Babi Na Arba'in Da Uku (43).

950 143 58
                                    

Lagos, Nigeria.

Ranar gaba daya Kabeer be sake futa ba kuma ba wai dan ya damu da barin ta ita daya bane, sai dai kawai all of a sudden he lost interest in going out. Dan haka ya bar ta tayi ta barcin ta a bedroom shikuma ya wuce living room ya cigaba da kallo. Har zuwa sanda ya gama shirin barci bata farka ba. Kallonta yayi ya ja wata yar tsaki kan ya ja telephone din da ke ije gefen gado yayi dialling room service ya fadi musu yana buqatar extra duvet. Baa yi minti goma da yin wayan ba aka kawo masa duvet din ya ije kan gado ya wuce bathroom yayi brushing bakinsa ya yo alwala yazo yayi nafila kamar yadda ya saba kan yazo ya kwanta. Sai da ya juya ya sake kallon yadda take barcin ta peacefully ya ja tsaki ya juya mata baya ya rufa da bargon da aka kawo masa ba a wani jima ba barci ya dauke sa.

Khayri bata farka ba har sai can cikin dare wani tsananin kishin ruwa ya tashe ta. Miqewa tayi zaune ta dan yi addu'a, koh da ta juya sai ganinsa tayi gefenta yina barcin sa. Bata san meyasa ba taji haka ya faranta mata rai har wata yar dariya ta kufce mata tayi ta da dan qara.

"Akwai abinci a microwave". Taji ya fadi mata. Bayan haka be sake ce mata komi ba itakuma a zuciyar ta ta fadi 'Dama ba barci yike ba?'.

Zame jiki tayi daga saman gadon ta wuce kitchen ta sha ruwa sannan ta duba microwave kamar yadda ya fadi there was food in there for her dan haka tayi warming ta koma da shi living room ta ci a hankula, saboda yunwa da ya riga ya mata yawa ma a ciki kasa cinye abincin tayi, dan kadan ta tsakura ta maida sauran kitchen ta rufe ta sha ruwa ta koma bedroom din ta shiga bathroom tayi wanka ta sa kayan barci a nan sannan ta futo ta fara gabatar da sallolin da tayi missing.

Duk wani motsi da tayi damun Kabeer yike sai dai kuma ya kasa ce mata komi, duk yadda ya so mata ihu ya sama kansa da kasa yin haka. Qilan tausayin ta ne ya fara shigansa. Ita kam Khayri tana gama gabatar da sallolin ta ninke hijaab dinta da sallaya ta dawo ta ja pillow ta kwanta a qasa kamar yadda ta saba dan gudun ta koma kan gado ya mata jaraba, ta san zuwan likita duba ta ne kawai ya sa Ya Kabeer barin ta ta hau gado ta kwanta dan haka gara ta koma qasa ta kwanta tun kan ya farka ya ci mata mutunci.

"Ki hau gado mana. Bana son munafurci". Muryar sa ne ya katse mata dan guntun tunanin da take. Ba kadan ba mamaki ya kamata wai Ya Kabeer ne ke fadin ta dawo kan gado. 'Toh shi wannan wana irin mutum ne' tayi tunani a zuciyar ta. Sanda take ganin zai mata fada sai taga be yi ba, sanda kuma bata tsammani sai taga ya rufe ta da jaraba over very trivial things. Da sauri ta koma gado ta kwanta a takure ta ja bargo ta rufa kanta dan dama ba karamin sanyi take ji ba saboda qure sanyin A.C da Ya Kabeer yayi. In no time wani barci me shegen dadi ya dauke Khayri dan koh kiran sallar asubah bata ji ba sai ji kawai tayi an dan tabo ta. A hankula ta buda idanunta suka yi ido hudu da Ya Kabeer da ke tsaye a kanta yana kallonta, dan runtse idanun tayi kan ta sake budesu dan ta tabbatar da cewa ba mafarki take ba sai ji tayi ya ce mata "ki tashi lokacin sallah yayi". Ba tare da ya qara fadin wani abu ba ya juya ya wuce bathroom ya gama abunda zai yi a ciki kan ya futo tuni har ta dan kintsa gado. Bayin itama ta shiga ta dauro alwala tana futowa ta sama yana jiranta ta futo suyi sallar tare. Shi ya ja su sallah, ga mamakin Khayri taji yana karatu cikin qira'a me dadi, abun ya dan daure mata kai dan a ganinta mutumin da ya san Allah, yike da ilmin addini bazai yi irin abubuwan da Ya Kabeer ke yi ba, ga shan giya da yike yi da taba, ga hulda da matan da muharamman sa ba ga kuma shegen fada da fadin rai. Nafilfilu suka yi kan suka yi sallar asubah. Bayan sun idda Khayri ta gama addu'o'in ta juyowa tayi ta gaida shi, ba yabo ba fallasa Kabeer ya amsa gaisuwar ta ba karamin dadi hakan ya mata ba dan ita tun da ta san Ya Kabeer bata taba gaida shi ya tanka ta ba sai wannan ranar. Har ta miqe zata wuce ta kwanta ya tsayar da ita.

"Dawo" kawai ya ce mata. Bin umarninsa tayi ta dawo taga yayi mata nuni da ta dauko sallayan da ta ninke, haka din tayi ba gardama. Tana shimfadawa ya miqe ya kabbara sallah suka sake gabatar da wasu nafilfilun. Koh da ya sallame raka'ar karshe sai gani tayi ya juyo yayi facing dinta ya fara reciting dua's. Hakan ya ganar da ita cewar sallan da ya kamata ace sun gabatar tare tun daren su na farko as newly weds ne suka gabatar a wannan lokaci. Hakan ya qara sa ta jin wani dadi, a zuciya tana fadin 'qilan sauyin zuciya ya fara samu'. Without seeing it coming taji ya dora mata bayan hannunsa saman goshin ta, wasu imaginary backflips zuciyar ta ta dingi yi, yina beating furiously as if it was about to break out of her chest. Da ya cire hannunta ji tayi kamar ta ja hannun ta maida kan goshin nata, haqiqa so sosai take yi wa Ya Kabeer duk da irin tsanar da yike nuna mata. Gyara muryar da yayi ya sa ta maido attention dinsa kansa.

SANADI✔️Where stories live. Discover now