ZAN SOKA A HAKA

By queenbk2020

392K 23.9K 2.2K

#5 tausayi June 2020. #3 tausayi 20 June 2020. #1 munafurci #8 hausa novel. #2 tear drop june 2021. More

page 1
Page 2
page 3
page 4
page 5
Page 6
page 7
Page 8
Page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 1⃣4⃣
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
pahe 22
page 23
page 24
page 25
page 26
page 27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
Page 34
page 35
page 36
AUTHOR'S NOTE
page 37
page 38
page 39
page 40
page 41
page 42
page 43
page 44
page 45
page 46
page 47
page 48
page 49
page 50
page 51
page 52
page 53
page 54
page 55
page 56
page 58
page 59
page 60
page 61
page 62
page 63
page 64
page 65
page 66
page 67
page 68
page 69
page 70
page 71
Page 72
page 73
page 74
Page 75
Page 76
page 78
page 79
page 80
page 81
page 82
page 83
page 84
page 85
page 86
page 87
page 88
page 89
page 90
The end and thanks.

page 57

4.7K 301 32
By queenbk2020

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨





💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼







🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )















Page5⃣7⃣







Ya faɗa yana karkaɗa idanu yana kallon waje, juyowa yayi sai kuma yayi sakakai ganin yadda yanayinsu yake, ƙarasowa yayi yace "Ammie! Beauty! me yasa ne kuke ta kuka wai?".


Ammie ta share sabbin ƙwallan da suka zubo mata tace "Abdallah kukan farin cikine, Beautynka ƴar uwarka ce ta ƙut da ƙut".

Murmushi yayi kamar ya fahimta sai kuma yace "ai Ammie na sani ai beauty ƴar uwata ce ba shiyasa muke zaune gida ɗaya ba? kuma har ta zama matata ba?".

"Ay yayansu shiyasa bacin haka kuma ita ɗiyar hab........." da sauri ya tari lumfashin Ammie da faɗin,

"Yehhh wallahi an fara ruwa kuzo muje muyi wasa a ruwa dan Allah" ya faɗa yana jansu da hannayensu, ammie ce ta zare hannunta ganin shi da gaske janta zai yi su fita cikin ruwa tasan Abdallah da san ruwa, cewa tai "ni rufa mun asiri yaro na shiga ruwannan ai sai wata ba ni ba".


Nan Ammie tasa sukai sallar magruba sannan ta zubo masu tuwo a plate suka zauna suka ci tare, suna ta hira Asmah da Ammie ne ke firar dan shi Abdallah hankalin shi na window yana kallan yadda ruwan ke sauka yana ta murmushi shi kaɗai abunshi yana ƴan suratan shi, ganin ruwan ya ƙara zugewa Abdallah ya buga tsalle ya tashi yana cewa "yeeeeee Allah kawo ruwa muje malali mallam na gyangyaɗi yana saka lomar tuwo" yana yi yana ƴar rawar sa, tun daga Asmah har Ammie ba wanda bai dara ba, ganin suna dariya shima ya ɗau sowa.

Hannun Asmah ya kamo yana faɗin "Beauty i sauri kizo mu tafi wallahi kiyi sauri kar ruwa yafi mu gudu" ya faɗa yana janta.

Ammie ta kalle ta tace "ai ki tashi kawai ki bishi dan ya matsa kuje kawai sashenku sai gobe amman bari na ɗauko maku lema sabidda kar ruwa ya jiƙa ku".

Ammie ta ɗauko masu lema ta basu duk taji bata son su rabu kamar yadda itama Asmah taji nan dai da ƙyar sukayi ma juna sai da safe sanna ta bi Abdallah suka wace suna fita waje ta buɗa lemar tana rufesu su duka amman Abdallah sai zillewa yake yana shiga cikin ruwan yana ihun daɗi yana faɗin "Beauty shigo cikin ruwan kiji wani daɗi wallahi".

Haka ya yaye mata lemar tuni iska tai sama da ita, ganin ya tsaya sai wasa yake a wajen tace muje can part ɗin mu sai na taya ka wasan dan yau ina cikin farin ciki, hannunshi taja su ka tafi suna shiga garden ta rufe ƙofar garden ɗin da sakata, gani tayi ya isa tskaiyar filin yana ta jujjuyawa yana jin ruwan a kowane sassa na jikinshi daka ganshi kasan yana matuƙar farin ciki, ƴar varender shiga part ɗinsu ta isa ta aje jakarta da gyalenta sannan ta dawo inda yake ta shiga yin abunda yake, ba ƙaramin daɗi yaji ba ganin Asmah na taya shi tsayawa yayi da abunda yake yana kallonta yana jin wani shauƙin ƙaunarta na shigar shi ba ƙaramin birgeshi tayi ba, ita ma tsayawa tai tana kallon shi tana dariya da hannu take mashi alamar me ya faru mu cigaba mana, dariya ya saki shima yace "kalla beauty haka akeyi" ya faɗa yana ɗaga kanshi sama tare da buɗa bakinshi yana juyawa a hankali can kuma sai ya sakko da kanshi yana nuna mata ruwan da ya taru a bakinshi sai ya haɗe yana faɗin "kin gani na sha ruwan Allah".


