Babi Na Casa'in Da Uku (93).

507 102 12
                                    


Suna isa hospital aka yi saurin duba ta. Complain din zafi a cikin ta, ta gefen da ta fadin da take ta yi ya sa aka yi running general check up. Sai da hospital suka tabbatar da she was okay, no harm had been done tukun suka yi releasing dinta bayan an tula mata drugs.

Straight Maamah ta wuce da ita gidanta dama already akwai kayan khayrin a can wanda bata je ta kwaso ba bayan dawowan ta daga Dutsen safe. Abinci aka kawo mata Maamah na zaune gefen ta sai da tabbatar ta ci abincin sosai tukun ta bata magani. Bata wani jima da shan maganin ba barci ya dauke ta. Tare da Billie Maamah ta bar ta a gida ita da Ahmad suka futa dauko Mahra a airport. Already Kabeer ya kira Ahmad a waya da yaji shuru basu dawo ba ya tambaye sa koh su na can gidan ne. Bayanin komi da ya faru ya ma Ahmad din wanda ya rasa fada zai ma dan uwan nasa koh rarrashin sa zai yi.

"Da ka rabu da ita kaima Kabeer". Ahmad ya fadi.

"Ka ga rainin wayon da ta mun ne Ahmad. Dan ina lallaba ta?".

"Matar ka ce".

"Toh shine zata dinga mun abu yadda ran ta ke so? Ni sa'an ta ne?".

"Tooooohhhhh" Ahmad ya fadi "farko dai kai ka mata laifi koh me ta maka kai ka jawo sannan kuma matar ka ce ba maganar kai ba sa'an ta bane. Maganar wannan ya riga ya wuce". Ahmad ya fadi abun ya qara batawa Kabeer rai.

"Kai baka da haquri ne Kabeer". Ya qara "Yanzu dai ka san yadda zaka yi ku sasanta sannan ka lallaba su Maamah. Nikam na je dauko amarya ta daga airport". Ahmad ya fadi yana dariya shikam Kabeer tsaki ya ja kan ma su yi sallama ya katse wayar.

Koh da suka dauko Mahra gidan Dattijo suka wuce. Ahmad ya shige wurin dan uwan sa ita kuma Maamah ta haye sama wurin su Dattijo. Tas ta kwashe iya abunda ta sani ta fadi musu aka kira Kabeer aka saka shi a tsakiya sai jaraba suke ta masa. Da ya buda baki zai magana zasuyi shutting din sa.

"Wana cin fuska ya wuce wannan?" Dattijo ya fadi yana kallon Kabeer wanda kan sa ke qasa kamar zai yi kuka "Na tashi naje har wurin mahaifan ta na tambayo maka auranta suka yarda sabida yadda suke ganin daraja ta sannan ka zo kana musgunawa diyar su". Be gama ba Adda Manga ta sako nata.

"Abun ya kai har rauni kake ji ma matar ka? Ah lallai biri kam yayi kama da mutum, abunda ya hanata zaman can kenan".

"Wallahi ku tambaye ta. Ni ban taba bugun ta koh wani abu ba, yau ma din Maamah kin yi misunderstanding abunda kika gani ne".

"Ka futo kawai kace qarya nike mana Kabeer. Ba sai ka nuna mun iya turanci ba". Maamah ta fadi tana masa wani irin kallon bacin rai "Makauniya ce ni? Ban san me na gani ba. Koh ba kai ka hankada ta ba".

"Ba da niyyar ta fadi ta ji rauni nayi ba".

"Toh tarbiyyar da muka maka kenan? Ka dinga hankada matar ka". Shuru Kabeer yayi da yaga duk ta inda ya bullo sai sun sace masa gwiwa. Daga karshe Dattijo ne yayi suspending meeting din yace sai khayrin ta sama kwarin jikin ta tukun zai zauna da dukan su. "Sai kaje ka dauko ta k...". Dattijo be gama ba Maamah ta ce

"Haba Baba. Ya zaka ce ya dauko ta? Ya gama nakasa ta. Ai tana wuri na for now. Baza mu dawo masa da ita ya raunana ta ba ga juna biyu a tare da ita". Kwalla suka ciko idanun Kabeer sabida takaici. Kasa magana yayi sabida ya san da ya fara magana zai fashe da kuka gashi kuma be so yayi kuka a gaban su, ba kuma ya so dan kawai yayi fada da matar sa ya zauna yana kuka amma abun sosai ya masa ciwo tun daga maganganun da khayrin ta gaya masa har zuwa wanda su Maamah suka gaya masa ga kuma hanasa ganin ta da ake neman yi. Ana sallaman shi ya miqe ya wuce be zauna gidan ba futa yayi.

Khayri koh ta dade tana barci sabida magungunan da ta sha dan bata tashi ba sai can yamma. Sai a lokacin kuma tana neman wayar ta dan yin kira ta tuna ta bar shi a gida. Bata dauka ba a lokacin da zasu wuce asibiti. Haka tayi ta zama ba waya hannunta for a whole day har sai next day da aka aika Ya Ahmad gida tukun ta roqe sa ya daukar mata wayan. Koh da yaje gidan ranar Kabeer din be nan, side dinsu was locked dan haka be samu ya dauko mata wayar ba.

SANADI✔️Место, где живут истории. Откройте их для себя