ZAN SOKA A HAKA

By queenbk2020

392K 23.9K 2.2K

#5 tausayi June 2020. #3 tausayi 20 June 2020. #1 munafurci #8 hausa novel. #2 tear drop june 2021. More

page 1
Page 2
page 3
page 4
page 5
Page 6
page 7
Page 8
page 10
page 11
page 12
page 13
page 1⃣4⃣
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
pahe 22
page 23
page 24
page 25
page 26
page 27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
Page 34
page 35
page 36
AUTHOR'S NOTE
page 37
page 38
page 39
page 40
page 41
page 42
page 43
page 44
page 45
page 46
page 47
page 48
page 49
page 50
page 51
page 52
page 53
page 54
page 55
page 56
page 57
page 58
page 59
page 60
page 61
page 62
page 63
page 64
page 65
page 66
page 67
page 68
page 69
page 70
page 71
Page 72
page 73
page 74
Page 75
Page 76
page 78
page 79
page 80
page 81
page 82
page 83
page 84
page 85
page 86
page 87
page 88
page 89
page 90
The end and thanks.

Page 9

4.1K 255 0
By queenbk2020

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨









💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*NA*
_BILKISU ALIYU KANKIA_
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼









🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S*
(( _Gidan zaman lafiya da amana insha Allah🤜🤛 ))_






Wannan page din sadaukarwa ne ga k'ungiyar *ZAMAN AMANA WRITER'S,* *((Z.A.W))* Allah ya k'ara had'e kan mu, yasa albarka a cikin rubutun mu, ya bamu ikon fad'karwa. Y'an uwa one love❤





Page0⃣9⃣






(waiwaye adon tafiya)

A cikin tafiye2 na da nake na sana'a ta, wata rana ina dawowa na tsinci wani mutumi da yarinya k'arama a hannun shi, wadda baza ta wuce shekara ukku da rabi ba, yarinyar sai kuka take shikuma jikin shi jina2 kamar an kwato shi bakin kura, kuma da alamu yana neman taimako sosai, ganin yadda ya firgice kawai neman mafaka yake, ga mutane sai kallan shi suke, ni kuma ganin shi a wannan hali yasa na matso kusa da shi tare da tambayar shi me ya faru da shi, ba amsar da ya bani illah;
banga halima ba wallahi, tana ina?, kar su kashe mun ita, sae ya fashe da kuka.

Niko ganin ba a hayyacin shi yake ba, yasa na mik'o hannu dan in amshi yarinyar in ja shi mutafi gida, in ya dawo cikin natsuwar shi, daga baya sai inji me ke damun shi ko zan iya taimakon sa, da sauri ya kab'e mun hannu tare da k'ara rungume y'ar hannunsa, yana fadin " kar ku rabani da ita ma."

Da kyar da sud'in goshi ya yadda ya bini gida, bayan mun isa na bashi ruwa yayi wanka sannan yasha, raunin hannun sa kam har a lokacin be dena fitar da jini ba, da na duba sai naga kamar harbin bindiga kuma ba'a fitar da bullet d'in ba, banyi k'asa a gwiwa ba, na aika a kira mun ta-sallah, bayan tazo ta riski abun da ya faru, ta rasa yadda zata fidda bullet d'in dan bata tab'a aiki irin wannan ba, cikin dabara dai da taimakon Allah ta fiddo mai, sai dai yaji jiki ba kad'an ba tunda ba k'wararra ba ce, a haka dai ta shafa masa wani magani sannan ta bashi wani yasha, bayan ya huta sosai muna zaune, da kanshi ya fara bani labarin me ya faru.

Ya fara da godiyar temakon da na masa, sannan yace,

" Ni sunana Muhammad maska, ni d'an asalin garin katsina ne amman muna zaune ne a damaturu ni da matata da y'ata guda d'ayan nan da ka gani, ya fad'a tare da nuna yarinyar dake kwance kan tabarma tana ta baccin ta, ita kad'ai Allah ya uzurta muda ita, ita ma d'in har mun fidda tsamanin samun yara, muka haife ta a shekar mu ta biyar da aure da matata mai suna Halima, ita kuma y'ar mai-duguri ce.

