Babi Na Saba'in Da Bakwai (77)

591 115 48
                                    


Abuja, Nigeria.

In akwai abunda bata yi expecting faruwar shi ba shine ta shigo courthouse ta ga Niima El-Yaqoob as the lawyer representing Bakhtiar Arab. Masking mamakin da bacin ran ta tayi, it wasn't time to show those emotions, not when she was about to put up the greatest act of her life. Hannunta daya was wrapped in a sling, gefen fuskar ta kam a kumbure idanu jazur haka tayi walking into courtroom din ta zauna a opposite row from where Bakhtiar, his family and line of legal representatives we're all seated. Fara court proceedings aka yi, ba qarya lawyers inda Inno Marte tayi hiring kwararru ne dan sun san aiki sosai, sun san how to manipulate statements and evidence. Ga kuma tarin circumstantial evidences da aka yi gathering against Bakhtiar. Witnesses kam da yawansu aka kira out to testify against Bakhtiar Arab hadi kuma da footages na CCTV camera din gidan Inno wanda yike nuna Bakhtiar on two different occasions trying to harm Inno Marte. Duk sai da aka gama presenting duk witnesses and evidences against Bakhtiar Arab tukun aka yi inviting shi Bakhtiar din to the witness stand to testify.

"Mr Bakhtiar can you tell the court your relationship with the plaintiff?". Wannan tambayar ita ce ta farko da aka fara masa kuma ya basu ansa kamar ya dace cewar ya taba auren diyar Inno Marte, dan haka ita surukar shi ce a da. "Surukar ka ce kuma kuke da d'a tare?". Ya kuma tambaya amma sai miqewa Niima tayi to object to the question wanda luckily alkalin yayi sustaining objection dinta.

"So tell us Mr Bakhtiar did you or did you not sleep with your mother-in-law?". Lawyer da ke representing Inno Marte ya tambaye shi.

"Yes but...". Katse shi yayi yana fadin "No buts. Yes or no". Be kai ga ansawa ba Niima ta sake objecting cewar the lawyer was asking Bakhtiar leading questions amma sai judge din yayi overruling objection dinta, aka ba lawyer din Inno Marte dama ya cigaba da jefa ma Bakhtiar tambayoyi wanda only proved him guilty not innocent. Frustration ya ma Niima yawa kuka ne kawai bata yi ba, she was feeling cluessless because that was her first time handling a case. Sai da aka yi rugu rugu da Bakhtiar aka digging masa an even deeper hole tukun aka sallame sa. Next person da aka kira was Inno Marte wanda ta futo har da shesshekar kukan ta na qarya. 90% din abubuwan da ta fadi duk qarya ne, fabricated story ta basu na yadda Bakhtiar ya mata fyade kuma yayi threatening dinta da kuma how after 23 years he was back blackmailing her, threatening to kill her and Sudais. A karshe ta ce raunukan jikinta ma duk shi ya bata su. Bakhtiar only sat frozen listening to how she narrated her well written story, da ba da shi abun ya faru ba da ya yarda da abubuwan da Inno Marte ke fadi; that was how convincing she sounded. Break aka tafi na two hours dan a ci abinci, masu sallah suyi, masu hutawa suyi su kuma masu Sharia suje su qara regrouping and restrategizing.

"No I want the case finished today. Ka gayawa alkalin haka" Inno Marte tayi maganar da daya cikin amintattun ma'aikatan ta lawyer dinta kuma yana gefe zaune da ita "Sannan su nawa ne a jury din?". Ta tambaya aka bata ansa.

"Send three million naira to each of them now. Harda alkali". Ta fadi masa   "Muna cin case ka qara musu miliyan bibbiyu". Sai da ta gama kaf abunda take yi da su tukun tayi dismissing dinsu duka suka rage ita da lawyer dinta.

"Is there hope?".

Yana washe baki ya ansa ta "Hajia we have already won the case. We've provided the court with more than evidences there's no way he's escaping punishment". Murmushin satisfaction Inno Marte tayi kan tace.

"What punishment are we talking about here?".

"Most probably fine, community service and maybe a year or so in jail".

"What!" Inno Marte ta fadi ran ta a bace. "You call that a punishment?". Bayani lawyer din ya fara mata cewar case din rape ya faru ne can da dadewa dan haka jury din bazasu bada muhimmanci akan wannan ba kuma sannan baku direct evidence proving Bakhtiar's guilt, it could be consensual for all they cared. "So our best bet is the blackmail and assault charges". Inno Marte ba haka ta so ba dan so take Bakhtiar ya wahala matuqa sannan ta zama wanda zata yi saving din sa dan ya dawo gunta; ya zamo nata.

SANADI✔️Where stories live. Discover now