Babi Na Hamsin Da Biyu (52).

620 109 13
                                    


Abuja, Nigeria.

Abdallah ne ya fara juyawa yayi hanyar study dinsa ba tare da yace komi ba. Yana isa ya shiga yayi banging qofar hakan ya sa Karimatu runtse idanunta, a hankula hawaye suka fara sauka kan kumatun ta. Juyawa tayi itama ta wuce hanyar bedroom dinsu ta shige ta rufe. Niima kam ta kai minti biyar tsaye a wurin tana mamakin what just occurred da kuma abunda taji Abban ta ya fadiwa Ummin ta. Wai ba ita ta haife ta ba, toh in ba Ummi ta haife ta ba wacece ta haife ta? Menene kuma alaqar ta da su Ummi da har ya sa ta riqe ta bayan ba ita ta haife ta ba.

'Koh dai Abba ya taba aure ne?' tayi nazari. 'Qilan ya taba aure suka rabu koh matar ta rasu. Qilan ita ta haife ni' Niima tayi ta tufka da warwara cikin zuciyar ta.

Koh da ta koma dakinta kasa barci tayi sai juyayi take ta yi kan gado ta rasa ya zata yi. She needed to speak to someone or she was going to run mad amma sai ta rasa da wa zatayi opening up to. Ummi da Abba basu cika samun sabani ba amma sai gashi yau sabida ita sunyi arguing.

'kuma da suka yi Ummi bata kwashi kayan ta ta wuce gidan su ba' She thought in her mind. Hasalima bata taba ganin Umminta ta koma gidansu sabida wata sabani da suka samu da Abba ba, zama take yi suyi sulhu tsakanin su. Toh ita ma me sa bata tsaya ta saurara Bakhtiar ba sun sasanta matsalar su a tsakanin su ba? Me sa bata yi koyi da mahaifiyar ta ba, sai ta taho gida har gashi hakan ya kawo sabani tsakanin iyayen ta. Hakan ya sa tayi resolving cewa koma menene komawa zatayi gidan ta sannan kuma ta zauna da mijinta su tattauna, taji dalilinsa na boye mata a very vital information about his life. Wayan ta ta daga ta tura masa text na cewa yazo su tafi gida. Shigan text dinta ke da wuya Bakhtiar ya turo mata reply cewa first thing tomorrow morning zai zo ya dauke ta. That gave her some semblance of relief har ta samu tayi barci.

Da asubah Niima na kan sallaya Ummi ta shigo ta zauna gefen gado tan jiran ta ta gama addu'o'in ta tukun suka gaisa. "You know what happened last night..." Ummi ta fara fadi amma sai Niima tayi cutting dinta midway.

"I just want to know one thing Ummi. Abunda Abba ya fadi gaskia ne? Wai be ke kika haife ni ba?" Ta tambaya idanunta cike da kwalla dan tana tsoron answer in da Ummi zata bata, what if ta bata answer inda ba shi take son ji ba fa?.

"Baki da wata da ta wuce ni Niima. You know how your father can get sometimes when he's angry" karimatu ta fadi tana qara matsowa kusa da Niima "Ya fadi ne kawai dan ya bata mun rai amma I'm your one and only mother Niima. You're my baby not anybody's" Karimatu bata san sanda kuka ya kufce mata ba har hawaye suka fara sauka kan kumatun ta. Niima ce ta matso ta rungume mahaifiyar ta tana rarrashin ta. Sai da hawayen Karimatu suka tsakaita tukun Niima ke fadin mata decision dinta.

"I'm going home today. My husband is coming for me". Dago kai Karimatu tayi zata yi magana amma sai Niima ta riga ta "Coming home was childish. I should've stayed and solved my problems. And ba wai wani babban abu bane ya faru tsakaninmu Ummi, I just acted on instinct, home has always been my safe haven when faced with a problem but I've realized my home is now where Bakhtiar is Ummi. I never should've come". Rungumo diyar ta kawai Karimatu tayi tana qara jin son ta a cikin zuciyar ta.

"Niima na ta girma". Ummi ta fadi duka suka fashe da dariya "Toh ki samu ki koma barci kan gari ya waye". Ta fadi tana miqewa.

Bakhtiar da dama duk ya matsu gari ya waye ya tafi ya dauko matarshi da kyar ya iya bari karfe takwas yayi kan ya kama hanyar gidansu Niima. Gani yayi ta yi kamar in ya bata lokaci Niima zata ce ta fasa bazata dawo ba dan haka yayi ta sauri.

Karimatu da Abdallah wanda har zuwa lokacin haushi suke da juna, suna qasa suna breakfast Bakhtiar ya iso. A ladabce ya gaida su suka ansa, Ummi tayi masa tayin breakfast yace coffee ma kawai in ta bashi yayi. Zama yayi ta hado coffee din ta kawo masa Abba kam ya yi ta jan sa da hirarraki irin nasu na maza shikuma gaba daya hankalin sa ba a nan yike ba, yana ta zuba idanu koh zai ga saukowan Niima amma yaji shuru. Ummi ce tayi rescuing dinsa from the situation da tace masa Niima tana sama he could go up in yana son ganin ta. Handshake suka sake yi da Abdallah da ya miqe zai wuce office sabida yana da meeting da wasu investors dinsa a ranar tukun Bakhtiar ya wuce sama zuwa dakin Niima dan ya riga ya san inda dakin ta yike a gidan ita kuma Ummi ta riqowa Abba briefcase dinsa har zuwa bakin motar sa. Suna isa ta miqa masa jakar ta juya zatayi wucewar ta ba tare da tace masa komi ba. Da sauri Abdallah ya kamo ta tana ce masa ya sake ta.

SANADI✔️Where stories live. Discover now