Babi Na Ashirin Da Biyar (25).

911 152 11
                                    


Kano, Nigeria.

Kwance take tayi nisa cikin tunani, riqe take da takarda a hannun ta amma hankalinta ba a kan takardan yike ba tana can duniyar tunani. Koh kadan duniyar yan kwana biyun nan baya wani mata dadi, bata taba tunanin son da take ma Ya Kabeer har ya kai haka ba da take jin irin wannan zafin a ranta tun ranar Dattijo ya sanar musu da auran Kabeer da Khayri. Da farko tayi tunanin mancewa da batun Ya Kabeer  and burying whatever feeling she ever had for him abu ne da zai zo mata da sauki amma sai dai ta ga abun ba haka yike ba, kwanakin nan so da kaunar Ya Kabeer kamar qara shigar zuciyarta yike. Ta rasa yadda zata yi, tayi kuka har ta gaji. Tana cikin duniyar tunanin ta har Maamah tazo ta zauna kusa da ita bata yi realizing ba sai da taji an yi tapping dinta softly. Murmushin yaqe tayiwa Maamah kan ta miqe daga position din da take ta zauna.

"Sauko ki zauna" Maamah ta fadi in her ever sweet tone. Rumaisa ta kasance mace wadda Allah yayi matukar sanyin rai dan koh daga yadda take magana ma zaka san me sanyin zuciya ce, ga son mutane da kuma mutunta su. Kudin da Allah yayiwa mahaifin ta da kuma mijinta be sa ta zama mace me son wulakanci ga na qasa da ita ba. "You're growing up so fast, when was the last time i oiled your hair?". Ta fadi bayan Billie ta gyara zama. Duba container din essential oils inda ta shigo da tayi da kuma su combs kan ta juya ta sabule hular da ke kan Billie. Shuru ba tare da sun fara hira ba Rumaisa ta fara gyara kan diyar ta, sun dade zaune shuru bame magana kan Maamah tayi breaking silence din.

"How're you feeling?" Ta tambaya with her voice laced with so much concern for her beloved daughter.

"I'm fine. Alhamdulillah" kawai Billie tace.

"Oh come on. I know you're not, kin manta ni na haife ki" At this point Maamah ta saki kan gashin Billie ita kuma Billie juyowa tayi ta zauna facing her mom. "You love him so much, don't you?".

"So so much Maamah, so much it hurts". Billie ta fadi, tears slowly cascading down her cheeks "Ban san ina so sa haka ba".

"I know habibty, I do. You haven't been yourself lately and that bothers me sosai". Rumaisa ta fadi bayan ta sauko qasa itama ta zauna level daya da Billie "He wasn't meant for you, ba rabon ki bane shi kuma I'm sure there's someone out there who is befitting for you. You just have to let go and go out, meet the world, know new people and do things that make you happy".

"Things like shopping?". Billie ta tambaya.

"Yes baby, like shopping. As long as it keeps you happy for me". Ta fadi tana pinching cheek din Billie. Hakan ya sa Billie dariya ta rungume sosai tana mata godia. "You know what? We should go out, shop and have some nice time. Your dad and Ya Ahmad can meet us for dinner later koh?. Sosai Billie tayi murna da suggestion din mamanta. "Amma bari a gama gyaran gashin tukunna koh Hajja ta". Duka suka yi dariya kan Rumaisa ta koma saman gado ta zauna Billie kuma ta juya aka cigaba da gyaran gashi. Baa yi cikakken thirty minutes ba suka gama Rumaisa ta miqe ta wuce dakinta shiryawa. Itama Billie wardrobe dinta ta buda tana neman kayan da zata saka. Wani dogon floral dress ta ciro tare da wani cashmere veil me kyau wanda zai shiga da rigar ta kan ta wuce ta shiga watsa ruwa. Tana fitowa tayi shiryawan ta tsaftsaf tayi kyau abunta ga wani kamshin me sanyi dake tashi daga jikinta. Wata yar jaka ta dauko ta saka wayarta, da credit card and other necessities a ciki kan ta wuce shoe rack dinta ta dauko wani espadrille ta futo ta ja qofarta ta sauko qasa. Ba da jimawa ba Maamah ta sauko qasa itama tayi shirinta tsaf cikin wani Pakistan top da wando ta lulluba dan madaidaicin veil over her head. Car key dinta ta dauka suka wuce straight basu tsaya koh ina ba sai Ado Bayero mall. Shops daban daban suka shiga mostly na kaya da takalma da cosmetics, jewelries and the rest, duk dai irin kayan da ke interesting mata especially teenagers. Komi Billie ta dauka sai Maamah tace ta duba something similar a dauka na Mahra da Khayri. Haka suka yi ta saye saye kan ka ce me sun kashe hundreds of thousands. Sai da suka futa suka ije kayan da suka saya cikin mota kan suka koma ciki straight masjid suka wuce sukayi sallah. Daidai lokacin da suka futo masjid Su Ahmad suka kirasu cewar sun iso Maamah tace musu su hadu kawai a 'Bombay To Beirut'.

SANADI✔️Where stories live. Discover now