Babi Na Sittin Da Uku (63).

566 127 12
                                    


London, England.

Iya kokarin sa yayi dan yaga ya samu ganawa da ita, yayi apologizing to her one on one amma ina hakan ya gagara dan haka daren ranar da Kabeer ya dawo apology note ya rubuta ya ije ma khayri a inda ya san zata gani. Next morning, khayri bata futo ba sai da ta tabbatar da cewa ya futa daga gidan. Kitchen ta wuce dan shan ruwa sai ta gamu da note dinsa kan counter.

I was such a jerk. Forgive me, will you?- KB

Haka nan khayri ta sama kanta da jin dadin. Ba wai wasu kalaman soyayya Kabeer ya rubuta mata ba, hasalima note dinsa was a straight forward one amma the fact that he actually apologized made her happy, at least they were getting somewhere. Ya Kabeer in da ta sani da bazai taba bata haquri ba, be taba ba. She loved this improved version of Ya Kabeer. Clutching note din tayi to her chest tana yar murmushi, a zuciyar ta kuma addu'a take Allah ya sa su dore a haka.

Throughout ranar khayri cikin farin ciki take. Allah Allah tayi ta gama karatun ta for the day ta wuce ta kira Niima. Koh da Mr Richardson ya tafi, Khayri ta dade on the phone that day with Niima who kept giving her ideas on how to work on her rocky marriage.

"In ya qi bani hadin kai fa?". Khayri ta tambaya reluctantly.

"It's okay my love, Rome wasn't built in a day" Niima ta fadi "A hankula zai bada kai bori ya hau, kedai just be consistent and patient. In Shaa Allah zaki ga amfanin hakan". Hira suka sha Khayri ta tambaya Niima karfin jikin ta nan ne Niima ta tambaye ta if she'd love to go with her to shop for a few baby things. Dariya khayri tayi tace mata tun yanzu zata fara shopping din kayan baby Niima tace mata ta kasa haqura ne shisa. "Kuma nan da sati me zuwa zamu koma garinmu". Ji khayri tayi ba dadi because in a short while har sun kulla wani kawance da juna.

"Ni har na mance ba nan kuke zama ba". Dariya Niima tayi "Kamar kar ki tafi". Khayri ta fadi kamar zata yi kuka sabida Niima was the first true friend she's made tun da ta dawo England, infact tun komawar ta Kano bayan su Billie, khayri bata hadu da wata wadda zata iya considering dinta as a friend ba sai Niima.

"Zamu dinga waya ai". Niima ta fadi in a bid to comfort her amma itama har cikin zuciyar ta take ji kamar ta zauna koh kuma khayrin ta dawo Nigeria dan ita bata san mesa ba always ta hadu da khayri ji take bata so su rabu, duk sanda zasu rabu ji take kamar she was leaving a very important part of her behind.

"So will you go with me? Kullum na futa sai naga something very cute that I really love". Dariya khayri tace mata she'd love to go with her.

The following day da Mrs Lee tazo khayri ta fadin mata cewa daga lokacin ta daina musu girki tana ijewa sai dai in khayrin ce ta buqaci hakan sannan kuma gyaran sama inda Kabeer ya fi zama daga lokacin shima ta daina.

"I'll do it myself". Khayri ta fadi a turancin ta da zuwa lokaci yayi improving sosai.

Bayan sallah asubah ya wuce jog kamar yadda saba, kullum sai yayi jogging kan ya dawo gida by 7:00 ya fara shirin futa duk da ba wai white color job yike ba, work space dinsa yike suwa yayi aiki 9-4 on weekdays dan yafi aiki sosai a nan akan a gida, sannan kuma once in a while yana meeting da businesses inda yike da su da kuma partnering in with others. Safen ranar, Kabeer na shigowa gida daga jog dinsa straight kitchen ya wuce kamar yadda ya saba to get coffee kan ya wuce sama yin shirin. Dama mostly ba wai yana wani breakfast din kirki bane kan ya futa, sai dai ya sha coffee on his way to his studio kuma sai ya tsaya to grab breakfast or snacks. Abunda be yi tsammani ba shine ganin khayri a kitchen, still her pyjamas making breakfast. Yana shiga khayri tayi sensing presence din sa a bayan ta dan haka ta juya. Suna hada ido dukansa suka dauke idanu kan juna. Wucewa yayi zuwa inda coffee machine yike ita kuma ta gaida shi ta cigaba da aikin ta. Ansa ta yayi yana searching for mug, da be ga favorite mug dinsa ba wanda yike son shan coffee ya juya zai tambaye ta sai dai kan ma ya buda baki tayi beating dinsa to it. "Yana can" ya nuna masa gefe inda ta riga tayi arranging masa tray with sugar, his fave mug and a tea spoon. Cabinet inda suke ije teas and ground coffee ya bude zai dau container din coffee tace masa "Na riga na dafa. If you'll sit, I'll serve breakfast". Kallon ta Kabeer yayi, ya kalla pan inda ke kan wuta sannan ya juya ya wuce ya zauna har lokacin his brain was still trying to process the whole thing. Coffee dinsa ta hada masa just the way he loved his coffee; strong, one cube of sugar, no creamer.

SANADI✔️On viuen les histories. Descobreix ara