Babi Na Goma Sha Uku (13).

1K 186 15
                                    

.

Abuja, Nigeria

.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
.

Kan ya zauna sai da Bakhtiar ya mannawa yayarsa dan kiss a saman goshinta. "I've missed you, how was Canada?".

"Alhamdulillah Bakhtiar. Na bar Laylah and Khalifa can". Ta masa bayani. Sun kai minti goma sha biyar zaune suna ta hirar su kan Yasmeenah ta shigo pushing a food cart.

"Waye a gidanmu yau" ta fadi fuskar ta dauke da murmushi. "Gaba daya ka bi ka mance da mu Bakhtiar. Ka rabu da zuwa".

"Yasmeenah habibty I've always known you can't do without me" Bakhtiar ya fadi cikin wasa kan ya miqe ya dan hugging dinta. Tea ya fara hadawa, ita kuma Yasmeenah ta deba samosas guda uku ta sa a dan plate karami ta miqawa Sahar wadda ta ansa gratefully kan Yasmeenah ta sama wuri kusa da ita ta zauna. Hirar politics suka fara, daga nan aka sanja akalar hirar zuwa na business. Bakhtiar sai da ya shanye second cup of tea dinsa kan yayi gyaran murya dan gabatar wa su Begum da dalilin zuwansa.

"I'm getting married in ten days". Ya fadi kai tsaye ba tare da ya tsaya wani kwane kwane ba. Daga Sahar har Yasmeenah duka suka juya suna kallonsa sai kace he had just grown a second head.

"Ban gane ba Bakhtiar".

"Nace aure na nan da ten days".

"Su wa suka nema maka auran hala?" Sahar ta tambaya not knowing where to start from. "Wace zaka aura? I hope it's not that little child of El-Yaqoob's". Ta tambaya.

"Daga gidan Baffa Rashid nazo nan, we spoke and tomorrow inshallah zasu je ayi finalising komi dan bana son delay koh kadan. Cikin kwana goma In Shaa Allah Ni'imatullah will be mine". Ya fadi with so much conviction in his tone.

"Wannan karamar yarinyar Bakhtiar? Kayi uba da ita".

"Why is her age so much of a matter to you?".

"I was j.....".

"Look Sahar, Kar mu bari abunda ya faru auran Khalifa ya sake faruwa. Our family can't handle such controversies, it'll affect our public image" Bakhtiar ya taka ma yayar tasa burki tun kan tace zata yi raising wani objection game da auransa "Abdallah is a good business man, we will benefit from the alliance. And what's more important is that ina son Ni'imatullah itama kuma tana so na". Sahar zata yi magana Yasmeenah ta dora hannunta a kan cinyar ta ta dan yi squeezing dinta softly just to assure her that everything's going to be okay.

"I'm so happy for you Bakhtiar" Yasmeenah ta fadi da fara'a. "Allah ya kaimu lafia". Murmushi kawai Bakhtiar ya mata kan ya miqe zai tafi. Kiss ya sake mannawa Sahar kan goshin ta.

"Ki shirya zuwa jibi zaku gidan future in-laws dina kuyi duk wani abu da mata ke yi kan ayi aure". Be tsaya jin abunda zata fadi ba ya fara tafia. Kan ya kai parking lot ya shiga motarsa personal assistant dinsa ya kirasa to remind him of his meeting with Hajja Inno Marte.

.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
.

Kano, Nigeria.

Ranar tun safe Maamah ta shirya gidan Dattijo with the hopes of convincing him. Dan ita a ganinta in ba tashin hankali ba, ba abunda wannan abu da Dattijo ke shirin yi zai kawo masu. It was clear none of the kids was happy with the arrangement except for Billie wanda tun ranar da suka koma gida Maamah ta zaunar da ita ta fara kokarin ganar da ita illar auran wanda koh kadan baka zuciyar sa. Tabbas Kabeer na son ta amma ba so irin na aure ba. Babban tsoron Maamah shine kar bayan anyi auran su juya suna tsanar juna hakan ya qara mata karfin gwiwar zuwa wajen Dattijo da niyyar jawo masa ra'ayi da kuma nuna masa illar da ke cikin abunda yike shirin yi.

SANADI✔️Where stories live. Discover now