Babi Na Hamsin Da Bakwai (57)

527 123 21
                                    


London, England.

Sarai Kabeer ya san koh kadan be kyauta ba kuma ya kamata ya bata haquri ya kuma yi mata bayanin mantuwa ne amma girman kai ya hanashi. Yana ganin ya sha karfin ya tsaya yana bata haquri dan haka koh da ya qaraso ta bags dinta kawai ya dauka ba tare da yace mata komi ba ya juya ya fara jan luggages din zuwa mota. Miqewa tayi ta dau qaramin jakkan da handbag dinta ta bi sa a baya. A seat din baya ya jera kayan ya shiga itama ta shiga passenger seat ta zauna ya ja mota.

"Ina kwana". Ta fadi murya qasa qasa tana addu'a Allah ya sa kada ya sace mata gwiwa.

"Ina gajia, sannu da zuwa". Ya amsa mata daga nan be qara ce mata komi ba koh da kuwa tambayar mutanen gida ne be kuma bata fuskar ta sake wata maganar ba. Juya kanta tayi ta fara kallon sceneries inda suke ta wucewa, komi na burge ta. Taga abubuwan da koh a Abuja da Lagos bata taba gani ba. Ga garin babba, suna tafia tana tunanin yadda zata saba da wannan babban garin har ta iya futa da kanta gashi kowa turanci yike turancin ma irin wanda ba ganewa take ba sabida accent. Ji take kamar a mafarki wai ita Ummul-Khayri yau ita ce a garin London. London inda sai dai taji ana fadi a labarai wai gata yau a qasar Ingila, a nan kuma zata zauna rayuwar auranta. Kamar yadda Maamah ta fadin mata cewa itama zata zama Yar qasa tunda mijinta dan qasa ne kuma yaran da zata haifa suma yan qasa zasu zama. Wannan tunanin ya sa ta murmushi, wai itama wataran zata haifa yara nata na kanta, yaran ta tare da Ya Kabeer.

'Da irin wannan halin koh in kulan da yike nuna miki?' tayi wannan nazarin cikin ranta.

Sun kai kimanin mintuna arba'in zuwa awa daya a hanya kan suka isa wata unguwa me kyaun gaske. Gidajen duk gwanin ban sha'awa. Sun wuce gidaje kamar bakwai kan suka isa wani gida me dan madaidaicin girma, nan ta ga Ya Kabeer ya juya kan mota yayi parking a driveway din gidan. Ba tare da yace mata komi ba ya sauko taga madadin yayi amfani da mukuli sai wasu codes ya danna a wani electronic pad da ke maqale jikin bango sai ga qofa ya bude. Kayan ta ya fara shigar mata cikin gidan. Itama saukowa tayi ta bi bayan sa. Sallama tayi ta shiga suka wuce dan stairs inda ke foyer din gida zuwa wani living room haddade wanda is attached to a dinning, taga tsarin gidan koh kadan be yi kama da irin gidajen da take gani a gida Nigeria ba. Wucewa yayi zuwa wani corridor wanda take tunanin yana leading to dakunan kwana. Akwatunan ta yaje ya ije ya futo, koh kallon gefen ta be yi ba yace "Bedroom din na ciki, kitchen's that way akwai abinci a fridge". Daga nan be ce mata komi ba kuma ya juya ya fice abun sa dan already he was getting late for his meeting.

Khayri ta kai mintuna goma tsaye tana nazarin what just happened. After leaving her for over twelve hours at the airport, a garin da bata taba zuwa ba, garin da bata da kowa yanzu ya kawo ta gida kawai yayi dumping yayi futar sa, a haka zaa yi zaman?. Numfashi ta ja kan qasa qasa tace 'Allah ya shirya'. Corridor inda taga ya shiga itama ta bi ya kai ta wani qofa, da ta bude daki ta samu qato hadadde. Gado ne qato, queen-size kuma haddade a tsakiyar dakin ya sha pillows ga bedspread inda ke kan gadon da ka gani a ido ma ka san me tsada ne. On each side of the bed kuma akwai side drawers wanda saman su were adorned with side lamps. Ga qaton flat screen TV a jikin wani bango. On one side of the room kuma was a comfy looking loveseat da kuma beanbag babba guda daya sai dan qaramin center table. Wani open passageway ta bi ta ga closet ne qato da compartments for various articles of clothings, sai kuma bathroom wanda shima ya hadu. Komi a ciki irin na yan gayu. Hatta slippers inda ke ije a qofar shiga me kyau ne, soft and fluffy daya pink daya blue. Haka ma kan sink ta lura da toothbrushes biyu daya in pink the other in blue sabbi ful. Haka ma a towel rack akwai two robes with the words "Mr" and "Mrs" written at the backs of each. Ga kuma towels of different sizes, colors and textures neatly folded kan rack din sai kuma cabinet din medicine da skin and hair products. Komi tsaf tsaf. Futowa tayi ta jawo boxes dinta zuwa closet din. Wardrobe and compartments din side daya cike suke da kayan Kabeer, from shirts to kaftans to his shoes and ties duk suna nan carefully arranged. Tun kan ta buda dayan side din ma ta riga ta san nata ne sabida takalman da ta gani displayed on the shoe rack, duk na mata ne. Koh da ta buda cike ta sama wardrobe din da kaya duk sabbi, dan space kadan ne kawai ba kaya, just enough for her to arrange the stuffs she brought.

SANADI✔️Where stories live. Discover now