Babi Na Saba'in Da Takwas (78).

696 121 26
                                    


Kano, Nigeria.

Billie koh da ta dawo gidan tension inda ke tsakanin ta da Maamah be sauka ba dan har zuwa lokacin Maaman haushi take da ita akan ta liqewa Sudais Aadam Abiso with all that was happening.

"Ga dan qawata nan Hajia Shema'u. Yaron kirki, dan asali me kyau yazo ya gan ta kawai a samu fahimtar juna mu hada da na Ahmadi". Maamah ta fadi suna zaune a dining hall ana dinner. Uncle Sadiq ne ya juya ya kalli Maamah kan yace.

"Not now. Please Rumaisa". Rolling idanu Maamah tayi ta cigaba da zancen ta.

"In ba yanzu ba sai yaushe? Zama zamuyi mu kalli yarinya? Tana neman kunyata mu iyeeee?".

"Toh gani dai nayi shi Bakhtiar din yana auran diyar kawarki kuma koh dazu kunyi waya da ita Maamah. Itama surukin ta ai is involved in all this me sa bazaki yanke hulda da ita ba?". Billie ta fadi cikin bacin rai.

"Ni kike wa mayana haka Bilkisu. Ni Maman ki?". Maamah ta fadi tana miqewa. Kan Billie ta yo zata kai mata duka Baba yayi saurin tarewa "Ka sake ni Sadiq na gurji bakin ta, yanzu Bilkisu har ta kai in yi magana ta maida mun? Because I have her best interest at heart iyeh!". Shi dai uncle Sadiq gam ya riqe ta ya qi saki yana kokarin calming dinta. Billie kam sai kuka ta miqe ta haye sama Khayri ta bi bayanta a guje. Uncle Sadiq ne da Ya Ahmad suka zaunar da Maamah wanda itama ta fara kukan suka yi ta mata fada akan cewar her approach was wrong. Ya kamata ta duba halin damuwa da Billie take ciki kuma ta bi da ita ta yadda zata fahimta.

"Kuma Maamah seriously ina ruwan Sudais da laifin da iyayen sa suka aikata? Abunda ya faru tun kan a san zaa haife sa Maamah" Ahmad ya fadi.

"Ina wayewar ki Rumaisa?" Cewar Uncle Sadiq "Ina ilmin? Na boko da na addini? Toh ni dai ina so na sanar da ke cewar wallahi wallahi in har na yi bincike na gamsu da halin yaron nan Sudais, ba abunda zai hana na basa Bilkisu. Muddin ya shirya auranta".

"Amma fa....".

"Dakata!" Uncle Sadiq ya fadi yana daga mata hannu "Bana so na saurara zancen iska. Ki dai je ki zauna kiyi nazari" ya fadi kan shima ya fice ya bata wuri. Ahmad ne kawai ya zauna da ita ya cigaba da rarrashin ta yana kuma kokarin fahimtar da ita cewa ba gudun Sudais ya kamata suyi ba, baza su biye ma duniya ba suyi blaming dinsa koh suyi ostracizing dinsa for that which isn't his fault.

"Duk mu nan Maamah ba wanda ya wuci ya fada irin halin da Sudais yike ciki. Jarabawa ne babba dan haka kamata yayi mu taimaka masa wajen ganin ya cinye jarabawar shi ba wai mu qara jefa rayuwar shi cikin rudani ba. Ke kin sani Maamah son Billie da gaske kuma yaron yana da hankali, he's nothing lik his mother. Toh kin taba tunanin irin halin da yike iya shiga in har aka hanasa Billie?". Ahmad duk ya mata bayani Rumaisa sai taji duk jikinta yayi sanyi, ta rasa me ke mata dadi. Su khayri a nasu gefen itama kokarin rarrashin Billie tayi ta yi tana bata baki har dai ta samu ta kwantar da hankalin ta. Ranar tare suka kwana da Billie a dakinta duk dan kar ta bar ta ita daya ta shiga tunani da damuwa.

Kwana biyu suka dauka suna kokarin dodging din juna sai a kwana na uku ranar Maamah ta bi Billie har dakin ta suka zauna suka yi magana ta ba Billie haquri itama Billie din ta ba Maamah haquri for how she acted. Rungumar juna suka yi Maamah tace In Shaa Allah ta daina daga hankalin ta kan maganar Billie da Sudais, sai dai ta taya su day addu'a da fatan alkhairi. In no time Maamah da Billie aka dawo kamar da suka fara wasa da dariya da junan su.

"Toh a shirya muje mu gaida su Dattijo". Maamah ta fadi da zata futa daga dakin "Ina Khayri?".

Billie ta ansa da "Tana daki tana barci. Tun dazu take complain din ciwon kai". Kan Maamah ya daure ta fara tunanin anya wannan yan ciwo ciwon da shegen barci da Khayri ke yawan yi yan kwanakin nan lafia kuwa?.

SANADI✔️Where stories live. Discover now