Babi Na Ashirin Da Bakwai (27).

793 161 22
                                    

Kuyi ta haquri da ni, I'll edit the chapters one of these days In Shaa Allah..enjoy🤗
.

********************

Abuja, Nigeria.

Cak Khayri ta tsaya saboda jin muryar sa da kuma kalaman da suka futo bakin nasa ga kuma hannunta da ya riqe. Da sauri Kabeer ya sakin mata hannu ya wuce ya shiga mota, Billie kam kashe mata ido kawai tayi ta wuce ta shige motar Ya Ahmad suka yi roundabout suka dau hanyar waje. Juyawa Khayri tayi ta buda qofar passenger seat ta shiga ta zauna shuru. Sai da ya sauko da roof din motar, ya daura seatbelt kan yayi starting motar kamar be san da mutum ba zaune kusa da shi. Sai da suka kusa da gate yace mata ta saka seatbelt itama. Haka suka cigaba da tafia shuru, Khayri zuciyar ta sai wani bugu yike ta yi saboda tsoro. Bata saba kebewa da Ya Kabeer haka ba gashi tana gudun ta masa laifin da zai bata masa mood dinsa ya hau ta da masifa. Maida hankalin ta tayi kan streets din Abuja tana kallon buildings da wuraren da bata taba gani ba a rayuwar ta. Tana da tambayoyi kala kala akan garin Abuja sai dai kuma bazata iya tambayar Ya Kabeer ba dan ta san ba ansa ta zai yi ba watakil ma hakan ya basa haushi ya sauke ta a titi.

Su Ahmad sun riga su isa Jabi lake mall, amma sai da suka jira isowar su tukun. Kabeer yayi parking next to Ahmad suka sauko daga mota Khayri ta hade da Billie, shikam Ahmad liqe da Mahra, Ya Kabeer kuma na tafiyar sa shi daya.

"Toh ya zamu yi? Movie before pizza or pizza before movie, amma in haka ne we have to rush dan kamar bamu da enough time".

"I love eating my pizza in luxury" Billie ta fadi. Mahra ma tace she's okay with movie before pizza, Khayri da ita ba wai ta wani gane zancen bane tace itama ta yarda da su Billie.

"MKD?". Ahmad ya kira nickname din Kabeer.

"Yeah whatever". Ya fadi kan ya fara tafia "I'll just go get tickets, ku same ni sama". Da sauri yayi wucewar sa su kuma Ahmad suka wuce da Billie zuwa hanyar washroom dan tace ita fitsari take jin yi. Sai da suka jira ta ga ta taho tukun suka wuce.

"The stair is close, let's use it". Ahmad yayi suggesting su kam suka bisa ana tafe ana hira. Suna isa gaban cinema din suka izza Kabeer har ya siya musu tickets din ya tsaya da wani suna magana. Sai da suka siya popcorn da soda kan suka taho suka tsaya da Ya Kabeer, duk hannayen su a cike.

Kamar ance Billie ta dago kai kawai suka hada ido da wancan dan saurayin da tayi ta kallo a parking lot din airport. The one Mahra said was Sudais Abiso.

"Y'all this is Sudais Abiso. Met him at an exhibition in Armenia last year". Murmushi Sudais ya musu ya miqawa Ahmad suka gaisa yan matan kuma suka gaisa, his eyes lingering on Billie.

"See you around man, enjoy the movie". Suka sha hannu tare da yin shoulder bump kan Kabeer yace musu su tafi, shima Sudais wucewa yayi dan movie inda zai kalla daban da wanda zasu kalla. For no reason Billie taji heart din ta na racing.

'God he's so beautiful'. A voice in her head said.

Kabeer ne ya fara shiga ya wuce ya zauna, Billie na ganin haka ta tura Khayri to sit next to him kan itama ta shiga ta zauna. Next Mahra ce ta zauna, Ya Ahmad ya zauna gefenta.

Zuwa sanda aka gama movie din, Khayri har ta dan fara nisa a barci dan dama ita da wuya tayi kallo bata fara kallo ba. Billie ce ta shafa ta a hankula to wake her up.

"Time to go Khayri". Ta fadi mata. Koh da Khayri ta buda ido sai gani tayi an fara futa daga cinema din. Goge fuskar ta tayi da tafin hannunta kan ta miqe suka wuce. Direct suka yi waje zuwa parking lot, yadda suka zo haka suka sake shiga mota aka kama hanyar Dominos. Koh da suka isa yan matan samun wuri sukayi suka zauna su kuma Ahmad suka wuce to get everyone's order. Hannu cike da abinci iri iri suka dawo duka aka miqe aka wuce dan dama a gida zasu ci saboda duk a gajiye suke, tun isowar su Abuja basu wani sama hutawan kirki ba.

SANADI✔️Where stories live. Discover now