Babi Na Sittin Da Daya (61).

502 121 31
                                    


London, England.

Tun da suka mota khayri ke ta sharara kuka bata kuma daina ba har suka isa wani qaton gida a wani street da khayri zata iya kirga koh kwata kwata gidaje nawa ne. Wani abu taga Niima ta danna gate ya bude automatically, daga gate dinma suwa main house din akwai dan tafia dan koh a mota it'll take one a whole minute kan ka kai gaban gidan. Tsayuwar motar ke da wuya wani ma'aikacin gidan namiji ya taho ya tsaya yana jira uwar gidan nasa ta sauko ta miqa masa key din mota ya kai motar garage.

"Toh kukan nan dai ya isa". Niima ta fadi tana tabo kafadan khayri "Mu je ciki ki kintsa". Reluctantly khayri ta biyo ta zuwa cikin gidan wanda sosai ya hadu da kaya na zamani. Suna shiga me aiki ta taho ta ansa coats dinsu ta wuce da su bayan ta musu barka da dawowa. Juyawa khayri tayi to take in everywhere, tsananin girman gidan khayri ta san aqalla masu aikin gidan zasu kai hudu koh biyar. Sama Niima ta riqo hannun ta suka wuce bayan ta ma wata me aiki magana akan ta aiko musu tea upstairs. Nan Niima ta ma khayri masauki a wani living room me kyau a saman tace mata gata nan zuwa. Ta kai ten minutes kan ta dawo zuwa lokacin tea inda tace a hada an hayo sama da shi.

"Bismillah" tace tana ma khayri murmushi.

Hada tea sukayi dukansu kowacce ta zauna quietly sipping her tea. Sun kai fifteen or soon minutes ba wanda yace komi. Khayri har zuwa lokacin abunda Ya Kabeer ya mata na nan yana qona mata rai, Niima kuma tana son tayi magana amma ta rasa me zata ce mata.

"Dama nan kike zama" duka suka fadi a lokaci daya. Kallon juna sukayi suka yi Niima ta fashe da dariya. Khayri ma wadda akwai sauran hawaye a fuskar ta dariyar take yi. "You go first". Niima ta fadi. Tambayar ta khayri ta sake yi cewar dama a England take itama.

"Aah, hutu muka zo ni da miji na. Ke fah".

"Nan muke". Kawai ta fadi quietly Niima ta daga mata kai "Ban dai cika shekara da zuwa ba". Daga nan basu sake magana ba, shurun da yayi ma Niima yawa ta daga remote ta kunna tv. Dukansu kallon TV din suke ba dan suna son kallon ba kuma hankulansu gaba daya ba kan TV din yike ba. Duka tunanin ta yadda zasuyi initiating chat da juna suke yi.

"Har yanzu malamar asibitin kike so ki zama?". Niima ta tambaya.

Yar dariya khayri tayi kan ta ce "Baki mance ba". Murmushi Niima ta mata tace bata mance ba duk conversation inda suka yi having tana tune da shi.

"A wacca unguwa kike?" Niima ta tambaya sai dai bata jira ansa din khayri ba ta kuma jefa mata wata tambayar "Me sa kike ta kuka?". Dago kai khayri tayi suka hada ido kawai for no reason taji she trusted Niima El-Yaqoob, kawai taji tana son fadin mata gaba daya halin da take ciki. Yadda suka yi da Kabeer ranar a mall din ta kwashe ta fadin ma Niima wadda tayi paying attention to khayri. Kan ta kai karshen labari ta sake fashewa da kuka. Tasowa Niima tayi daga kujerar da take zaune ta koma kusa da khayri ta fa jawo ta jikinta tana ta kokarin bata haquri.

"Na gaji, na wulakanta a hannun mutumin nan. Tun da na zo garin nan yike wulakanta ni, ya san baya so na ya aure ni? Sai kace rashin gatan duniya kai na ya qare. Bazan iya ba". Niima bata hana ta pouring heart din ta ba, barin ta tayi ta dinga expressing kanta cause she knew cewa khayri zata sama relief in har tayi pouring heart dinta out sai da tayi ta bata haquri.

"Komawa gida zanyi, bazan iya ba. Na yi iya kokari na, yanzu kam na gaji". Cigaba da ba khayri haquri Niima tayi har sai da kukan nata ya tsagaita tukun ta tambaye ta koh akwai wanda zata iya kira. Maamah ce mutum na farko da ta fara zuwan ma khayri rai dan haka koh da ta dau wayarta number din Maamah ta fara dannawa sai dai kan call din ya shiga wayar ta dauke sabida rashin charge.

"Ba komi let me get my phone, you can use it. Naki sai a sa yayi charging. Just let someone at home know where you are okay? Kada hankulan su ya tashi". Kai kawai khayri ta daga ta miqa mata waya. Wucewa Niima tayi ta dauko nata wayan ta miqawa khayri sanna tayi plugging na khayrin a charge. Number din Maamah da ta riga ta sani a kai shi ta danna ta fara Kira. Ringing daya biyu Maamah ta daga wayan da sallama tana wanene.

SANADI✔️Where stories live. Discover now