You Didn't See This One Coming!!!

342 31 9
                                    


'You're doing it again!' Bakhtiar ya fadi yana dora hannunsa daya saman na matar sa. Kallon sa tayi baki a tabe. 'You know that thing you do when you're tensed. Shi kike yi, ki daina'.

'B ban san meyasa ba' ta fadi cikin muryar ta wanda a koyaushe qara rikita Bakhtiar Arab yike yi 'Duk sanda zamu hadu sai na ji wani irin anxiety'. Yar murmushi mijinta yayi kan ya bata ansa.

'By God I've never seen two sisters that share a bond as yours. What you have with Khayri is magical! Ki daina jin haka okay'.

'Baba! Baba!' Ali da Abdallah suka sauko a guje suna kiran sunan mahaifinsu, nanny dinsu biye da su tana riqe da Ansaar a qugun ta. 'Baba ni zan zauna kusa da kai'

'Aah Baba ni ne!' Yaran suke fadi suna tsalle. Bakhtiar da Niima suka kalli juna suna murmushi kan Bakhtiar ya duqa to address the boys.

'In kuka zauna kusa da ni wanene zai zauna da grannie and grandpa?' Bakhtiar ya tambaya with a puzzled look on his face kamar wanda ke nazari.

'Mamma and Ansaari!' Niima ta fadi tana karban sa daga hannun nanny dinsa 'Shikenan ni da shi sai mu zauna da su tunda ku da Baba zaku yi tafia' Nan aka shiga wani sabon rigima kuma Ali da Abdallah suka ce duk sun fasa zama kusa da Baba, su da kakkanin su ma zasuyi tafiyar tunda haka ne. Dariya iyayensu ke yi suna kallon yadda yaran ke ta tsalle tsallensu suna fadin sun sanja ra'ayi. Niima ta miqawa Bakhtiar baby inda ke hannunta tace zata koma sama dan ta qara tabbatar da cewar sun dau duk abubuwan da ya kamata.  Tsaf sai da suka tabbatar da sun kwashi komi tukun aka futo tafia zuwa lokacin Alhaji Abdallah tare da matar sa Hajia Karima har sun isa filin jirgi already, isowar su Niima kawai suke jira. Murna wurin su baya misaltuwa a lokacin da suka hango yan jikokin su tafe a guje zuwa gare su, hatta Ansaar wanda a hannu yike sai tsallen murnan ganin kakkanin sa yike. Dariya Niima tayi tana fadin

'Wai Ummi baku gajia da ganin yaran nan ne. Duk ran Jumu'ah fa sai kin gansu amma kullum kuka hadu kamar an shekara!' Dariya Ummi tayi tana fadin 'Toh ina ruwanki, ni da yan mazaje na kuma'. Gaisawa duka aka shiga yi kan suka shige private jet din Bakhtiar kowa yayi settling in jirginsu zuwa Kano ya miqe.

Koh sanda suka isa Kano, already motoci na jiransu zuwa qatoton gidansu wanda Bakhtiar ya siya tunda suna yawan zuwa Kano. Gida ne me bangarori biyu daya wanda yike zama da iyalin sa, daya kuma wanda babban dansa Sudais yike zama tare da nasa iyalin. Suna isa tun kan su gama saukowa daga mota Suraiya ta rugo a guje straight ta fada jikin Bakhtiar tana murnan ganin kakan nata wanda take cewa Baba kamar yadda yaransa suma suke ce masa. Suna buda gefen su suka shiga Billie ta fara aiko masu aiki da kayan abinci dan dama ita kwananta biyar kenan a Kano, ta riga su zuwa kuma dama da tazo Maamah take aiko mata da masu aiki wanda suke taya ta kula da gida har zuwa lokacin da ta koma Abuja.

Su ma Maamah a can gefen su babu zama. Tana ta fama shirin karban mutan Ingila, wato su Khayri ga kuma hidimar Mai jego da take ta yi dan a lokacin satin Mahra Uku da haifo yaronta. Tun cikin na shiga watan haihuwa ta maido ta gida dan ta sama enough kulawa har zuwa wannan lokacin bata koma ba dan Maamah ta ce sai tayi kwanan arba'in da haihuwa tukunna zata bari ta koma dakin ta. Inna Gwamandi itama tana nan daga Dutsen Safe tazo dan ita ke taya Maamah kulawa da Mahra da jinjirin ta.

