Babi Na Hamsin Da Daya (51).

629 139 26
                                    

Kano, Nigeria.

Sosai Maamah tayi mamakin ganin Inno Marte ta kawo musu ziyara har gidansu. Quite alright ta san wacece Hajja Fadime Abiso dan family dinsu is well known kuma baccin haka ma Dattijo ya sha yin business tare da corporations dinsu. Sun gaisa tayi welcoming din Inno Marte a babban living room din gidan, nan da nan ta sa masu aiki aka hado refreshments aka kawowa baqi. Bayan Maamah ta gama hidimar ensuring an kawo musu refreshments ta dawo ta zauna sukayi gaisuwa properly.

"Wajen diyarki nazo". Inno ta fadi going straight to the point.

"Billie na?" Maamah ta fadi cike da mamaki. Nazari ta hau yi akan possible reasons inda zai sa Hajja Fadime Abiso tayo takakkiya tun daga Borno har zuwa kano dan ganin Billie.

"Eh, ba itace Bilkisu Sadiq Yakasai ba?". Eh Maamah tace fuskar ta dauke da mamaki. Murmushi Inno Marte tayi ta dan yi sipping shayin da aka ije gabanta kan tace "Karki damu, ba wani abu bane".

"Toh shikenan, she's currently out taje Tahfeez amma driver ya riga ya wuce dauko ta dan haka any moment from now zata shigo gida". Ba a cika fifteen minutes ba bayan maganar Maamah sai ga sallamar Billie ta dawo daga Tahfeez. Tunda ta shigo ciki take kallon Inno Marte tana kokarin tuna a inda ta taba ganin ta amma ta gagara tunawa. Itama Inno kallon Billie ta ringa yi taji kawai instantly ta kamu da son ta dan ita duk abunda Sudais inta ke so itama tana so.

'So pretty, she'll make a lovely wife for my Sudais'. Tayi nazarin cikin zuciyar ta.

Maamah ce ta miqe ta bi Billie sama zuwa dakinta. Samun Billie tayi tana sanja kaya. "Ke Bilkisu" ta fadi tana shiga "Kin san matar da ke zaune living room dinmu?". Maamah ta tambaya, ita kuma Billie tace mata bata san ta ba.

"Baki taba ganin ta ba?" Maamah ta tambaya Billie ta ansa da eh. "kin tabbata? Dan ina mamakin abunda zai daga Hajja Fadime Abiso tun daga Borno har zuwa kano dan ganin ki Billie, in wani abun kika mata gara kin fada mun tun muna mu biyu".

"Wallahi Maamah ban mata kom...". Bata qarasa maganar ba ta tuno inda take tunanin ta san matar "Wait" fadi.

"Maamah kin san ta?". Ansawa Maamah tayi da eh "Tana da yaro me suna Sudais?". Maamah ta kuma ansawa da eh.

"Shi kika wa laifi Billie? Kin san yadda Hajja Fadime ke son dan nan nata kuwa?". Murmushi Billie tayi tana tuno Sudais Aadam Abiso "Ba abunda na masa Maamah, na dai taba haduwa da shi". Da Maamah taga dai da alamar bazata sama ansan da take nema ba daga wurin Billie, sai ce mata tayi ta gama shiri ta sauko qasa kar suyi keeping Hajja Fadime waiting "Kuma koh ma menene in kika sauko ai zan ji tunda kin qi fadi mun" Maamah ta fadi kan ta fice daga dakin. Sai da ta dau kamar ten minutes tukun ta sauko qasa, tana zuwa Inno Marte ta yi tapping space din gefen ta tana fadin "Come sit with me". Kusa da ita Billie ta wuce ta zauna, ba zatto ba tsammani taji Inno Marte ta jawo ta jiki tayi hugging dinta, tana releasing dinta from the hug ta fadi "Ma Shaa Allah, you're even more beautiful than Sudais said". Maamah dai zaune take shuru tana ta kallon ikon Allah, tunani take yaushe har Billie ta hadu da Sudais Aadam Abiso. Gaisawa sukayi properly kan Inno Marte ta fara ma Billie tambayoyi; shekarun ta nawa, ya matakin karatun ta da sauran su.

"I'm here because Sudais wanted me to come plead on his behalf". Ta fadi hakan ya sa Maamah yin yar tari. Wai Hajja Fadime Abiso ke fadin tazo pleading sosai abun ya ba Maamah mamaki. "I hope you'll give him a chance. Sudais is such a gentle man, you won't regret In Shaa Allah".

"He really asked you to come?". Billie ta tambaya. Daga mata kai kawai Inno Marte tayi bata ce komi ba. "What if I don't give him a chance?".

"You might end up living the rest of your life in regret" Inno Marte ta fadi fuskar ta dauke da murmushi sai dai kwata kwata maganar bata yiwa Maamah kama da wasa ba, hasalima words din came out as a threat to Maamah. Kallon da Inno Marte taga Maamah na mata ya sa ta gyara maganar ta.

SANADI✔️Where stories live. Discover now