Babi Na Farko (01).

4.7K 360 29
                                    

AUGUST 21ST, 1994.
A village located at the outskirt of town, in between Kano and Katsina State.

Miji da mata ne a cikin mota, mijin na tuqi while matar nasa na zaune gefen sa tana ba diyar su ýar wata biyu nono sai kuma dayan diyar ta su ýar shekara biyu da haihuwa tana zaune a backseat din motar tana ta wa ýar tsanarta kitso tana waqa. Dukanninsu cike suke da murnar zuwa ganin gida da zasu je.

"Na qosa mu isa wallah". Fadin Aliyu, mijin, kasancewar tun sanda ya sama aiki can lagos shekaru uku da suka wuce be sake dawowa gida ba, a lokacin matar sa na amarya tana da cikin diyar su ta fari.

"Toh toh dan mama Kwantar da ran ka nan bada dadewa ba ai zamu shiga katsina". Halima matar sa ta fadi tana yi wa ýar baby dinsu me suna Ummul-Khayri wasa. Juyawa tayi tana kallon dayan diyar ta su wadda ke copying abunda mamanta ke wa kanwar ta, ita ma tana wa baby dinta wai. Dariya kawai ta saka ta cewa mijinta.

"Duba ta mirror kaga me Kalthum take". Gaba daya Aliyu ya dau hankalinsa ya koma ga kallon abunda diyar sa ke yi a backseat din mota sai dariya suke. Koh kadan be lura da qaton tanker din mai inda yayi loosing brake har ya fara nufo musu ba. Kawai sai ji yayi matar sa ta saki wani ihu.

"Aliyu loooook". Ta fadi in an attempt to warn him of the danger that laid ahead. Shikuma gaba daya sai ihun ta ya ruda sa ya rasa abun yi har yayi loosing control over motar. Suna ji suna gani tanker din yayi ta approaching dinsu. In an attempt to escape it, Aliyu yayi qoqarin manoeuvring motar zuwa daji, a haka ne door din gefen matar sa ya bude daga ita har baby din hannunta suka yi ta rolling har kan ta yayi colliding da wani qaton rock, nan jini ya fara zuba. Shikam Aliyu wanda ganin abunda ya faru da matar sa ya kuma rikitar da shi kawai ya sadaqar har tanker din ya yo kansu da shi da dayar yarinyar su.

AUGUST 21ST, 1994.
Katsina State.

"Dan Allah ka qara saurin motar nan, yarinyar nan suma take. Ka rufa mun asiri Abdallah". Matar wadda fara ce me matukar kyau ta fadi, hawaye sai ambaliya suke a fuskar ta. Tana riqe da diyar ta ýar kimanin shekara uku a hannu, wadda suke hanzarin kaiwa hospital saboda maganin kwari da ta sha accidentally.

"Haba Karimatu, duk kin bi kin rude. So kike na hau sama koh so kike na dinga buge mutane. Kiyi haquri dan Allah ba abunda zai sameta". Abdallah ya cigaba da Kwantar wa matar sa wadda duka ta gama rudewa hankali.

"Ita daya dal gareni Abdallah, me zai hana hankalina tashi. Sai da nayi shekara goma kan na same ta. Gashi a sanadin haihuwar ta na rasa mahaifa ta. Kaico na ni karimatu". Ta fadi hawayen ta na qaruwa "Wallahi ina iya mutuwa in na rasa diyata".

"Ke dallah yi wa mutane shuru. Waya ce zaki rasa ta daman". Abdallah ya fadi cikin bacin rai kan daga baya ya fara rarrashin matar nasa har sai da ya tabbata ta dan Kwantar da hankalin ta tukun. Shuru motar yayi kowa yana saqe saqe cikin ransa, ita dai karimatu ba abunda take yi in ba addua ba zuwa ga subhanahu wata'alah akan ya ceci rayuwar diyar ta wadda a duniya ba wadda take so irin ta.

AUGUST 21ST, 1994.
Bauchi State.

Dan dattijo ne tare da wani dan yaro wanda bazai wuci shekara goma ba ke ta faman Safa da Marwah a corridor din delivery ward din wani babban Asibiti dake cikin garin Bauchi. Duka dai da alamar hankalinsu a tashe yike. Doctor ce ta fito tare da wani nurse yana bin ta a baya.

"Alhaji Dikko?". Ta kira.

"Yes yes that's me".

"Kai ne ka zo da Bilkisu Adam? Patient inda tazo haihuwa".

"Yes yes doctor, daughter in law dina ce".

"I'm sorry to say but she's in a critical condition, gashi baby din ya fara galabaita, da alamun we need to perform a cesarean section on her dan gudun kar a rasa both or one of them".

SANADI✔️Where stories live. Discover now