Babi Na Talatin Da Bakwai (37).

683 152 29
                                    


Dutsen safe, Katsina state.

Ana biki saura sati uku cur, a lokacin kwanakin Khayri tayi just few days kawai a gida su Maamah da tawagar kawayen ta da yan uwa mata suka iso garin Dutsen safe dan kawo kayan lefen Khayri. Anyi musu tarba na mutunci kuma aka yi ta musu godiyar irin riqon amana da suka yiwa Khayri zaman da tayi da su na watanni. Suma su Maamah sosai suka ji dadin irin karamci da girmamawa da dangin Khayri suka nuna musu. An ci an sha anyi raha kuma aka tattauna shirye shiryen biki kan taro ya watse. Kan su wuce sai da Maamah ta buqaci kebewa da Khayri.

"Nan da sati daya daidai zan aiko da me gyaran jiki, dan Allah Khayri in tazo ban da wasa ki tsaya a gyara mun ke da kyau". Maamah ta fadi. Ita dai Khayri kanta na qasa dan wani sudden kunyar Maamah ta fara ji. "Kaya ma suna wajen tailor, suma as soon as ana kawowa zan aiko miki da su. Ki kula mun da kanki kinji, sai mun sake haduwa". Maamah ta fadi tana rungumar Khayri wadda ke ta mata godiya. Bayan ta futo daga dakin da ta zanta da Khayri ne Gwamandi ta buqaci magana da ita. Gefe suka koma ta fara mata magana.

"Toh ban san ya naku al'adar take ba, koh akwai abunda za a buqata daga iyayen amarya? Ina ganin ya kamata in akwai a sanar damu dan mu zauna da shirin mu".

Yar dariya Maamah tayi kan ta bata ansa "Ai wallahi Inna karki ji komi, mun riga mun zama daya. Ki bar ganin Kabeer d'an mu ne, Khayri ma ta riga ta zama 'ya a gare mu kuma wannan aure abu ne na gida. Ba mu buqatar komi daga gareku, abu daya ne tal muke buqata".

"Toh me kenan?". Inna ta tambaya.

"Matar mu mana" Maamah ta fadi tana dariya "Da fatan muna zuwa nan da sati uku za a miqa ta gare mu, mu shikenan fatan mu. Allah ya sa ayi wannan aure lafia lau, ya sa albarka a cikinsa". Duka suka ansa da Ameen kan Maamah tace in shikenan zasu kama hanya dan kada suyi tafiyar dare. Sallama sukayi bayan Inna ta cika su da tsarabar abubuwa irin nasu na yan karkara. Sosai ta dinga mamakin karamci irin na mutanen nan, ina ma za a ce duk mutan duniya su kasance masu saukin kai kamar wannan bayin Allah, ai da duniyar ta zama a peaceful place to live in.

Lefen Khayri dai ya zama talk of town dan kaf garin Dutsen safe babu diyar da aka tabawa lefe irin na Khayri. Akwatunan ta kawai abun zuwa kallo ne bare kuma kayan da aka zuba cikinsu. Gaba daya akwatunan guda goma sha biyu da aka kawo cike suke maqil da kaya ga kuma wasu cikin ghana must go me girma. Atamfuna ne cike na dangi. Mutane haka suka yi ta flooding gidan Malam Mansur kallon arziki ana ta ma Khayri fatan alkhairi. Mata da su dan hadu sai hirar lefen Khayri kawai zaka ji suna yi, sai dai kiji ana fadin "Ai qasar waje ma aka ce zata zanna". Kowa tana fatan Allah ya sa diyarta a danshin Khayri.

Kamar yadda Maamah ta fadiwa Khayri, after exactly one week da zuwan su Dutsen safe aka aiko driver ya kawo me gyaran jiki tare da kayan da Maamah ta dinkawa Khayri na fitar biki da kuma kayan abinci cike da bayan mota Maamah ta siya ta aiko wai gudumawar ta kenan ayi hidimar biki. Kiranta Khayri tayi a waya tana godia har da kwalla dan a rayuwa bata san da me zata iya sakawa family din Alhaji Muhammad Dikko ba, sun dauke ta tamkar nasu sun nuna mata tsantsar so da kuma kulawa wanda koh wani wanda ka hada jini ma da shi ba lallai ya nuna maka irin wannan so da kulawan ba.

Koh a kano ma, sosai shirye shiryen biki ya kankama. Maamah sai gayyata take ta yi yan uwa da abokan arziki na kusa da na nesa. Ta so yin gagarumin biki amma Kabeer ya buqaci da ayi simple biki, cewar baya son flashy weddings dan haka Maamah tayi cancelling dinner inda ta so throwing aka tsaya akan yinin biki da kuma dan taron mata bayan an kawo amarya. Roqan Dattijo tayi ya bari ayi komi gidanta. Ba gardama Dattijo yayi na'am da shawarar.

"Ai Babana bayi da iyayen da ya wuce ku, na bar muku wuqa da nama. Allah ya muku albarka, su kuma iyayen nasa Allah ya kai haske kaburan su". Sosai wannan karamci da Dattijo yayiwa su Maamah yayi mata dadi.

SANADI✔️Där berättelser lever. Upptäck nu