Babi Na Casa'in Da Daya (91).

625 116 25
                                    


Abuja, Nigeria.

Anyi seven days da rasuwan Suraiya kan Hadiza da Zahriyya suka wuce. Sudais da kansa ya kai su airport, ya rungume su suka yi sallama bayan ya musu alkawarin zasu ding communicating more frequently kuma zai dinga zuwa.

"Take care of yourself". Hadiza ta fadi kissing his forehead. Wani irin sabon son sa taji ya shiga zuciyar ta yanzu da ta gane nephew din ta ne shi. The only piece of her sister she had left, she was going to love and cherish him.

The next day da safe Niima sun sauko breakfast sai ga envelope an kawo mata wai saqo ne ya iso aka ce ita zaa ba ma. Koh da ta duba kan envelope din sunan ta ne a rubuce. Mamaki ne ya cika ta, wa ne zai aiko mata da envelope kuma me ke ciki?. Sama ta koma ta sama Bakhtiar, tare suka zauna suka buda envelope din. "You know you don't have to do this. Na san wannan abun daga inda ya futo".

Dan shafo sa tayi tana fadin "It's okay love. She can't hurt us anymore. Let's see what her last move was, we could use some laugh". Kissing gefen kan ta yayi yana ba tare da yace komi ba.

"I remember this accident" Bakhtiar ya fadi holding the newspaper clipping "the news was everywhere when it happened. Hatsarin mota tsakanin tanker din petroleum da qaramar mota. Claimed the lives of a whole family". Bakhtiar ya fadi.

"One of the girls survived". Ta fadi, showing Bakhtiar inda aka rubuta hakan.

"Who is this girl with Ummi and Abba?". Niima ta fadi quietly. She was trying so hard to remember where she had seen the girl. Sai daga baya ta tuna inda ta ga hoton, a safe din Ummi. Hoton da kakar ta tace mata cewar ita ce but even though they shared a slight resemblance, Niima bata ji itace a wannan hoton. Hannunta rawa ya fara yi zuwa sanda ta dau third picture din, i'ina ta fara "What am i doing with these people. W.wh.who are they?". Bakhtiar ne ya dau newspaper clipping din yana dubawa, idon Niima na fadawa kan shi ta ga hoton mutanen da aka ce sun mutu a hadarin, it was the same picture she was holding in her hand. Da sauri ta jefa hoton gefen tana fadin

"Me nike yi da mutanen nan da suka mutu. Their daughter died B, why's my picture there with them? What am I doing there?". Janyo ta zuwa jikinsa yayi yana dan murza shoulder din ta just to reassure her. Sai da ta dan yi calming down tukun ta fara duba sauran abubuwan da ke gaban ta. Hoton yarinyar da ta gani earlier in a picture with her Ummi and Abba ne, a bayan hoton an yi rubutu kamar yadda da aka saba ana yi a bayan hoto, a rubuta date da occasion inda aka dau hoto to preserve the history of the picture. A bayan wannan gani tayi an rubuta

18th April. On the third birthday of our lovely daughter Ni'imatullah Abdallah El-Yaqoob.

Zuwa lokacin kan ta ya gama daurewa ta rasa what  to making  of these strange photos, and this girl  who has her name. Koh dai Ummi da Abba sun taba haifar wata yarinya ne da ta rasu in her childhood? Amma kuma 18th is her birthday so wouldn't it be too much of a coincidence ace iyayen ta sun taba haihuwar yarinya me sunanta kuma born on the same day as her? Tayi voicing wannan to Bakhtiar who only told her that stranger things happen in the world. Shuru tayi ta cigaba da duba sauran abubuwan. Next hoton na yarinya ce yar kimanin shekaru uku riqe da jinjira a hannun ta. Sai kuma wani tsohon hospital result na blood tests din iyayen ta. Koh date din jikin result din was old, it was from the early 90s.

Wani abu ne yayi occurring to her "Ni AS ce" ta fadi a hankula. How could her parents both be AA ita kuma ta zama AS? Tun kan tayi magana Bakhtiar ya bata ansa as if he were reading her mind.

"This result is from the nineties. There could be inaccuracies". Hannu na rawa ta duba final two documents din. Birth certificates ne na Ni'imatullah Abdallah El-Yaqoob who was born on the 18th of April, 1991 and has blood genotype AA. Second one din kuma na Umm-Kalthoum Aliyu Mansur ne, born on the 2nd of January 1992 with blood genotype AS.

SANADI✔️Where stories live. Discover now