Babi Na Hamsin Da Tara (59)

501 113 26
                                    


Unedited chapter alert😂😂

***************************

London, England.

Kamar yadda mommy ta fadi mata, Khayri na cika wata da zuwa London aka fara zuwa mata karatu. A study din gidan aka yi mata setting up komi da zata buqata na karatu malamai uku suka fara zuwa so uku a sati suna mata karatu. Akwai Mr Richardson wanda yike zuwa on Mondays to teach her science courses sai Mrs Anand me zuwa Wednesdays to teach English, arts and history. Ranar jumu'ah kuma Sheikh Izzuddeen ke zuwa yana koya mata karatun arabi. Karatun da ta fara ya sa ta rage zama cikin kadaici, she now had things to take her mind off things. Kabeer kuma sai su jera sati biyu har uku ma wasu lokutan basu hadu ba dan wasu ranakun ba ma ya kwana gida kuma ta lura yana yawan tafia amma koh fadi mata baya yi bare kuma sallama. Halinsa kuma na drinking and partying ba wai ya daina bane. He did whatever he wanted dan ya san Khayri bata da baki da shi kuma tsoron sa da ya riga ya sa mata a ran ta bazai bari ta kai qaransa gida ba.

Su mommy basu kawo ma khayri ziyara ba sai da ta yi wata biyu tukun. Ranar Kabeer yana gida yana barci dan the previous night he was out partying all night, sai karfe biyun dare khayri ta tashi nafila taji shigowan sa be kuma yi barci ba yayi ta zane zanen sa har sai bayan asubah dan haka throughout that day he was sleeping. Cikin muryar barci ya ansa kiran mommy tana ji ta fara masa tsiya tana har yanzu suna honeymoon mood ne barci haka har rana. Biye mata yayi sukayi ta raha kan tace masa suna hanyar zuwa.

"We'll be arriving in an hour or so". Lokacin Kabeer ya tuna cewar tun sati guda da ya wuce mommy ta fadi masa zuwan su kwata kwata ya mance. Fatan isowa lafia yayi musu kan ya miqe a guje ya sauko qasa yana kwalawa khayri kira at the same time yana danna wayansa trying to order lunch dan ya mance so ba abunda suka shirya dan tarbar baqi. Tana daki kwance tana karatu taji kiransa, sanye take da sweatpants and shirt kan ta ba hulla dogon gashin ta da ke ta kyalli a tufke, ya sha gyara.

"Mommy suna hanyar zuwa. Ki hau sama ki gyara dakin nan, gaba daya kayana ki sauko da su ki maida dakin da kike kwana" ya fadi koh please babu. Toh kawai ta ce masa kan ta hau sama dan aiwatar da abunda yace. Sarai Kabeer ya san halin mommy kuma ya san bakin ta daya da Maamah, duk abunda tazo ta gani sai ta fadin mata dan haka be so ya basu any room for doubt. Kuma ya san in har baa yi clearing out dakinsa na sama ba mommy na gani zata gane nan yike kwana kuma daga nan zaa sanya musu alamar tambaya.

Kabeer ya kai forty-five minutes kan ya dawo riqe da take outs da yawa na abinci kala daban daban da ya siyo. Zuwa lokacin khayri ta gama gyaran dakin, yan few kayan sawan sa da suke sama da toiletries duk ta maido da su master bedroom har ta shiga ta sake watsa ruwa ta shirya. Ta gama saka dan kunne kenan to finish her look ta jiyo shigowan sa, kitchen ya wuce ya ije take outs din ya shigo bedroom din shima to get ready. Bathroom ya shige itakuma ta futo ta wuce kitchen ta fara microwaving abincin tana dishing dinsu a casseroles. In record time Kabeer ya gama wanka ya shirya. Slacks ya saka da shirt dinsa na Hugo boss. Qafafun sa sanye da black socks ya futo yana ta kamshin turare, his mop of black hair still wet from the shower. Shima kitchen din ya wuce dan ya saka mata hannu su gama komi kan baqin su su iso. Sai a lokacin ya tsaya ya qare ma khayri kallo. Bayan ta a juye bata ankara da shigowar sa ba. Sanye take da wani peach coloured wrap dress which had floral patterns. Sosai rigar ya kama jikinta in all the right places kuma dama Allah yayi ta da dan jiki ga kuma figure me kyau. Gashin kanta ta daure shi in a peach coloured turban tana aikinta tana waqa softly.

'When did she learn to dress like this?' Yayi tunanin a zuciyar sa. Feeling presence din mutum da khayri tayi ya sa ta juyo shikuma sai ya sha mur ya yi hanyar fridge yana duba beverage inda suke da shi a fridge din. Cigaba khayri tayi da aikin ta tana ta warming abinci tana dishing. Bayan ya rufe fridge din ya zo ya fara setting table. Matsowa yayi bayan ta dan cabinets inda suke ije plates na saman daidai inda take tsaye tana aikin ta. Leaning yayi to take some plates, hakan ya sa jikinsa ya shafa nata, action din ya sa khayri tayi freezing momentarily. Shima Kabeer a nasa gefen wani irin yanayi yaji ya fara shiga, dan tun dama shigar da tayi ya riga ya riga tafin masa da hankali, ga kamshin turaren da ke ta tashi daga jikinta and now this contact; it was going to be the end of him. Gyara murya kawai yayi ya ja plates din ya wuce yayi setting. Da ya dawo dan deban bowls sai ya sama kansa da tsayawa kawai directly a bayan ta yana kallonta. Sosai ya fara having an urge to touch her, to have any kind of skin contact with her. Tunda ya shigo ita kam khayri dama kawai taji gaba daya she wasn't comfortable dan haka ta kasa sakin jiki tayi aikin. Allah Allah kawai take ya futa koh kuma ita ta gama ta fice ta basa wuri. Ba zatto ba tsammani khayri taji mutum kusa da ita, sajensa na shafar gefen fuskar ta, his nose sniffing on her neck.

SANADI✔️Where stories live. Discover now