Babi Na Goma Sha Tara (19).

820 177 28
                                    


WARNING!!! This chapter is unedited. Ignore my errors. Thanks
.

.
*************
Abuja, Nigeria.

Da sauri ta boye hoton da ta riqe a hannu tana kallo sai da kuma Niima ta riga taga hoton. Dago kai tayi suka hada ido da Niima ta sakin mata dan murmushi.

"Baki kwanta ba?" Karimatu ta tambaya.

"Kema baki kwanta ba" Niima ta fadi bayan ta zago ta zauna kusa da mahaifiyar ta "Is everything alright? Kwanan nan kina behaving awkwardly". Niima ta fadi muryar ta cike da concern for her mother. Murmushi karimatu ta sake yi kan ta ce ba komi sai dai koh kadan Niima bata yarda da zancen mahaifiyar nata ba.

"Whose photo where you gazing at?" Niima ta fadi tana kokarin jawo hoton dan ta riga ta ga inda karimatu ta saka shi a bayanta.

"It's no one" karimatu ta fadi bayan tayi saurin miqewa tare da hoton a hannunta "kije ki kwanta, kina buqatar barci dan gobe muna da so many activities" ta fadi kan ta juya ta shige ciki. Straight bata tsaya koh ina ba sai can sama bedroom dinta da Abdallah. Cikin safe inda suke ije kudi da valuable items nasu ta buda ta ije hoton safely kan ta kwanta amma sai ta sama kanta da kasa yin barci.

Shuru Niima ta zauna bayan mahaifiyar nata ta wuce ta bar ta a inda take. Tunani ta dinga yi akan possible reasons da zasu iya sa Ummin ta behaving strangely amma ta kasa samun koh daya. Gaba daya ta rasa wa zata wa magana dan shi kansa Abban ta has been behaving awkwardly. Dogon numfashi ta ja kan ta duba wayarta da ke kan cinyar. Ta san Bakhtiar kawai zata iya nema ya kwantar da mata hankali a wannan lokacin dan haka ta dau wayar ta tura masa saqo dan taji koh idanunsa biyu. Baa yi koh minti biyu ba sai ga kiran Bakhtiar na shigowa cikin wayarta. Farkon abunda ta fadi masa bayan ya daga wayar was "Dan Allah in munyi aure don't you ever hide anything from me, kaji?". Shuru yayi har sai da ta kira sunan sa tukun ya ansa ta "kaji abunda na fadi kuwa?" Ta tambaya cikin murya me sanyi.

"Yes habibty" Shima ya fadi cikin muryar sa me matukar sanyi "Na ji ki, I'll never hide anything from you In Shaa Allah". Yayi assuring dinta. Sun dan dau lokaci suna magana tana filling dinsa in on her activities of the next day har suka katse voice call din suka koma video call. Sosai Niima take jin dadi a duk lokacin da ta kasance tare da Bakhtiar, hakan ya sa duk ta mance wani damuwa na yadda iyayen ta ke behaving awkwardly ta saki jiki suka sha soyayyar su. Shi ya bi ta da lallama da rarrashi har ta miqe ta wuce ciki zuwa bedroom dinta. Be katse wayar ba har sai da Niima ta fara barci, saukar numfashinta da yike ji akan kunnensa na saka shi wani shauki, kaunar ta na qara dasuwa a cikin ran sa.

***********************

Kano, Nigeria.

Dattijo dai a ranar cike yike da farin ciki wanda ya kasa boyuwa, da kaga fuskar sa zaka san yana cikin walwala ne. Be ce da kowa komi ba har sai aka gama dinner akayi moving to family room din gidan tukun. Gyara murya yayi ya jawo hankalin kowa zuwa gare sa, surutun da ake ta yi duk aka daina kowa was eager to know what Dattijo had to share with the family. Sai da ya bi su da kallo daya bayan daya kan ya sake murmushi ya fara magana.

"Kamar yadda kuka sani, earlier on akwai maganan hada aure da muka tsakanin ku jikoki na hudu" duka su hudun kowa sai da yaji cikinsa ya kada saboda jin maganar da ake yi akan su ne, wato dai shi Dattijo yana nan akan bakanshi. Cigaba yayi da maganan da yike "Toh mun zo mun sake shawara da ni da iyayenku, wato muka ga zai fu muji ra'ayoyinku akan maganar, in akwai wadda a cikinku already yike kula wata koh take kula wani dan gudun ayi abu ba a kan son ran ku ba. Alhamdulillah that yielded a positive result". Tari Dattijo yayi Maamah tayi maza ta miqa masa ruwa a glass cup ya sha ta karba ta koma ta zauna kan shima ya cigaba da jawabin sa.

"Ahmad ranar da muka yi magana da kai ka tabbatar mun da babu wata wadda kake kulawa sannan kuma kayi na'am da decision dina amma sai in yar uwar ka Mahra ta aminta da kai, munyi haka da kai koh bamu yi ba?". Kowa ya maida attention dinsu ga Ahmad wanda ya saukar da kai qasa ya ansa tambayar Dattijo Colin wata karamar murya.

SANADI✔️Where stories live. Discover now