Babi Na Ashirin (20).

814 160 32
                                    

Hey people, another unedited chapter. Ignore the errors, feeling too lazy to edit.

.
***************
.

Kano, Nigeria.

"Me ya sa ki kuka?". Ya tambaya a hankula amma sai duqar da kanta kawai qasa tayi bata ce masa komi ba. "Baza ki mun magana ba?". Still shuru Mahra tayi bata ce masa komi ba bata kuma dago sun hada ido ba. Ahmad be sake ce mata komi ba illa gyara zaman sa da yayi akan kujerar da suke sharing su biyu. Sun jima a haka kowa a cikin duniyar tunanin sa.

Ba zatto yaji ta matso kusa da shi ta dora kanta kan shoulder dinsa amma bata ce masa komi ba. "We'll be alright" ya fadi in a bid to assure her. Dagowa kawai tayi suka hada ido da shi kan ta saukar da kanta ta sake dorawa kan shoulder dinsa. Daga nan ba wanda ya sake cewa komi, a haka har suka kashe kusan rabin hour zaune shuru a garden din. "Muje in raka ki cikin gida". Ya fadi a hankula kan ya miqe. Miqewa itama tayi ta biyo sa a baya ya rakata har bakin qofar dakinta. Har ta buda zata shiga ta juyo ta kalle sa. Murmushin da be taba ganin Mahra tayi ba yaga ta sakan masa before shyly wishing him a good night ta shige ba tare da ta tsaya jin me zai ce ba. Daga nan Ahmad be tsaya koh ina ba sai dakin Kabeer. Koh da ya murda yaji alamar qofar a rufe wayar sa ya ciro ya danna kiran Kabeer din.

"Let me in" kawai ya fadi ya katse waya. Ba a dade ba Ahmad yaji alaman an buda qofar ya murda ya shiga ya samu har Kabeer din ya koma ya zauna a qasa bayansa jingine da frame din gadonsa, ya jawo cinyoyinsa sama zuwa kirjinsa ya dora kansa a saman su. Halin da Ahmad ya sama dan uwan nasa ya mugun sa shi karaya, ya san cewa tabbas something is wrong somewhere. "What's up" ya fadi a hankula bayan ya zauna kan gado. "what was Dattijo saying, kai da Khayri. When did that happen?".

"I don't know man, I don't fucking know" Kabeer ya fadi murya kamar zai yi kuka. Gaba daya a rude yike dan shi baya iya tuna sanda yaje ya gayawa Dattijo cewar shi Khayri yike so, be kuma san me ya sa family dinsa suke tunanin soyayya yike yi da shi da Khayri ba. Hasalima shi ya tsana yarinyar, kwata kwata jinin sa be hadu da nata ba.

"Everyone's saying soyayya kuka fara a boye" Ahmad ya fadi flicking through his phone to keep himself busy.

"You should know me better than that. Kai ka san bana son yarinyar nan. Zulaikha nike so, I will referring to her a duk maganar da muka yi da Dattijo".

"Amma wannan abu kam da mamaki" Ahmad ya fadi yana dora hannunsa daya kan kafadan Kabeer "Get some rest, karka sa tunani da yawa. Zan shigo da safe and we'll find a way out. I'm sure duk misunderstanding ne. Dattijo will understand". Ahmad ya dan jima yana kwantarwa da Kabeer hankali kan ya wuce kasancewar dare yayi. Shikuma Kabeer din sosai yaji dadin maganganun Ahmad, yaji hankalin sa ya kwanta. It was definitely just a misunderstanding wanda suna zuwa suna ma Dattijo bayani komi zai daidaita daga nan sai ya bullo da hanyar da zai shawo kan Zulaikha dan dai Dattijo da gaske yike akan dole sai yayi aure kan ya koma London.

Billie ta dade tana kuka Anisa na shafa mata baya a hankula. Ita kanta bata san hakan tsananin son Ya Kabeer yayi mata muguwar kamu ba sai a lokacin da Dattijo yayi announcing auran Ya Kabeer da Khayri nan da wata daya. Yanzu shikenan ba maganar soyayya koh aure tsakaninta da Ya Kabeer har abada, baya son ta kamar yadda ita take son sa.

"Shhh toh ya isa haka mana". Anisa ta fadi. "Please ya isa kar kiyi zazzabi. Rabon mutum baya taba wucesa Billie, indai Kabeer mijinki ne koh nan da shekara hamsin ne sai ya aure ki, in kuma ba rabon ki bane sai kiga Allah ya kawo miki wanda ya fi alkhairi a gare ki dan haka ki kwantar da hankalin ki. It's not the end of the world". Share hawayen ta tayi ta kwanta shuru jikinsa Anisa tana ta sauke ijiyan zuciya daga baya ta miqe tace ma Anisa ta gode da support dinta, taji kuma zata yi aiki da shawarwarin da ta bata. Sosai Anisa taji dadin hakan.

SANADI✔️Where stories live. Discover now