Babi Na Tamanin Da Tara (89).

543 111 30
                                    


Bata wani jima da shiga ciki ba ta futo masa hura da kwano ta kawo ta ije masa a gaban sa tare da container din sugar dan ya zuba iya yadda yike so. Miqewa tayi zata shige ciki Inna ta tsayar da ita.

"Ina zaki kuma? Bazaki dawo ki zauna da baqon ki ba". Ba dan ta so ba ta dawo ta zauna can nesa dashi akan tabarma. Miqewa su Inna suka yi dan su basu wuri, Baffah ya ce zai koma can wurin sana'ar sa tunda sun gaisa.

"In zai wuce ki sa a kirawo ni". Ya fadiwa Inna wadda ta rako shi har zuwa bakin zauren gidan. Tana dawowa ta wuce ciki abun ta amma bata jima ba ta futo ma Khayri da wani magani da take dafa mata ta sha kullum ta miqa mata kan ta wuce. Shuru suka zauna, khayri na riqe da kofin maganin a hannu bata sha ba.

"Cewa tayi ki shanye yanzu ki maida mata cup din". Kabeer ya fadi yana kallon ta.

"Na ji ai". Khayri ta ansa shi.

"Mene ke damun ki?". Ya tambaya ta ansa masa da ciwon kai ne. Daga nan basu kuma magana ba dan Kabeer ya rasa me zai ce mata sabida yadda yaga tana ansa shi cikin bacin rai. Ita kam khayri gaba daya she wasn't comfortable zama tare da shi.

"Zamu koma tare koh?".

"Ba tare muka zo ba". Maganar yaji ta doke sa sosai. Wai yau shi khayri ke maidawa magana.

'You deserve it'. A voice from deep within whispered.

"Yaushe zaki dawo toh?". Ya tambaya tace masa kwana goma tayi da Maamah zata yi.

"Amma dai kin san ba Maamah kike aure ba koh? In nace dole ki koma yau dolen ki fa mu koma". Shuru tayi bata ce masa komi ba, ita dai a zuciyar ta ta san ba yadda zaa yi ya saka ta komawa da shi bayan bata shirya komawan ba.

Shurun da ya ga tayi bata tanka sa ba ya sa ya sanja tactic "Toh kwana nawa ya rage kwana goman su cika?" Ya tambaya tace masa uku. "Shikenan zan dawo nan da kwana uku daukan ki. Ki shirya".

Toh kawai ta ce masa daga nan bata kuma cewa komi ba. Shikam Kabeer yana zaune yana shan huran sa gaba daya attention dinsa akan ta yike. Sai bin gaba daya jikinta yike da idanu. Khayri ta sanja sosai a yan watannin da be gan ta. Ya kuma yi kewar ta sosai. Ya qara kamar awa daya tukun ya miqe yace zai tafi, Inna ta futo suka yi sallama tana fadin bari ta sa a kira Baffah.

"Aah dan Allah Inna ki bar shi. Ai zan dawo nan da kwanan uku daukan ta, zamu hadu". Shikenan Inna tace kan ta masa fatan alkhairi ta kawo fresh nono tace ya kaiwa Adda Manga dan dama duk sanda wani daga gidan yaje sai anyi aiken nono zuwa ga Adda Manga.

Ya kama hanyar waje ita kuma Khayri ta nufi hanyar daki Inna ta janyo ta tana fadin "Toh mandiya! Haka ake yi baza ki masa rakiya ba". Ta fadi tana tura mata nonon Adda Manga a hannu. Baki a sama Khayri ta bi sa a baya har zuwa bakin motar sa.

"Khayri" ya kira sunanta a wata muryar tausayi "Dan Allah ki shiga mota muyi magana. Dan Allah ba dan ni ba, kin ji". Da kamar bazata shiga ba amma yadda ya hada ta da Allah ya sa ta buda passenger seat ta zauna. Shima shiga yayi ya zauna ya sa ma motar central lock tukun ya juya ya kalle ta.

"Haushi kike da ni har yanzu khayri na?". Dan 'kwafa tayi jin yadda yike wani kiran ta khayrin sa. Sai a yanzu ya san da ita din nasa ce? Kai namiji da zaqin baki!. Kai hannunsa yayi zai riqo nata hannun tayi saurin kwacewa. "Haba khayri. I'm sorry, please". Shuru tayi bata ce masa komi ba tana dai ji kalaman yadaurar da yike ta fada mata. Har yayi surutan sa ya gama bata ce komi ba, ta zauna shuru idanunta anywhere but on him. Sun kai fifteen minutes bayan ya gama magana a motar kan tace masa.

"Ka gama?". Shuru yayi be ce mata komi ba "Ka buda ni in shiga gida in shikenan". Dan runtse idanun sa yayi in his mind yana fadin

'Don't loose your cool KB. Don't'. He knows khayri is just angry at him and she had every reason to be. Deciding yayi ya rabu da ita tunda ai bayan kwnan uku zai dawo ya maida ta gida. In sun koma koh tana so koh bata so dole ta saurare shi tunda dai tare zasu dinga zama. Power bank dinsa ya cire ya miqa mata dan ta dinga samun charge, ya san zai ishe ta for three days inda suka rage mata a dutsen safe. Kan ta futa daga motar yace mata

SANADI✔️Where stories live. Discover now