Babi Na Hamsin Da Shidda (56)

544 113 26
                                    

Kano, Nigeria.

Kiran Maamah ne ya tashe ta daga barci safiyar ranar. Tana dauka ta gaida ta a ladabce Maamah kuma da taji muryar ta alamar daga barci ta tashi ta shiga bata haqurin tashin ta da ta yi daga barci.

"Dama kira nayi ince miki ki shirya kizo nan. Shirin one week zakiyi, na riga nayi magana da Kabeer kuma ya ce ba matsala". Khayri toh kawai ta ce wa Maamah sukayi sallama Maamah ta ije waya. Bata sauka qasa ba sai da ta gama packing kayan da zata je yin one week gidan Maamah tukun. Har gefen Dattijo ta shiga bayan ta gaida su ta musu bayanin kiran da Maamah ta mata suka ce ba komi sai ta dawo.

Zuwa sha daya na safe har Maamah ta sake kiranta cewar taji shuru. Lokacin Khayri ta saki abunda take yi ta fara kintsawa. Tare da Mahra wadda itama tace zata je suka wuce. Zuwa lokacin dama Mahra da Billie sun qare secondary school, dan sun gama rubuta exams dinsu. Zaman jiran results kawai suke su wuce jami'ah. Itama khayri ta gama exams dinta ta sama promotion zuwa ajin gaba, a lokacin Js3 ita zata shiga.

Tunda suka isa ta izza Maamah tare da matan da ke zuwa mata gyaran jiki, wanda kuma aka aika dutsen safe lokacin bikin ta suka mata gyara kawai jikin khayri ya bata abunda ke shirin faruwa. Sosai Maamah ta nuna farin cikin ta da ganin zuwan su. Zasu haura sama da Billie ta tsayar da su tana fadin "Ai ke Khayri hira bata gan ki ba, kije ki ije kaya ki shirya gyara zaa yi". Sosai taji jikin ta ya mutu, gaba daya yan kwanakin nan ta sama nutsuwa da kwanciyar hankali ta mance da lamarin Ya Kabeer dan ba wai yana wani shiga sabgar ta bane, hasalima sai yayi har wata be kirata ba yaji lafiyar ta amma yanzu ta san lokaci yayi. Wata shiddan da Maamah ta roqan mata sun cika Ya Kabeer na hanyar zuwa tafia da ita. Hawaye taji suna neman saukan mata amma tayi ta kokari ta danne su dan bata so tayi gaban su Maamah.

Haka aka kwashi sati daya ana ta gyara khayri, a shafa wannan a shafa wancan, a bata wannan ta ci a bata wancan ta sha. Tun kan a cika one week ma jikinta ya sanja sai wani sheqi tayi. Dama kuma khayrin da tazo daga dutsen safe da wannan khayrin ba daya ba akwai sanji sosai dan ta sama hutu, jikinta da komi nata sun sanja sai dai har zuwa lokacin da sauran kunyar ta da rashin wayewa. Ranar da aka yi gyaran karshe me kitso da lalli suka zo aka zana mata kitso me kyau da kuma lalli shima me kyau ya sha turare. Sai a daren ranar Maamah take fadin mata cewa lokacin tafiyar ta gidan auren ta ne yazo tunda ta gama school session.

"Nan da kwana uku In Shaa Allah zaki wuce. An gama shirya komi, mijin ki na can yana jiranki sabida aiki bazai sama zuwa ba". Da zuciya na iya fasa ribcage ya futo da a ranar na khayri ya fasa ribcage dinta ya futo sabida yadda yayi ta bugu da sauri. Da Maamah zata sa kunne da tana iya jin sound din heartbeat din khayri wanda maganar da Maamah ke yi ya gama gigitar da ita.

"Sai a kwanta da wuri yau. Tafiyar ne yazo a qurarren lokaci da kinje gida kin musu kwana biyu amma ba komi in lokacin bikin su Ahmad yayi sai kizo ki musu kwanaki kan ku koma koh". Kai kawai khayri ta daga bata ce komi ba "Madallah yar albarka. Gobe Ahmad zai kaiki kuyi sallama ku dawo". Amsawa khayri tayi da Allah ya kaimu kan Maamah ta shafa saman kanta tana sa mata albarka tace shikenan tana iya wucewa.

Koh da ta shiga ciki, bata biyewa su Mahra da ke ta tsokanan ta ba. Kwanciya tayi shuru tace musu kan ta na ciwo zata yi barci amma kwata kwata Khayri ta sama kanta da kasa yin barcin. In ba tunanin komawa UK inda zata yi ba ba abunda take yi, tunanin waca irin rayuwa zasuje su fara take yi. A nan ma gabansu Maamah yana wulakanta ta ina ga sun tafi garin da babu su Maamah.

'Qilan kuma ya sanja cikin wata shiddan da kuka yi apart' wata zuciyar ta fadin mata sai dai khayri ta kasa samun kanta da iya yarda cewa Ya Kabeer zai taba iya sanjawa, bata ganin zai iya taba daina tsanar da ya mata, koh ya daina bata ganin zai taba iya son ta har suyi zama tare su mora rayuwar auransu. Ita kuma ga bala'in so da kaunar sa da take fama da shi, wata shiddan da suka yi apart, in ba qaruwa da son sa yayi ba, ba abunda ya faru da kaunar da take masa a zuciyar ta.

SANADI✔️Where stories live. Discover now