Babi Na Talatin (30).

888 158 44
                                    


And we've made it to chapter 30🤩💃 yau akwai party😂🤣 Thanks y'all for supporting SANADI 💕. (NB- Unedited chapter).
.

*****************
.

Abuja, Nigeria.

Bayan Billie, haka wata kawar Hajia Karimatu tazo ta sake raising magana cewar gaskia Khayri da Niima suna kama.

"Sai kace wasu yan biyu. Koh ya da 'kanwa". Karimatu kam sai murmushin yaqe take dan koh kadan abun baya bata dariya. Taya two people from different walks of life look so much alike. Kar dai fa abunda zuciyar ta ke ta raya mata tun farkon da aka fara kamar su Niima da Khayri ya zamto gaskia fa.

Ita dai Khayri wani iri dadi take ji a ran ta for no prior reason. Gaba daya worries inda ta tashi da shi that day was gone. Gashi ta kasa daina stealing glances at Niima, wanda itama ta kasa daina kallon Khayri, tana jin wani dadi a ranta.

Zuwa karfe hudu na yamma an gama ma amarya lalli, mutane da yawa ma an musu dan su Billie ma duk an musu kowa sai yaba kunshin sa yike. Mata ana ta hira, wasu na rawa wasu kuma na gefe ana ciye ciye.

"Zo muje". Khayri ta ji an fadi mata daidai kunnen ta. Koh da ta juya Niima ta samu kusa da ita fuskar ta dauke da murmushi "I want to show you round the house". Ita kanta Niima bata san me sa take shisshigewa wannan Khayrin ba, abubuwan da bata taba yi ba a rayuwar ta ta sama kanta da yin su a ranar. Niima El-Yaqoob a rayuwar ta bata taba bin wata yarinya sai ma dai yan mata suyi ta bibiyarta dan suna son zama kawayen ta amma sai gashi yau wai ita ke shigewa wata.

Da murmushi Khayri ta miqe bata ce komi ba. Su kam Billie cike da mamaki suke bin su da kallo. Kamar yadda ta fadi, room by room Niima ta zaga da Khayri tana nuna mata makeken gidan iyayenta. Ba inda bata kai Khayri ba, inner chamber din iyayenta ne kawai bata kai ta ba.

"Laaa na mance, muje na nuna miki drawing room din Abba". Niima ta fadi tana jan hannun khayri wadda ta bi bayanta koh gardama babu. A hanyar su na sauka qasa ne Niima ta fara making convo da Khayri "Baffah shine mahaifin ki?". Ta tambaya dan a time inda suka yi spending tare, Khayri ta kira sunan Baffan ta so ba adadi.

"Aah. Mahaifin Babana ne shi".

"Shi mahaifin ki fa?". Khayri ta tambaya curiosity getting the best of her.

"Ban san shi ba". Khayri ta fadi, har Niima ta buda baki zata sake wani tambayar muryar Khayri ya tsayar da ita "Allah ya masa rasuwa a lokacin ina da watanni hudu a duniya". Salati Niima tayi kan ta fara ma mahaifin Khayri addu'o'i.

"Toh mahaifiyar ki fa?". Niima ta tambaya.

"Itama ban san ta ba. Rana daya suka rasu da mahaifina". Dago kanta tayi suka hada ido da Niima. Murmushi kawai ta mata duk da idanun ta cike suke da kwalla. Addu'o'i Niima ta sake farawa tana kokarin kwantar ma khayri da hankali.

"Amma kina da yan uwa? Yayu koh qanne?".

"Yayata daya, sunanta Ummu Kalthum kuma itama ranar da Allah ya karbi rayuwar iyayena, a ranar ya karba nata dan haka ni daya ce". Sosai Niima ta ji wani irin ras a zuciyar ta, kasa cewa komi tayi na wasu yan mintuna kan ta daga baya ta buda baki tayi magana.

"Me ya kashe su haka?". Duk yadda ta so danne zuciyar ta ta kasa sai da tambayar ta futo. Sam bata so fama ma khayri mikin rasuwar iyayenta da yar uwar ta ba amma kuma Niima bata san me ya sa take jin ya kamata ta tambaya, ya kamata ta san me ya faru da su, ya kamata ta san wannan Khayrin sosai dan ba kadan take jin ta a ran ta ba.

"Hatsari suka yi, hatsarin mota". Tun daga nan basu sake cewa komi ba har suka isa drawing room.

"And here we go". Niima ta fadi da murmushi ta buda qofar wani makeken daki haddade an 'kawata shi da kayan alatu, ga kuma family portraits nan kala kala a jikin bango. "Muje in nuna miki best part din dakin nan". Jawo hannun khayri tayi zuwa wani trestle table inda aka yi arranging frames na hotunan Niima tun tana qarama har zuwa girmanta.

SANADI✔️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora