Babi Na Talatin Da Tara (39).

729 141 31
                                    

Kano, Nigeria.

Motsin da taji ne ya sa ta buda idanunta softly, cikin idon barci ta hango retreating figure dinsa. Ya shigo dakin straight away ya wuce hanyar bathroom. Ba a wani jima da wucewar sa ba taji da qarar shower alamar ya shiga wanka. Wayar ta da ke by bedside drawer inda ke side inda ta kwanta ta daga ta duba time, it was past ten already and it was so unlike her tashi latti amma saboda tsananin gajiyar biki tayi oversleeping kuma koh a wannan lokacin ba wai barcin ya ishe ta bane. Kabeer sai da ya gama shirin sa tsaf ya saka riga shirt da shorts ya taje kai ya fesa turare kan ya futo ba tare da ya kalla gefenta ba ya futa abunsa. Dan dogon numfashi Khayri ta ja a zuciya kam tana fadin

'Akwai sauran aiki'.

Hamma tayi sanna tayi miqa kan tayi reciting du'a ta miqe tayi hanyar bathroom din itama. Har zuwa lokacin bandakin kamshin body wash dinsa yike. Wanka tayi da ruwa me shegen zafi ta gasa jikinta sosai kan ta futo tayi shirin ta tsaf. Wata atamfa ta ciro, super wax green in colour wanda aka yiwa dinki na alfarma, doguwar riga ya sha aiki yayi kyau. Tana gama shafa mai ta bi jikinta da turaruka kan ta sanya rigar ta zauna ta yi dauri dan dama indai dauri ne ba laifi Khayri ta iya. Sosai tayi kyau sai sheqin amarci take. Bedroom din ta koma ta duba gadon be wani baci ba, straightening din sheets din tayi ta ninke duvet inda ta rufa da kan tayi bracing kanta. A hankula ta sauko qasa ta same sa a living room din qasa zaune yina playing game. Har qasa ta durqusa ta gaida shi a ladabce shikuma ya ansa mata sama sama ba tare da ya kalla fuskar ta ba.

"Ga abinci can dining Maamah ta aiko". Ya fadi mata. Tambayar sa tayi koh tayi serving dinsa ne yace mata aah shi baya jin yunwa "Amma ki bani coffee". Ya fadi tace toh ta miqe ta wuce. Kitchen ta wuce straight ta fara brewing masa coffee. Ruwan coffee din na zafi ta juye a ceramic jug kan ta duba fridge ta sama milk ta dauka, in no time ta hada komi da komi akan tray ta wuce masa da shi. A table inda ke gefen sa ta dire masa kayan tayi wucewar ta dining don yin breakfast. Abinci kala kala ta tarar Maamah ta aiko musu, deban wanda ranta ke so tayi dan daidai amount inda ta san zata iya ci. A hankula ta fara ci hankalin ta na can yayi nisa cikin tunani, ji take tun a wannan lokacin ta fara karaya tana ganin kamar bazata iya ba. A hankula tayi ta cin abincin ta har ta gama tayi clearing table din ta wuce da kayan kitchen zuwa lokacin shima Kabeer ya gama shan coffee dinsa ta wuce ta kwashi kayan ta wuce kitchen da su ta wanke duk dirty utensils din ta goge su ta maida kowanne mazaunin sa kan ta wuce sama ta shige daki ta kwanta. Wayar ta ta jawo ta dan buga game har ta gaji barci ya dauke ta.

Khayri bata farka ba sai lokacin zuhr, alwala ta wuce tayi tazo ta gabatar da sallah. Tana kan sallayar bata gama du'as ba taji qarar bell din side dinsu yayi ringing har so biyu hakan yasa ta miqe koh hijaab din jikinta bata cire ba ta sauka qasa taje ta buda qofa. Me aiki ce dauke da basket din kayan abincin rana, gaisawa da Khayri suka yi me aikin na mata Allah sanya alkhairi. Duk yadda Khayri tayi me aikin nan taqi miqa mata basket din kayan abinci, ita ta wuce da shi har kitchen ta ije.

"Ga wannan kayan ki wuce cikin gida da su, abincin sun mana yawa". Khayri ta fadi tana nuna mata warmers din kayan abincin safe. Me aikin na futa Khayri ta duba kayan abincin tuwo ne da miyar kubewa ya sha nama, dayan warmer din kuma peppersoup ne na cowhead sai jug din zobo me sanyi. Setting table tayi for Ya Kabeer tana gamawa ta wuce sama dan ba yunwa take ji ba. Wayanta ta daga bayan ta shiga cikin daki ta fara kiran yan uwa da abokan arziki wa inda take ganin ya kamata ta kirasu ta musu godia da kuma fatar duk sun isa gida lafia. A karshe ta kira Baffah suka gaisa shima tayi masa godia, yace mata baya gida tace in yaje gida sai ya kirata dan su gaisa da Inna. Dukansu ba wanda ya ci abincin rana har lokacin na dare yayi aka sake aiko da na dare, haka Khayri ta sake bada warmers din abincin aka shiga main house da su, zobon kawai ta ije a fridge dan taga Ya Kabeer ya sha kadan watakil ya qara sha kuma. Abincin daren ne ta zuba dan kadan bayan sallar isha'i ta ci. Tana gamawa ta zauna a qasan ta dau remote ta fara searching for channels daga baya ta barshi a Aljazeera, dama ita ma'abociya son kallon labaru ne barin ma na qasashen turawa duk saboda turanci ya zauna bakin ta itama. Wasu lokutan har zama take da takarda da pen, duk word inda ta ga ya futo a headlines wanda bata sani ba ta rubuta daga baya ta duba ma'anar word din a dictionary. Tana cikin kallon news din Ya Kabeer ya sauko daga sama rusunawa tayi ta gaida shi amma koh kallonta be yi ba ya wuce hanyar dining. Miqewa Khayri tayi ta bi bayansa dan serving dinsa abinci amma sai ce mata yayi baya buqata.

SANADI✔️Where stories live. Discover now