Sai da yazo nan a maganar shi sannan ya kalli ni ya ce mun yau laraba ko, ni kuma na gyad'a mashi kai, ya cigaba " kwana biyu da suka wuce ranar litinin kenan, tunda asuba da muka tashi ba mu koma ba kasancewar ina shirin zuwa office, ita kuma halima na ta shirya ma yarinyar mu dan ranar ne zata fara zuwa makaranta, kwatsam muka rik'a jin k'arar raki masu razanar wa, wata k'arar in ta tashi har gidan mu sae yayi girgiza, ga gari tuni ya hautsine ya hau kururuwa tunda ba wanda yasan mai ya faru, haka na tashi naje na kulle mana gidan mu, muka dawo mukai jugum2 in banda add'ua ba abunda muke, dan bamu san me ke faruwa ba, dan daga gani gari ba lafiya.
Halima ta bada shawarar mu kunna radio ko labarai, haka ko akayi muka kunna redio, anan muka ji ana ta shelar cewa " a safiyar yau ankawo wa garin damaturu farmakin ba zata, sun samu nasarar sa bomb a wurare da dama tunda ba'asan da zuwan nasu ba, kamar bankuna, masalatai, churchina, makarantu da dai sauran su, duk da ansamu rashi na y'an uwa da yawa, kar hakan ya tsorata ku hadin kan ku kawai muke buk'ata, dan Allah kar wanda ya fita, kowa ya tsaya a muhallin shi, domina gwamnatin k'asa tana ta aiki kan turo zakarun sodojin ta, dan suzo su yak'i wa'ennan y'an ta'adda, yanzu haka an taro wasu dakarun dan samun tsaro, had'in kan da zaku bamu kawai kar wanda ya fita, ku killace kan ku a cikin gidajen ku, kuyi ta addu'a.

Ko da jin wannan sanarwa sae muka k'ara tsurewa, itako yarinyar nan suma tarin k'ayi tsabar firgice, tunda bata tab'a riskar kanta a irin wannan yanayi ba, mu ma kan mu, mun kasa adapting ina ga ita.

Haka muka zauna muna ta addu'a, wajen k'arfe bakwai na yanma komai ya lafa, duk harbe2n da k'arar bomb d'in duk ba mu jin shi, kamar anyi ruwan sama an d'auke, kuma munji shelar cewa dakarun sodoji sun iso, sun kuma fara aikin su, ko da jin haka sai hankali mu ya d'an kwanta, amman muka kwana da aniyar cewa in komai ya lafa, zamu tattara ina mu, ina mu mu bar garin tunda dama ba namu bane, aiki ya kawo ni garin.


Washe gari muka tashi kamar ba abunda ya faru jiya, duk da ba shiga ba fita, mun dai ji dad'in yanayin shiru na yau akasin jiya,
Kamar daga sama kuma mu ka k'arajin wata hasumiyar ta tashi, wadda ta fi tajiya rikitarwa, haka dai akai ta abu hankula a tashe, bama iya connecting da junan mu sai ta waya, anan ne muka fara jin wai yanzu gida2 suke shiga su kashe mutane.
Duk mu ka k'ara sadak'aswa, mu kaji wata girgiza, har wutar tashin bomb d'in mun gani tuda a masallacin unguwar mu aka sa,
Haba nan y'an unguwa aka rud'e, suka rink'a fitowa ana dosar daji da gudu, ganin haka halima tace mu ma mu gudu, tunda kowa ma guduwar yake kar a bar mu, mu kad'ai, ba'asan rai na ba dai na biye mata dan nima a kid'ime nake.

In ka fito waje yadda kasan tashin duniya, ko wa gaya nan ya fito ya rirrik'e hannu y'an uwan su, ana ta gudu an doshi daji, gari yayi duhu, in ka kalla sama tayi bak'i sasoi tsabar hayak'i, nima da hannu d'aya na rik'e halima d'ayan kuma na sab'a d'iya ta a kafad'a mu kai cikin dajin da gudu.