'Maamah na wuce dauko su' Ahmad ya leqo dakin Maamah yana fadi ta masa fatan alkhairi. Sai da ya shigo ya duba dansa ya sumbace shi a saman kai be ankara ba Maamah ta kai masa dundu tana fadin 'yaran yanzu da shegen rashin kunya' Ahmad be kula ta ba yana yar dariya yace 'Inna Gwamandi ince dai kina ganin abunda ake mun takan na nuna soyayyata akan yarona' kan Inna ta ansa Maamah ta jefo masa pillow tana 'Sarkin garinku Ahmad! Bazaka wuce ka dauko mun yara na da jikata ba'. Yana dariya ya juya ya wuce. Futan sa yayi daidai da shigowar Khalid tare da yaransa Zayd da Zayn wanda sun girma sosai da kuma qannensu mata biyu Fatima da A'ishah yaranda Khalid ya haifa tare da matar da ya sake aure dan auran sa da Anisa tuni ya mutu. Duk yadda su Maamah suka so su sasanta su a shirya a dawo tare Anisa ta qi sabida wahala iya matuqa da ta sha a hannun Khalid. Ta sama mijinta wanda yike kaunar ta ta aura kuma har Allah ya basu haihuwa tare. Shikuma khalid a bayan Anisa yayi aure sun kai kala hudu duk ba wadda ta zauna sai ta qarshen wadda itama yau lafia gobe babu. Suna shigowa suka wuce suka anshi new cousin dinsu suka fara masa wasa ita kam Maamah duk murna ta rasa inda zata sa kanta dan a duniya ba abunda take so kamar yaranta da jikokin ta.

Kan Ahmad ya dawo daga airport dauko su Kabeer har su Bakhtiar sun riga sun isa gida ya fara cika. Maamah ta dinga murnan ganinsu, ta riqo hannun qawarta Hajia Karima suna ta murnan ganin juna.

'Oh ji mu Hajia Karima! Kamar jiya muke yan mata' Maamah ta fadi.

'Wallahi gamu yanzu gashi duk furfura. Mun tara jikoki. Kai Allah abun godia' suka tafa hannu suka cigaba da godewa Allah da alkhairorin sa a gare su.

Kamar thirty minutes da isar su Bakhtiar sai ga Ahmad nan ya iso da mutan Ingila. Khayri da kukan ta ta sauko daga mota dan lokacin da Allah yayiwa Dattijo rasuwa tana tsaka da jaraba ga ciki da ya zo mata da tsananin laulayi dan haka bata samu tazo Nigeria ba. Daga qarshe kuma tazo ta sama barin cikin ta shiga jinya. Ganin tana kuka ya sa matan gidan suma duk aka shiga kuka ana tuno Alhaji Muhammad Dikko da iya kokarin da yayi wurin hada kan zuri'ar sa. Tabbas rasuwar sa wani abu ne da baza su taba iya mantawa da shi ba a rayuwar su.

'Sai haquri khayri Allah ya amshi Dattijo ya kuma bamu wani Dattijon' Adda Manga ta fadi tana share nata hawayen. Dama Ahmad yana samun d'a namiji ya bada sunan Dattijo kuma shima yaron hakan suke kiransa Dattijo. 'Allah dai yayi muku albarka, ya sa kuyi koyi da halayen sa na gari' Adda ta cigaba da musu addu'o'i suka yi ta ansa ta da Aamin.

Khayri da Niima kuwa da suka sama kebewa da juna ba a qara jin motsin su ba dan su dama a kullum da sun hadu shikenan sai a nime su a rasa. Komawa suke wuri guda suyi ta hirar su abun sha'awa da su. 'Toh yau dai hirar nan da mu za ayi shi!' Billie ta fadi tana zama kusa da Niima wadda ta gallo mata harara cikin wasa tana fadin 'ke har yanzu baki san ni uwarmiji bace koh' duk suka kwashe da dariya. Mahra itama ta sama wuri gefen Khayri ta zauna suka cigaba da hirar su. Suma mazan a nasu gefen suka taru aka dinga hira, iyaye ma na nasu gefen da kuma yan qananun jikoki da tattaba kunnen gidan ana ta wasa. Gida dai ya kacame gwanin ban sha'awa.........


Surprise!!!!!!

Ya mukaji😹🤣 meeting our favorite characters again! Did we enjoy the surprise?

Wallahi I miss writing about these characters just as much as you guys miss reading about them too. I hope you enjoyed my little surprise.

And i have yet another surprise for you! I'm starting a page on tiktok for storytelling. Zan dinga rubuta short stories ina narrating muku on tiktok. Sounds fun right!!!! But I'll need your support for that, the page is new so I'll need followers. Kindly follow and tell others to follow the page. You'll enjoy it In Shaa Allah. Zan dinga narrating muku labarai wanda zasu qayatar da ku, su ilimantar da ku sannan su nishadantar da ku. Below is the details. Thanks.

Don't forget to follow!!!!

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Don't forget to follow!!!!

SANADI✔️Where stories live. Discover now