Babi Na Goma Sha Takwas (18).

1.6K 141 24
                                    

Kano, Nigeria.

Ta dawo makaranta kenan ba da dadewa ta ci abinci tana hutawa aka yi kiranta cewar Dattijo na neman ta. Jiki a sanyaye ta miqe ta wuce dan dama tun daren da ya same ta da Ya Kabeer a corridor take iya kokarinta wajen dodging din Dattijo, daga shi har Ya Kabeer din. Hijaab dogo ta dauka ta saka kawai ta wuce, a hanyar sauka ta hadu da Ya Kabeer wanda koh kallon ta be yi ba ya bangaje ta koh sannu babu yayi wucewar sa.

"Kai da Allah" ta fadi a hankula kan ta cigaba da tafiyar ta tana yan gunagunai "Mutum kullum rai a dagule kamar wanda akawa rasuwa. Mugun banza da wofi kawai" jan tsaki tayi kan tayi sallama a kofar Dattijo. Sai da taji ya ansa mata sallama tukun ta tura kofar a hankula ta shiga. A qasa ta zauna kan Persian rug inda yayi adorning portion na well tiled floor in dakin.

"Khayrin Adda da Dattijo" ya fadi fuskar sa cike da fara'a "Koh na Baffah da Inna ne?" Ya tambaya cikin zolaya ita dai kanta a qasa bata ce komi ba sai Yar murmushi da take yi. Farawa yayi da tambayar ta akan karatu da kuma rayuwa cikin gidansa, koh akwai wani abu da ake mata wanda he's not aware of duk ta tabbatar masa da cewar komi lafia lau kuma sosai take jin dadin kasancewa cikin iyalin sa.

"Madallah" ya fadi "Allah ya miki albarka".

A hankula ta ansa da "Ameen".

"Koh kin san meyasa na kiraki kuwa?" Ya tambaya amma ta ce masa aah ita bata sani ba.

"Naje gidanku kwana uku da suka wuce". Dagowa tayi ta kallesa tana jin wani dadi a ranta. Tambayar sa tayi ya ya sama su Baffah yace mata duk lafia lau ya same su. Bayan ya gama ansa mata dukkanin tambayoyinta, gyara murya Dattijo yayi ya kira sunan khayri hankula.

"Maganar da zamuyi yana buqatar nutsuwa dan haka ina fata zaki bani full concentration dinki". Ansa masa tayi da In Shaa Allah, kanta a duqe. Farawa yayi da mata wa'azi irin me kashe jiki, ya sa zuciyar mutum ya karaya. Da kadan da kadan ya fara shigar mata da asalin zancen da yike so ya tattauna da ita dan dama ya so ace ya maida ta gida su Baffah su mata bayanin komi amma yarda da amincin da ke tsakanin Dattijo da Malam Mansur yasa Malam Mansur din cewa ya bar wa Dattijo wuqa da nama, muddin Khayri ta amince da auren toh suma sun amince.

Ba zata ba tsammani taji Dattijo ya furta kudurin sa na ganin jikansa ya aure ta. Kasa cewa komi Khayri tayi dan al'amarin ya matukar bata mamaki, ya sa ta fadawa cikin tunani.

Koh dai ba'a Dattijo ke mata? Amma kuma koh zai mata wasa sai da irin wannan al'amarin?. Ta ya ma zaa ce wai ita Khayri, Yar kauye da ita zata aura Ya Kabeer bayan babu wani batun so tsakaninsu, hasalima tun zuwanta garin kano ta lura da cewa kwata kwata jinin Ya Kabeer be hadu da nata ba dan gaba daya ba abunda ke hada shi in ba zagi ba da kallon banza. Lokuta da yawa zai yi yan uwansa Mahra da Billie kyauta tana wurin amma koh kallo bata ishesa bare itama ya mata ihsani. Sannan yanzu ace zaa musu aure. Tana cikin wannan tunani a zuciyar ta taji muryar Dattijo.

"Batun boye boye ya qare tunda har Allah ya sa kunnuwa suka jiye mun, idanuwa na kuma suka gane mun komi, dan haka ba tare da bata lokaci ba nike so ayi auran nan. Mun riga mun yi magana da Kabeer, ya kuma amince naki go ahead din kawai muke jira a fara shirye shiryen auran ku". Dagowa tayi da sauri ta kalla Dattijo fuskar ta cike da mamaki.

"Ya Kabeer ya yarda?" Ta tambaya.

"Kabeer ya amince kuma in so samu ne a daura auran ku kan komawar sa dan haka nike baki daga yau zuwa gobe kiyi shawara. Ina nan ina sauraron amsar ki". Ya fadi kan yace ta miqe ta wuce. Jiki ba wani kwari ta miqe, da kyar kafafunta ke jan jikinta har ta haura sama ta wuce dakinta ta zaune gefe gudu shuru. Ta rasa abun yi, murna zata yi koh kuma fargaba? Tama rasa me ke mata dadi gaba daya.

'Wai ta ya Ya Kabeer ya amince ya aure ni?' har barci ya kwashe ta daren ranar tunanin da take ta yi kenan. Nan qasa inda ta zauna barci ya kwashe ta dan farkawa tayi cikin dare ta sama kanta kwance kan tiles din. Bandaki ta shiga ta dauro alwala ta dawo ta shimfida sallaya ta hau kan zubo nafila, tana Allah ya bayyana mata mafita cikin wannan al'amari da ke shirin faruwa da ita.

SANADI✔️Where stories live. Discover now