Babi Na Tamanin Da Hudu (84).

527 109 26
                                    


Borno, Nigeria.

Living room suka shiga haddade wanda duk wani abu na ado, na zamani akwai shi a ciki. It felt so weird seeing the splendor in the room considering the location of the house.

"Me sa kike zama a nan?".

"Who are you?".

"Why do you look like my mother".

Murmushi tayi ta kalli Sudais kan ta miqe tana fadin "I'll make some more tea. Ruwan kadan na saka da naji tsayuwar motar ku, tunani na it was my sister paying me a visit".

Duka da Sudais din da Bakhtiar kallon juna suka yi. Shi Bakhtiar koh kadan hankalin sa ya kasa kwanciya, ji yike ya qosa ya bar gidan, ya bar farmhouse dan har yanzu be gama yarda cewa ba one of games din Inno Marte bane take masa wasa da hankali. Ba a wuci ten minutes ba da shigan ta kitchen din ba ta dawo da kettle din tea da cups a tray. Ije musu tayi a gaban su ta koma ta zauna idanun ta akan su, ta kalli Sudais ta kalli Bakhtiar su kam tea din kowa ya hada to his preference suka zauna shuru not knowing where to start from. Itama zuba tea din tayi a mug ta riqe a hannunta.

Hada idanu suka yi da Sudais tayi masa murmushi tana fadi "Sudais ka kasa daina kallo na. We look alike don't we?". Ba tare da jira ansar da zai bata ba ta cigaba da magana "Ta taba fada maka yadda ta sama sunanta, Inno Marte?". Juya mata kai Sudais yayi cewar be sani ba.

"Mahaifin mu yayi wani aboki wanda suke kasuwanci tare. A duk ranar litinin da ake cin kasuwan garinmu zasu hadu a can da haka suka saba har suka zama abokai.". Wataran Malam Abdu Abiso ya kawo kayan sayarwar shi a ranar kasuwan Benisheik sai be hadu da abokin sa ba. Koh da yayi tambaya koh lafia be ga abokin sa ba, sai aka sanar da shi cewar haihuwa da aka masa ne ya hana zuwan sa kasuwar. Shekarar Malam Kachalla a kalla ashirin da aure, ya kuma auri mata har biyar amma Allah be taba azurta shi da arzikin samun haihuwa ba. Har wata matar da ya aura ya saki da yaji labarin ta yi aure a wani gidan har ta haihu yara kan Allah yawa mijin da ta aura rasuwa, Malam Kachalla ya koma ya dawo da ita gidanshi da fatan Allah zai albarkace shi da haihuwa amma hakan be faru ba har shekaru suka ja masa. Ya fara cire rai da haihuwa har sai da ya auri wata matar shi wanda ita ce daga zuwa Allah ya azurta da ciki har ta haihu yara yan biyu. Hakan ne ya sa malam Abdu Abiso yanke shawarar zai sa a kai shi gidan abokin sa bayan ya gama cin kasuwa dan ya masa barka.

"Yana kallon yaran ya musu addu'a ya kuma sa musu albarka". Ta fadi kan ta tsaya tayi sipping tea dinta tukun ta cigaba "Koh da ya tambaya sunayen su sai ce masa aka yi an saka musu Nanah Fadimatu da kuma Zahriyya". Sake kallon yaran yayi yana murmushi ya yi nuni da babba cikin yaran biyu kan ya cewa abokin sa 'Wannan ita ce me sunan mahaifiyata wanda asalin ta yar garin Marte ce' .

SANADI✔️Where stories live. Discover now