Babi Na Saba'in Hudu (74).

551 120 57
                                    


Abuja, Nigeria.

Shigowa Salame tayi, sabuwar me aikin da Ummi tayi kwana kwanan nan. Da fara'ar ta ta miqawa Niima madarar da Ummi ta aiko ta da shi.

"Auntie Niima gashi inji Ummi" Dan dama sabida saukin kai da kuma rashin kyamar dan adam irin na Hajia Karimatu, hatta ma'aikatan gidan ta duk Ummi suke ce mata kamar yadda diyar ta ke ce mata kuma kyautatawa iya gwargwado tana musu. Karban cup din Niima tayi fuskar ta dauke da fara'a ta ije a gefen gado ta cigaba da karatun takardan ta. "In dauke shi Auntie?". Salame da bata futa ba daga dakin ta tambaya Niima tace mata ehmana tana iya daukan Hashir wanda ke cikin crib dinsa idanun sa biyu. Dauko sa tayi ta riqe shi zata zauna a qasa Niima tace ta miqe ta zauna kan rocking chair inda ke kusa da crib dinsa.

"Baki sha madaran ba auntie zai huce".

"Zan sha karki damu". Sai da aka qara kamar minti goma tukun Niima ta daga cup din ta kai baki ta kurba ta ije ta cigaba da karatun ta. Haka ta dinga taking milk din in sips har ta shanye tas, har zuwa lokacin kuma Salame bata bar dakin ba. Har Hashir ya koma barci a hannun ta ta kwantar da shi ta zauna tana yin ma Niima hira.

"Na fara jin barci". Niima ta fadi bayan ta yi hamma.

"Da wuri haka auntie. Koh tara be yi ba". Niima tace mata gajia tayi sosai don haka zata kwanta in ya so zuwa anjima ta farka. "Sai da safe Auntie Niima". Ta fadi tana dauke cup inda ta sha madaran ta fice da shi.

Tana futowa daga cikin dakin Niima ta jawo zandareriyar wayarta da take boyewa bata bari kowa ya gani daga brazzier dinta. Number tayi dialling ta kafa wayar a kunnen ta. Da sauri ta wuce ta gefen da ta san zai wuya wani ya jiyo ta ta tsaya.

"Hajia ni ce".

"Na san koh ke wacece ina da number ai". Aka fadi daga dayan gefen "Na fadan miki da kin kira ki dinga bani update kawai ba sai kin tsaya surutun banza ba".

"Na bata ta sha. Ta kwanta barci". Dadi labarin yayi wa Hajja Fadime Abiso. Step one na plan din ta was successful now they needed to move to step two.

"Toh kina ji. Zuwa anjima sai ki koma ki aiwatar da sauran aikin".

"Toh amma Hajia gas..." Inno bata bari ta gama magana ba ta katse ta dan she had a feeling she wasn't going to like what Salame was going to say.

"Ke ki saurare ni, Kin san dai na san garinku koh, na san iyayen ki na san gidan da kika yi aure. Wallahi ina iya sawa a kashe mun iyayenki, da yaranki. Kaf biyar dinsu". Inno ta fadi ba dan ta tsoratar da Salame ba but dan tsaf abune da zata iya, hasalima ta sha yi. She eliminated anybody that was in the way of her and her goals, loved ones of such people included "Baki son kiyi arziki ne? Kin fi son ki mutu kina bauta gidan wani? Koh aikin gida ne zai hada miki miliyan biyar inda na ce zan baki eh?". Inno Marte ta fadi all in her bid to manipulate Salame. Already ta riga dama ta kashe mata kudade, ta siyan mata waya me tsada, ta aikawa iyayen ta kuma da kudi dubu dari biyar a siya awaki a dinga mata kiwo duk dan Inno ta siya trust dinta.

"Call me when you've completed the task". Tana fadin haka ta katse wayar.

Qasa Salame ta wuce da cup din ta ije a kitchen ta sama Ummi ta shigo da kayan da Abdallah ya gama cin abinci. "Ta sha koh?". Salame tace mata eh har ta kwanta ma wai tana jin barci "Toh madallah, ke ma sai aje a kwanta a huta gajia koh". Wucewa tayi staff quarters zuwa dakin da take sharing da wata me aikin gidan ta shiga ta zauna shuru kan gado. Sai da ta bari dare ya raba biyu tukun ta miqe da sand'a ta koma cikin gidan ta back entrance din gida da ta bari bude on purpose. Sama ta haura zuwa dakin Niima ta bude a hankula ta shiga. Yadda ta bar ta haka ta same ta koh juyawa bata yi ba. Daukar risk tayi ta dan taba Niima don taga koh zata farka amma sai taga koh motsawa bata yi ba dan haka ta wuce zuwa crib din baby da ke barci shima.  Daya daga cikin small pillows inda aka yi arranging cikin crib dinsa ta dauka ta kai fuskar sa. Before she had any second thoughts ta danne fuskar shi da pillow din. Whimpering ya fara, his small body shaking, his lungs fighting for a breath of air amma ina Salame bata daga pillow din daga kan shi ba har da ta ga ya daina motsi koh kadan. Mai da pillow din tayi ta ije ta kai hannun ta kan hancin sa ta tabbatar da cewa baya numfashi tukun ta bar dakin a guje. Kan ta koma dakin kwanan su ta kira Inno ta sanar da ita cewar ta qarasa aikin.

SANADI✔️Where stories live. Discover now