Babi Na Takwas (08).

1.3K 177 7
                                    

Abuja, Nigeria.

Zaune karimatu take hankali yayi nesa cikin tunani. shikam Abdallah yama kasa zama, ba abunda yike yi in ba pacing to and fro qatoton study din su ba all in an attempt to come up with a solution to their predicament. Ringing inda wayar ta ta dau yi ne ya dawo da karimatu cikin hayyacin ta. Duba caller identity din kawai tayi ta dago kai ta kalli Abdallah wanda yayi mata umarni da ta daga wayar. Sai da ta ja ýar tsaki kamun ta daga wayar ta sa ta a speaker. Sai da suka gama gaisuwa aka gama jin lafiyar juna kan Inno Marte ta gabatar da dalilin kiranta.

"Nayi shawara da Sudais". Ta fadi cikin muryar ta wanda is naturally high pitched, mutum in be sani ba sai ya zata cikin fada take magana "He saw your little daughter the other day kuma yace bazai iya haqura ba dan tayi masa sosai. I hope I am clear, zancen aure tsakanin diyar ku da ďana Sudais akwai shi koh kun qi koh kun so". Ta fadi tana ýar dariya. Karimatu rasa abunda fada tayi sai Abdallah ne ya fisge wayar daga hannunta ya fara magana da Inno Marte.

"Haba Hajja, ya zaki mun haka".

"Alhaji Abdallah nima ya zaka mun haka? Ya zaku nema ku mun wasa da hankali, tun ýar nan tana da shekaru goma sha biyar muka yadda Sudais dina shi zai aure ta, sai yanzu da aski ya fara zuwa gaban goshi zaa wani ce an fasa? Bayan duk mutanen da nike hulda dasu sun san cewa Niima ďa na Sudais zata aura". Shuru Abdallah yayi na jim kadan kan ya bata ansa.

"Is this about that money?" Ya tambaya a hankula "karki mance agreement dinmu was zan maido miki kudin ki after 5 years, ina da sauran one year Inno. Dan Allah ki haqura, yarinya ta sama wanda take so kuma baza mu iya mata dole ba, Niima bata saba neman abu ta rasa ba".

"Ta sama wanda take so?" Ta tambaya rai a bace "Da me Bakhtiar Arab yafi Sudais dina? Eh. Wannan tsohon ma in ba ku ba wa zai dau yarinya karama me kyau irin wannan yarinyar ya basa". Koh kadan Abdallah be yi mamaki akan ta yadda Inno Marte ta san da proposal na aure da Bakhtiar ya kawo masa ba, sarai ya san halin Inno, she has a dirt on almost every industrialist wanda take hulda na kasuwanci da. Mace ce wadda maza da yawa, manya masu kudi, masu fadi a ji a qasa suke shakkar ta dan duk wani sirri da kake ganin ba wanda ya sani, Inno ta san da shi bare kuma biggest virals dinta a business, the Arab family.

"Dan Allah Inno a bar zancen nan, kiyi haquri, ki bani zuwa next year gaba daya kudin ki zan dawo miki da su, na kusa gama hada su. Kiyi haquri ki rabu da mu".

"Inyi haquri? Toh shikenan but keep one thing in mind... This isn't about the money anymore, it is about Inno Marte's dignity in the eyes of society". Ta fadi da alamun ranta ya baci sosai. Shuru duka suka yi kan ta sake magana "A isar da gaisuwa na zuwa ga diyata Niima".

"Zata ji" Abdallah ya fadi ciki ciki kamar ana sa shi magana dole, har zai katse kiran sai yaji ta tsayar da shi.

"I wonder how the poor child will feel reading about a certain accident that occurred 17 years ago". Tana fadin haka ta katse wayar ta, ta bar su Abdallah cikin tashin hankali. Sosai hankalin Abdallah ya tashi, babban damuwar sa shine loosing investors din business dinsa yanzu da yike ganin ya fara climbing ladder din success ita kam karimatu nata tashin hankalin shine loosing the only apple of her eyes. Juyowa Abdallah yayi yawa karimatu wani irin kallo cike da bacin rai.

"What?" Ta tambaya "Ni ban aike ka cin bashin Inno Marte ba".

"Amma kin saka ni yin sata koh, dan abunda muka yi da shi da sata basu da maraba". Yana fadin haka ya ja tsaki ya fi ce, har karo suka kusa ci da shi da Niima a qofar shiga study din, koh kallon ta be yi ba rai a bace ya wuce, abun sosai ya matukar daure mata kai dan bata saba ganin Abbanta cikin irin wannan yanayin ba, koh yana bad mood ma be cika sanja mata ba amma wai gashi yau har ya bangaje ta ya wuce. Shiga study din tayi da sallama wanda karimatu bata ma ji sanda tayi ba. Tray inda ke hannunta ta fara Ije wa akan table kan ta zauna kusa da karimatu ta tabo ta kadan, hakan ya sa ta yin firgigit.

SANADI✔️Where stories live. Discover now