Babi Na Talatin Da Biyar (35).

711 135 12
                                    

Abuja, Nigeria.

By 7:47pm su Kabeer sun isa venue din dinner din, dama ance musu akwai one hour red carpet event and interview starting by 7:30 dan haka koh da suka isa photographers da yan jarida sun cika koh ina da kuma guests suna ta arriving. A wata arniyar Mercedes Benz suka isa, driver ya jawo su, su kuma yan mata suka iso a Ford edge inda suma driver ya tuqo su. Ahmad da Kabeer suka wuce cikin takun su na qasaita sai hotuna ake ta musu aka dan yi interview da su akan couple din, wa suka sani a cikinsu and what can they say about them. Su na gamawa suka wuce wani usher ya duba invite dinsu ya kai su har zuwa seats dinsu, tables anyi shi ne for six people kuma Ahmad da Kabeer su ne farkon isa table dinsu dan haka suka zauna suka dan fara hira abun su suna zuqar cocktail drinks. Suma yan matan sun je sun sha hotuna sunyi interview kan aka nuna musu waiting room inda duk friends masu asoebi zasu jira har sai lokacin da akayi allotting for shigowar su yayi. Da haka da haka mutane suka yi ta zuwa ana ta interviewing dinsu ana hotuna, biki dai irin na manya.

Niima tayi kyau matuka gashi dai make up da aka mata ba wani heavy one bane amma da yike tun asali ita din kyakyawa ce sosai sai make up din yayi complimenting beauty dinta. Wani gown red ta saka, an dinka shi to fit her slender figure, ta qasan kuma ya dan buda, takalmin qafar ta ma red ne amma a darker shade sai dankwalin da aka daura mata shima darker shade of red, more like maroon, yayi complimenting shoe dinta, jewelry dinta simple ones made of zirconia with Swarovski stones adorned on them. Kawayen ta kuma sun sha adon su cikin gowns na gold coloured lacey material, kan su ma gold head suka daura duk sun yi kyau da su.

Laylah Al-Haydar ce ta shigo dakin cikin adon ta, tana sanye da wani haddaden riga emerald green, tayi kyau sosai itama ta tambaya koh an gama dan motoci sun zo already. Koh da aka futa harabar gidan sai da photographers suka yi ta daukar newly wedded couple din hotuna kan aka buda musu bayan limou suka shige kawaye ma aka shige motoci aka wuce venue.

Koh after red carpet event din, welcoming guests da suka zo aka yi da wanda suka zo from different places in Nigeria da kuma wanda suka zo from other countries. Iyayen amarya aka fara welcoming Hajia Karimatu ta shigo da kawayenta suna rawar su na alfarma sun sha laces dinsu masu tsada ga jewelries kala kala masu tsada, kowacce da irin nata. Itama Karimatu kamar ba maman amarya ba ta sha kyau abunta, ta dawo kamar wata sweet sixteen. Su dama maza da yike ba wani ruwansu da raye raye and the rest duk sun sama wuri sun zauna, Alhaji Abdallah da abokan sa na arziki duk suna wajen da sauran maza dangin Bakhtiar duk suna nan. Sai da Hajia Karimatu da tawagar ta suka zauna suka yi settling a section inda aka reserving just for them tukun aka yi welcoming the Al-Haydars, algaita kawai kake ji yana tashi da sauran local instruments ana wani sauti na girma da kasaita. sai wani me kirari yana ta wasa Sahar Al-Haydar tare da Yasmeenah Al-Haydar gefensu kuma ga surukansu Laylah Al-Haydar da Saima Mohammed. Suma sosai kowaccen su tayi kyau abunta, shikam me kirari ya sha kyautar kudi. Suma sai da suka yi settling tukun aka yi welcoming friends na ango, suma da yike manyan maza ne basu wani taka ba suka shigo ana kirari suna ta watso kudi. Ba a ga cashewa ba sai da kawayen amarya zasu shigo, tsakanin su da Allah suka cashe abunsu kowa tana iya rawar da ta iya gashi duk sunyi kyau in their beautifully tailored dresses and impeccable make ups. Suna settling aka sake welcoming mutane kan aka tashi to give the new couple a standing ovation. "Pop something" by Dr sid ne ya fara blasting through the speakers (I think it was one of the hottest jams then😂). Suna shigowa aka fara throwing confetti all over the place suna ta takunsu a hankula, dai-dai kamar suna tsoron qasa hannunsu cikin na juna. Niima a bit shy, shikuma Bakhtiar so full of confidence with a look that reeked of so much power. Suna isa dancefloor kawayen amarya suka miqe suka fara taya su takawa har music din yayi ending aka yi ushering dinsu to their seats.

Sai a lokacin su Billie suka nema hanyar table dinsu inda zasu zauna together with Ahmad and Kabeer. Aikam dukansu mamaki ya kama su da suka sama Ya Ahmad da Ya Kabeer zaune da wani a gefen su sai hira suke kamar wanda suka san juna. Ko da suka isa table din Sudais Abiso suka tarar, guy inda Ya Kabeer yayi introducing dinsu to a cinema the other day cewar sun san juna tun a UK. Zama suka yi, Billie ce ta zauna next to Sudais, ita kuma Mahra next to Ya Ahmad dinta Khayri kuma gefen Ya Kabeer.

SANADI✔️Where stories live. Discover now