Haka mukai ta wannan gudun fanfalak'in munyi tafiya mai nisa, ga dare yayi sosai ga gajiya ga yunwa, don haka muka yada zango a wata gona, a tunanin mu munyi sa'ar barin y'an ta'addan basu cimmana ba, ganin shiru ba wata hayaniya muka d'an saki ranmu, ga yanwa na ta adabar mu da yaran mu dan gajiya da gudun da muka tik'a, daga nan muka yanke shawar cin kabewa da gyadar da ke shuke a gonar, haka kuwa akayi mata suka had'a wuta mazan kuma suka karkatso aka dafa, nan ne kowa ya d'an samu abun sa ma bakin salati, yara suka d'an rage koke2n su, sai na samun kansu a wani yanayi dabam.

Ganin yana yin gonar na da sirri sai muka baje a tsakiyar ta, muka d'an kishin gida kafin gari ya ida waye wa kowa ya kama kansa, ashe su kuma sodoji sun biyo wasu rundunar y'an ta'adan da sukayi kwantan b'auna a wani daji na gaban mu, da sodojin suka biyo su sae suka yo kanmu, suku ma sodoji na sakar masu burusai, duk basu san damu ba, mu ma bamusan da su ba, haka aka cakud'e kowa ya tashi cikin firgici, suku ma sodoji na sakin ruwan bindiga, mu da muke kwankwance2 kowa ya tashi ya fara gudu, dan mu munsha y'an ta'addar ne suka cin mana.

Ni dai zan iya cema bansan inda hankalina yake ba, ni dai na san bacci ya fara kamani, can kuma na tsinci kaina ina gudu sosai, cilla k'afa ta kawai nake, sannan nayi ma wani abu tsatsauran rik'o, bana iya tantacen a mace nake ko a raye, ban kuma iya tantace meke faruwa, zan iya ce maka kamar film nake kallo, kwata2 hankali na baya jikina.

Haka na rink'a tik'ar gudu, duk da har a lokacin bansan me nake ba, can naji wani shocking a hannu na, kamar zai tsinke ga azaba sai kuma wani ruwa mai d'umi ke binshi har zuwa jikina, ban tsaya ba har sai da nakai wani titi, nan na tarar da wasu wanda suma tare mu kayo gudun hijira daga garin mu, sun tsaida wata daf mai itace suna rok'on mutumin ya taimake su, bayan ya yadda suka fara d'are wa kan itacen, ni dai da kallo na bisu, wata mata ce ta matso kusa dani, ta karb'i d'iyar dake hannuna ganin ta galabaita sae kuka take ba k'akk'autawa, ni kuma jiki ne duk ya b'aci da jini, tace mu tafi, ni dai zuk'wi2 na bita, badan na fahimci me nake ba, mu ka hau motar muka fara tafiya.

Ba laifi munyi tafiya mai tsawo, sannan hankali na ya fara dawo wa jiki na, na had'a biyu da biyu ya bani hud'u, take duk abun da ya faru yafara dawo mun, sai a lokacin na dubi hannuna da ke ta rad'ad'i naga ashe halbi ne aka mun, na waiga naga inda nake, ido na ya sauka akan d'iayata dake hannun wata, wadda har ta samu tayi baccin wahala, sannan na gama karad'e idanuna a motar nan ammn basu hango mun halima ba, take na tuna tunda muka kwanta a gonar nan, ban k'ara ganin ta ba, a kid'ime na saki wata k'ara had'e da salati, na rink'a ihu ina ce ma mai motar ya tsaya ya saukeni, ni saina je na nemo mata ta, ganin me motar be ma kula ni yasa na figi d'iyata naje zan dillika, ina yunk'urin fad'awa kawai naji an rirri k'eni.

