Babi Na Ashirin Da Biyu (22).

829 147 22
                                    

Kano, Nigeria.

Cigarette din hannunsa ne ya qare ya ije stub din akan ashtray inda ke gaban sa kan ya sake ciro wani stick na cigarette yayi lighting. Tunani yike ta wani hanya zai bullo wa matsalar sa, he should be the heir of Argon group of companies, he has to be, he has been preparing himself tun childhood then why all of a sudden wannan tsohon zai kawo cikas, toh sai me in shi dan mace ce? Da me Kabeer ya wuce shi da Dattijo zai ce shi zai taking over as the CEO. Shi kuma Baba dan me zai ba Ahmad highest shares na company din sa? Sai kace shi ba d'a bane, the first son for that matter. Tabbas dole ya nema mafita tun da wuri.

Cikin matukar bacin rai yike gashi tunda yazo Stephanie ta bi ta ishe sa da iyayin ta na banza da wofi. Gaba daya nothing was amusing Khalid at all, ran sa a bace. Fitowa tayi tsaf tsaf cikin shirin ta na fita, dan kiss ta matso manna masa amma sai ya dan ture ta. Hakan ya sa ta gane ba ya cikin mood me kyau, dama ta riga ta gama sanin halin Khalid, yadda yike da temper mara kyau duk da be taba nuna mata the beast in him ba, baya treating dinta yadda yike wulaqanta matar sa ta halal amma hakan be hana ta ganewa cewa shi mutum ne me matukar zuciya ba. Murmushi tayi kan ta masa magana "Baby boo thank you, I got the alert" kai kawai ya daga mata alamar yaji amma be buda baki yayi magana ba. Ita ce ta sake masa magana "I'll be seeing a friend for brunch. See ya later". Tana fadin haka ta juya ta dau car key dinta ta fita. Hakan ya yi wa Khalid dan dama he has been craving for the quiet. Wayar sa ya ciro dan yaji kwanan Anisa and the boys. Wayar be dade yana ringing ba Anisa ta dauka suka gaisa kan ta miqawa yaran waya suka yi ta masa surutu hakan sosai yayi uplifting mood din Khalid. Da Anisa ta karban waya ya tambaye ta.

"Zayn said you guys are going out?".

"Eh, bakaga text dina da safe ba? You must've been busy with work. Zan yi dropping yara a birthday party sannan na wuce to see a friend". Ta masa bayani. Okay kawai ya ce mata sukayi sallama bayan yayi assuring dinta cewa the next day zai dawo gida. Yana kashe wayar ya gyara kwanciyar sa, dama kan doguwar kujera yike. Tunanin yadda zai bullo wa matsalar sa ya cigaba da yi. He had to find a way out, sooner than later.

Ahmad be sake bibiyar gidan kakkanin sa ba sai after three days da rigimar sa da Kabeer wanda sun dade da shiryawa, kuma tun nan babu wanda ya sake dago topic inda ya fara hada fadan in the first place. Bayan sallar isha ya shiga gida ya samu Dattijo ya dawo masjid kenan suna zauna tare da Adda Manga suna dinner. Gaida su yayi a ladabce kan Dattijo yace ya wuce dining ya dauko clean plate ya zuba tuwo ya zauna ya ci. Ba musu ya je ya dauko plate ya zo ya zuba abincin ya zauna kusa da Adda Manga hakan ya sa Dattijo musu tsiya wai yau soyayya ta motso. Wayar Ahmad ya hau ringing yana dubawa yaga Kabeer ne dan dama yace masa yana nan hanya zuwa. Yana dagawa Kabeer ya fara korafin cewa yaji sa shuru.

"Sarkin marasa haquri, toh ina qasa muna cin abinci tare da mata ta". Tsaki Kabeer ya ja ya kashe wayar sa. Cikin kankanin lokaci ya sauko qasa shima. Tun kan ayi masa tayi har ya wuce ya dau plate ya taho ya fara serving kansa.

"Kai Amma Adda wannan tuwon yayi dadi sosai". Kabeer ya fadi yana ta santin girkin.

"Wallahi, rabon mu da tuwon dawa tun muna yara. You remember Iya?" Ahmad ya tambaya Kabeer.

"Ya zan mance Iya me shegen masifa ga dukan yara" duka aka kwashe da dariya aka hau hirar Iya wata tsohuwa da ta taba aiki a gidan Alhaji Muhammad Dikko tun kan a haifa su Kabeer har zuwa sanda aka haife su tana aiki gidan har sai da shekarun ta suka ja sosai ta koma wajen yaran t bayan Dattijo ya mata kyakyawan sallama, can bayan wasu yan shekaru kuma Allah ya mata rusuwa.

"Rabona da cin tuwo me dadi irin wannan tun Iya na nan" Kabeer ya fadi. Yar dariya Adda tayi kan ta basa ansa "Toh kwantar da hankalin ka, dan tuwo me dadi yanzu ka fara ci" Ta fadi tana kai loman tuwo baki. Sai da ta hadiye kan ta cigaba da zancen ta "Ai Allah ya ba Khayri baiwan iya girki".

SANADI✔️Where stories live. Discover now