Babi Na Biyar (05).

1.5K 209 12
                                    


Kano State, Nigeria.

Tsaye Dattijo yike daga terrace din dakin sa at 3 am in the morning. Cike da takaici ya dan runtse idanunsa ya ja dan dogon numfashi ganin a halin da kabeer da friends dinsa suka shigo gidan. From all indications daga club suke, duk a buge. Ahmad ne ya tuqo su yana parking ya zagayo ya tallafo hannun kabeer wanda koh tafiyar kirki bayayi because he was wasted. A karo na farko cikin shekaru da dama Dattijo ya sama kansa yana zubda hawayen ganin irin rayuwar da Jikan nasa ke leading, tabbas kai sa qasar waje bata amfane su da komi ba in ba lalacewar tarbiyyan da suka basa ba me kyau. Dole ne a yanzu ya dau matakin da ya dace kuma ba komi bane ba face nema wa jikan nasa mace me tarbiyya ayi masa aure koh zai gyaru. With the resolve ya gyara robe dinsa ya koma daki ya kwanta beside his wife who was fast asleep.

Shikam kabeer hayaniyar nephews dinsa Zayn da Zayd ne ya tashe sa da safe. Tunda ya dawo yaran, ýan tagwayen wanda kwata kwata 4 years suke suka liqe masa, a koh da yaushe suka zo gidan basu da wajen zuwa in ba dakinsa ba. Kabeer kuma shima Allah ya dora masa son yaran sosai duk da ba wani shiri yike da mahaifin su ba, khalid, brother din Ahmad. Their relationship was what you'd love to call civil, they spoke only when the need arised, shi khalid dama haka ya kasance mutum mara yawan magana ga Kullum fuskar nan nasa a hade, baa fara'a sam sam, gashi Allah ya basa mata me fara'a da son mutane. Yana gama makaranta be tsaya wasa ba yayi auransa abunsa to his childhood sweetheart Anisa, the daughter of a top politician. Auran su ya sama albarka and a year later they welcomed their twin boys; Zayn and Zayd. At the age of 29, khalid is leading a successful life as a civil engineer with his own construction firm.

Dariya sosai kabeer ya fara sanda yaga yadda Zayn da Zayd suke kwaikwayon rawar Drake as his song "Hotline bling" blasted through the speakers of his room. Argument suka fara on who could do the dance more better kabeer ya tashi ya kashe argument din da ya ja su zuwa waje a cewar su fita shan iska. A qasa da suka tsaya gaida Adda Manga suka tarar da Ahmad ya shigo gidan dan haka shima suka ja sa zuwa garden din da ke cikin makeken mansion din. Da gudu Zayn da Zayd suka fara bin dan puppy din da kabeer ya dawo da shi while kabeer and Ahmad conversed quietly.

"Ahmad". Kabeer ya kira sunan a hankula.

"Yes brother".

"I think i'm in love". Ya fadi calmly. Murmushi Ahmad ya saki not expecting what came afterwards "Zulaikha... I think i'm falling for her". Ya fadi causing Ahmad to choke on his orange juice. Shafa masa baya kabeer ya fara a hankula har tarin sa yayi subsiding.

"Which Zu...zu...laik..ha? Zulaikha Al-fayeed?". Ya tambaya just to be sure.

"Yeah, anything wrong?".

"No! Absolutely no. I'm happy for you". Ahmad ya fadi yana danne bitterness inda yike feeling down his throat "ka fadi mata?". Ya kuma tambaya.

"Not yet, I'm planning to surprise her later".

Murmushin takaici Ahmad yayi kan ya cigaba da ba kabeer karfin gwiwa, burying whatever feeling he had for her. A hankula ya matso kusa da dan uwansa yayi hugging dinsa "In your happiness lies mine, indai being with Zulaikha will buy your happiness back then I'm ready to support you". Ahmad ya fadi meaning every single word. Sun dan dade kadan a haka kan ya miqe stating that he had work which needed to be completed ya wuce ya bar kabeer together with the twins wanda suke ta wasa da joey, the puppy.

.
☆☆☆☆☆
.

Damko dogon gashin da ke kan ta yayi with resentment laced in his tone "You'll get that contract for me from your father". Ya fadi in a commanding tone.

"You're hurting me Abu Zayd". Ta fadi muryar ta na rawa kamar zata yi kuka "Dan Allah ka sakin mun gashi. I've told you father is giving the contract to someone else, na riga fa na masa magana". Mari ya kai mata me zafi. Da sauri ta kai hannunta ta riqe kumatun da ya mara.

SANADI✔️Where stories live. Discover now