meye shirin da baki ba?"

Dai dai nan dirabansu Zarah ya iso, ta shiga tana ɗaga ma Asmah hannu tana mata dariya, ita kuma tana faɗin a gaida su Mami da Ikram (ƙanwar Zarah), Zarah ta zuge glass tana faɗin

"Naƙi gaidasun, ai fushi suke dake tunda har yanzu kin ƙi zuwa ki gaida su da kanki kullum sai aike"

"Laaaaa Zarah kice suyi haƙuri insha Allah lokacin baiyi bane ina nan zuwa"

."Maƙaryaciya"

"Da gaske nake"

"Sau nawa kuma"
Suka ja mota suka tafi, Asmah ta wuce cikin gida tana dariya, Garden ta wuce tana zuwa ta zauna inda ta saba zama ta jawo paper bag ɗin ta buɗe..................





A/N

Are u curious 2 know wats inside, well met me in d next page, till then stay blessed, i will love it when u comment and vote for my story it stirs me up to the fullest and send me soaring up high in the sky, don't u think am doing all this for u readers, can't you just show appriciation by voting it doesn't take much i guess.

Allah Hafeez to y'all
👸🏼QUEENBK👸🏼

Continue Reading

You'll Also Like

181K 17K 79
"Sickler gare ta, kuma ku kuka ja mata." Ta yi shiru daga nan, dafe da goshinta, tana jin yadda kanta ke sara mata. "A kullum dad'a wayar wa mutane k...
134K 8.7K 55
Kallon kitse ba litaffina bane na marubuciyar nan ne Halima Abdullahi k/mashi
3.6K 285 44
labari me cike da darasi, kudi ba Shi ba ne komai Wanda Kuma kake ganin Bai isa ba sai kaga ya isa, labarin yarinyar da ta taso cikin kwazzabar mutan...
1.5K 168 22
saukakekken hanyar shiga,Amma naiman hanyar fita it will be diely.......WHEN IN NO WAY OUT