Wani mutumi ne yace haba mallam ka tattaro natsuwar ka mana, baka ganin yarinya a hannun ka, kuma in ka koma ita kuma ta tsira aka kashe ka to ya kenan, ga yarinya k'arama a hannun ka, ko dan ita ka taimaka mana, in Allah yayi matar ka a hannun su zata mutu, ba kada yadda zakai ka canja k'addarar Allah, haka kuma in Allah yayi kwananta na gaba ba mai iya canja hakan, kai dai ka kwanatar da hankali ka, kai ta addu'a.

Niko ji nayi kamar ina mafarki, haka nai ta sumbatu na ni kad'ai so nake kawai in ga na tashi daga wannan mummunan mafarkin, a haka har mota ta isa wani gari, ta tsaya kowa ya sauka ya kama kai, niko saukowa nayi rik'e da d'iyata a hannuna, na samu bakin wata bishiya na zauna, har a lokacin hankali na baya jiki na, to shine muka had'u da kai anan har ka taimkeni, kuma na gode matuk'a Allah ya biya ka da tarin lada. Sae dae inason na rok'e ka wata alfarma.

Baffa ko da tunda ya fara jin labarin bai bar zubar kwalla ba, ya share kwallan yace, " ka fad'i ko meye in dai ina da ikon taimakon ka, nayi alkwari zan taimake ka da duk abunda Allah ya hore mun."

Mal.Mahammadu ya ce, " dan Allah inason ka rik'e mun y'ata amana, don gobe in Allah ya kaini da rai, zan tafi nemo mahaifiyar ta, abunda yasa ba zanje yau ba dan bana jin k'arfin jiki na kwata2 in na tashi ma har jiri nake ji, alabashi gobe in na je na d'auko magaifiyar ta, sae mu dawo mu karb'e ta. Baffa ya amsa mashi da to insha Allah zai rik'e ta amana. Sannan nayi mashi addu'ar samun sauk'i.

Tunda baffah ya fara labarin sai yanzu ya juyo ya kalli ma'u wanda tayi shab'e2 da hawaye, sannan yace ba kowa bace yarinyar in bake ba Asma'u.

Nan ma'u ta k'ara sakin kuka, ita dai tasan ba gwggo ce ta haife ta ba, tunda tana ma fad'i mata da kanta, amman ita duk a zatonta baffa ma haifinta ne, sai yau take ji abunda ya samu iyayenta, yau tasan sillar zuwan ta rugar nagge, yau tasan danganta karsu da gwggo, shi yasa ma bata raga mata ko kad'an tunda ba y'ar uwarta bace.
Ta kalla baffa tace, " to sai akai yaya baffah, ya tafi d'in."
Sai da ya nisa sannan yace, " a daren da ya ban labarin, mun kwana da zummar gobe zaiyi tafiya ya nemo mahaifiyar ki, amman ikon Allah washegari da gawar shi muka tashi, ya rigamu gidan gaskiya.

Ma'u ta saki wani kuka wanda zai iya haddasa ma, mai sauraro xubar kwalla.
Baffa baiyi yunk'urin hana ta ba, dan labarin nata abun kuka ne, wani ma yaji zai mata kukan tausayi balle ita da kanta.

Haka ma'u tai ta kuka ba k'ak'autawa😭😭😭😭😭😭



A/N

nima kukan ya hana ni idasa muku tafin😭, mu had'e gobe.


" THE BEST, ARE THOSE WHO ARE THE BEST TOWARDS WOMEN" PROPHET MUHAMMAD (( P. B. U.H)).

👸🏼QUEEN BK👸🏼

Continue Reading

You'll Also Like

251K 20.4K 61
"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin w...
181K 17K 79
"Sickler gare ta, kuma ku kuka ja mata." Ta yi shiru daga nan, dafe da goshinta, tana jin yadda kanta ke sara mata. "A kullum dad'a wayar wa mutane k...
3.1K 389 31
Fyaɗe aka yi miki. Shi ne abinda zuciyarta ke ƙara nanatawa. Ban san waye ba, ban kuma san dalilinsa na aikata haka a gareni ba, ni a sanina bani...
53.5K 1.9K 12
Just walk in and read, I promise u are going to be mesmerize with the emotional love story embedded in this novel.