Babi Na Talatin Da Takwas (38).

742 149 14
                                    



Tsaf Kabeer ya gama shirin sa cikin kayan da Maamah ta aiko masa. Shadda ce me tsada, sky blue in colour ya sha aiki ga hular sa ma blue, loafers din qafansa baqaqe sabbi pul ranar ya fara sa su, daga saman sa har qasa komi nasa sabo ne. Ba karamin kyau yayi ba da ya gama shiri ya sha dark shades abunsa. Ahmad ma yayi kyau cikin wata cream coloured shaddar sa with brown cap and shoe. Duk da ka gansu kaga hutu kaga naira. Dattijo kam da uncle Sadiq shadda suka sa farare qal sun sha aiki, Dattijo harda nadin sarauta aka masa na rawani fari tas, harta takalman qafarsa farare ne, walking stick nasa ma me touches of white. Shades din idanunsa ne kawai dark.

Sanda Maamah da Adda Manga suka ga Kabeer har kuka suka fara dan sosai ya tuno musu da mahaifin sa. Da kyar suka rarrashi kawunan su suka rage hawaye. Duqawa yayi Adda ta rungume shi, sun dade a haka tana ta yi masa addu'a mutanen da ke dakin nata ansawa da Ameen. Har sai da aka shigo aka ce zasu makara tukun ta sake sa ya futa suka wuce. Convoy aka hada na manyan motoci dauke da manyan mutane sai Dutsen safe. A ranar dai garin Dutsen safe ya cika sosai da Jama'a, mutane na alfarma masu fada a ji a qasar duk sun hallara, koh ina ya cika. Koh ina ba wajen saka qafa.

Bayan sallahn zuhr ne aka daura auran Muhammad Kabeer Dikko tare da amaryar sa Ummul-Khayri Aliyu Mansur akan sadaki naira dubu dari biyu da hamsin wanda uncle Sadiq ne ya biya masa ba dan Kabeer din bayi da shi ba, sai dan tsananin gatan da ake masa.

A fadar hakimin garin aka shiryawa yan daurin aure yar walima, kuma iya gwargwado an ci an sha anyi hamdala. Sosai shima Malam Mansur yayi kokari dan ya san girma da qimar Alhaji Muhammad Dikko da kuma mutanen da yike hulda da su. shanu guda qato daga garken sa yasa aka kada aka yanka da kuma kaji da yawa, ruwa na gora ya siya da kuma drinks na gora da na kwali, girki kam yan uwansa wanda sukazo daga birni ya bawa dawainiyar girkin walimar yan daurin aure dan dai ayi abu cikin rufin asiri. Sosai aka dinga yabawa da kokarin Malam Mansur dan kowa da yazo wajen an ci an sha an qare lafia. Ba a wani jima ba aka fara juyawa dan komawa garin Kano, su dai Dattijo sai da suka shiga cikin gida aka gaisa da mutane aka kuma dau hotuna dan dama da photographers suka taho ana ta capturing every single moment of the event, tun daga sanda motoci suka daga daga garin kano. Shima Kabeer din ya shiga an gaisa da yan uwa da baqi anyi hotuna kan suka futo suka wuce. Itama amarya ba a wani bata lokaci ba aka fara shirya ta dan dama motocin da zasu dauko ta da yan uwanta da abokan arziki tare suka taho da yan daurin aure dan haka futowar ta kawai ya rage, motoci na jere suna jira. Ahmad shi ne yayi jagoran tafiyar tare da wasu daga cikin yan uwa da abokan Kabeer da aka tafi aka barsu da responsibility din dauko amarya. Suma few matan da aka taho da su daga kano aunties din kabeer da kuma wasu daga cikin friends din Maamah suna cikin gidan biki an basu ci da sha an karrama su. Hajia Asma'u mahaifiyar Anisa tare da Hajia Indo wanda ta kasance yaya a wajen mahaifiyar Kabeer su suka yi jagoran tafiyar masu dauko amarya. Karfe uku daidai aka futo da amarya, Khayri ta sha atamfar ta super wanda Maamah ta bada aka yi mata dinki na alfarma, an lullube ta da qaton veil sai kuka ta ke ta ci. Cikin motar Ahmad aka saka ta, Hajia Asma'u da Hajia Indo su suka zauna da ita a motar. Driver ne ya ja motar sai Ahmad da ke zaune a passenger seat. Sauran kawaye da masu rakiyar amarya suka shiga motoci aka kama hanyar Kano su kuma sauran Jama'a suka cigaba da shagalin biki.

Kiran sallar maghreb yayi daidai da isowar su gidan Maamah a inda nan ake ta shagalin biki. Sosai aka yi maraba da su, Maamah bakinta kamar zai yage da murna an kawo musu amaryar su. Dama already ta riga ta sa an buda guest chalet din gidanta an share koh ina tas an gyara dan haka nan aka sauke yan rakiyar amarya wanda kwata kwata basu wuce su goma sha biyu ba, Inna tace kar ayi musu zuga dan already ba karamin dawainiya suka dauke musu ba kar kuma aje a daura musu wani nauyin. Cikin mutane goma sha biyun, mutum hudu ne kawai kawayen amarya dan haka su cikin gida aka sauke su tare da amarya, extra rooms din cikin gidan aka gyara musu. Ita kuma amarya Maamah tace a dakinta zata kwana.

SANADI✔️Where stories live. Discover now