Babi Na Arba'in (40).

871 147 24
                                    

Daren ran alhamis bayan Khayri tayi serving dinsa abinci ta wuce ta zauna a living room tana kallo Kabeer ke mata maganar tafiyar su.

"Ki hada kaya, gobe da yamma muna da tafia". Toh kawai Khayri ta fadi ba tare da ta kallesa ba "One week zamuyi". Ya sake fadi ta ansa shi da toh. Jira tayi har sai da ya gama cin abinci ya dawo ya zauna living room din kan ta miqe tayi clearing table din ta haura sama ta fara hada kaya. Daidai kayan da zasu mata one week ta dauka da extra pair sai kayan barci da inner wears dinta. Tana gamawa ta hada kayan shafa suma, daren dai kan ta kwanta sai da ta tabbata ta hada komi da komi na tafiyar tukun.

The next morning tun safe Ya Kabeer ya futa ya rage Khayri ita daya zaune shuru ta rasa abun yi. Tun tana kwance tana ta juye juye kan gado har dai ta miqe ta futo zuwa living room inda ke sama ta kunna kayan kallo, koh zama bata yi ba taji belling na ringing dan haka qasa ta sauka straight away to check who was on their door. Sosai tayi murna da ta buda taga Mahra ne da Billie, suma sosai sukayi murnan ganin Khayri sai kace basu hadu ba the previous night.

"Amarya baki laifi". Mahra ta fadi kan ta qara da "Ina yayana?". Ba tare da Khayri ta kalli Mahra ba tace mata ya futa tun safe. Sama suka wuce suka zauna living room ita kuma Khayri sai da ta shiga kitchen ta kawo musu ruwa da refreshments tukun tayi joining dinsu a sama. Kallo suka fara jefi jefi ana dan hira har Billie ta dawo maganar tafiyar su Khayri. Tambayar Khayri tayi koh ta gama hada kayan tafiya dan lokaci nata gabatowa, Khayri tace mata eh ta gama hadawa.

"Muje ma naga abubuwan da kika yi packing dan na san ki da iya kwafsawa". Billie ta taso Khayri a gaba har zuwa bedroom dinsu ta buda trolley inda Khayri ta gama hada kayan tafiyar ta tsaf "La haula! Khayri me wannan" Billie ta fadi tana ciro wata lace da khayri tayi packing "Dan Allah Mahra jubi, da wannan nighties din zaki bi miji Lagos?". Ita dai khayri nata kallon ikon Allah bata ce musu komi ba. Nan da nan suka juye kayan da Khayri ta hada, Mahra ta fara maida su closet tana arranging dinsu Billie kuma tana lalubo wasu kayan da zasuyi befitting tafiyar da Khayri zata yi. Abayas suka ciro mata da English wears yawanci maxi dresses and skirts masu kyau da tsada wanda Maamah ta hada mata cikin lefe. Bayan Mahra ta gama mayar da wancan kayan tazo ta fara arranging sabbin da Billie ta fiddo su. Tana gama ciro kayan sawa ta koma section din inner wears da nighties ta fara ciro wasu very skimpy ones.

"Gaskia ni bazan iya saka wa'innan ba". Khayri ta fadi tana turo baki.

"Mene zai hanaki saka su".

"Kawai dai". Khayri ta fadi dan tama rasa excuse inda zata bada "Ni gaskia bazan iya ba, tare fa da Ya Kabeer zamu tafi".

"Toh mijin ki ne ai shi yanzu".

"Gaskia aah, kawai ki maida mun wanda kika ga na ciro. Gara gara su".

"Toh baza a maida ba. Wannan din zaki tafi da". Billie ta fadi tana tura su cikin akwati "Ai na gaya miki Mahra muna da aiki sosai akan wannan Khayrin kan ta tafi London. Kunya zata dinga bamu". Mahra kallon Khayri kawai tayi tana dariya. Ita kam Khayri kwata kwata abun baya bata dariya, hasalima gab take da ta fara zubda hawaye dan already fargaba sosai take akan tafiyar da zasuyi daga ita sai Ya Kabeer ga kuma yanzu Billie tazo tana qara complicating mata al'amarin. Danne hawayen ta tayi dan bata so su zubo a gaban su Billie, ta dau hijaab dinta dogo ta dora kan kayan. Wani kallo Billie tayi mata Khayri tayi sauri ki fadin "Na sallah ne".

Bayan sun gama hada kayan tsaf suka zauna da Khayri suna ta bata shawarwari iri iri akan yadda zata dinga bi tana jawo hankalin Ya Kabeer ita kam Khayri jin su kawai take yi, shawarar su na shiga ta kunnen hagu, suna futa ta kunnen dama.

'Da kun san yadda ya tsane ni'. Ta fadi a zuciyar ta.

Miqewa su Billie suka ce zasu wuce dan Maamah ma bata san da zuwan su ba, sosai ta gargade su akan damun the newly weds, tace a basu space and time to enjoy their time together kan a fara damunsu da ziyara. Hugging din Khayri suka yi suka mata fatan Allah ya kiyaye hanya dan by the time da zasu wuce, su Billie suna gidan Maamah.

SANADI✔️Where stories live. Discover now