Nan suka fara yadda Abdallah ya nuna mata suna yi suna haɗiye ruwan suna faɗin sun sha ruwan Allah, can Asmah taji Abdallah ya ɗagata ta ƙugunta yana jujjuyata a hankali suna dariya ɗaga kanta tayi tana jijjigawa cikin farin ciki, kallabinta ne ya cire yayi ƙasa take gashinta ya bayyana duk ya jiƙe nan ta shiga karkaɗa shi tana yafa ma Abdallah a fuska shi kuma yana dariya, sauko da ita yayi tare da tallafo fuskarta nan suka shiga kallon juna cikin ido Abdallah ya haɗe goshinsu waje guda yana sa hannu ya na taɓa gashin idonta da sukai zara zara duk sai yaga ta ƙara mai kyau, kamar yadda ita ma take kallonshi tana yaba halittar shi, Abdallah ya haɗe bakinsu waje ɗaya wani hot kiss suke ba junansu, irin kiss ɗin nan na I love you alot.

Can Asmah ta tuno dare ne fa kuma a waje suke da sauri ta janye bakinta tana faɗin "baby mu gudu ciki ga ant nan zai cije mu" ta faɗa tare da janshi sukai ciki Abdallah na faɗin "beauty mu gudu kar ant ɗin nan ya kamamu", haka suka shiga ciki kayan jikinsu sai ɗiga yake na ruwa, direct toilet suka wuce Asmah ta haɗa masu ruwa mai zafi cikin ƙaton kominsu, sannan ta sa bath flowers a ciki suka cire ma juna kaya suka faɗa cikin ruwan suna fancal fancal ruwan na ɗumama masu jiki, nan ma wasan ruwa suka shiga yi wannan ya watsa ma wannan wannan ya watsa ma wannan nan suka fara wasan ƴar bin juna a cikin ruwan, suna dariya suna jin daɗi sai da suka gaji Asmah ta kai bakin komin wankan tana ɗora hannayenta jikin komin tana kallon candles ɗin da ta kukkuna masu domin bata kuna masu wutar lantarki ba sai ta samu candles da yawa ta kukkuna masu, Abdallah ne ya ƙaraso gareta ya rungumota ta baya yana kwantar da kanshi saman kafaɗarta yana wasa da gashinta.

Can taji yace "kai yau yayi daɗi dama kullum haka zamuna yi ko?".

"Ay baby yau yayi daɗi kuma yau tana ɗaya daga cijin ranakun da bazan taɓa mantasu ba a shafin rayuwata ba".

"Nima ai".

"Babyna ina habibtyn ka?".

Tana ambata sunan taga yayi murmushi cikin fara'a yace " wayyoo habibtyta tana india" ya faɗa yana mata alamun jirgi da hannu.

Cewa tai "kasan meye babyna?" kaɗa mata kai yayi yana mata susa da hancinsa a wuyanta sai da tayi dariya tace "Habibtynka itace Ummata".

"Haaaaaa dagaske to me yasa baki yadda ku gaisa hamma kike kuka in muna waya?".

"Saboda ban sani ba sai yau Ammie ta faɗa mun".

"Yeeeeeeh Beauty shi kenan mun gano Ummanki da muke ta nema ashe ma Habibty tace, ke nan kina son Habibty ta sosai ko kuma za kuna gaisawa yanzu ko?".

"Ay Baby ina sonta sosai".

Juyo da kanta tayi tana kallonshi ji tai yace "nima ina sonki sosai beautyna" sannan ya haɗe bakinsu waje ɗaya.

Sun shagala sosai cikin ruwan nan daga bisani Asmah ta buɗe makwararar ruwan suka tsiyaye sannan ta buɗa masu shower ruwan zafi da sanyi ta haɗa masu nan suka shiga yi ma juna wanka suna annashuwarsu abunsu, sai da suka gama suka ɗauro alwallah suka fito daga comin Asmah ta ɗauko towel ta na niyar ɗaurawa Abdallah yace sam shi nata yake so kuma sai dai su ɗaura tare, haka suka yafo towel ɗin suka fito suna dariya saman gado suka baje suna shafa ma juna mai, sai da suka gama sannan Asmah ta ɗauko ma Abdallah jallabiya ta zura mai ita ma ta zura wata doguwar riga nan suka tada sallar isha'i, sai da sukai shafa'i da wuturi sannan suka yi karatun ƙur'ani suka shafa addu'oinsu sannan suka tashi wasu kayan bacci ta ɗauko mashi ta bashi ya saka ita ma ta janyo wannan kayan baccin da Mimi ta bata ta zura tare da feshesu da turare, kayan sun mata kyau sosai shiko Abdallah sai binta da kallo kawai yake, ƙanƙameta yayi yana faɗin "beauty yunwa nake ji".

"Ayyah babyna muje na dama ma fura kaji".

Da sauri ya ɗaga kai suka jera sukai kitchen ta gama dama mai fura a blender da tasha youghurt ayaba kwakwa sai suga, furar sai ƙamshi take niko nace wa zai nuna ma ma'u damun fura dan ma tayi na ƙiuya da da ludaye ta dama da yakenan, ƙasan falo suka baje tana tura mashi furar tana cewa bisimilillah, maƙale kafaɗa yayi yana cewa "sai dai ki bani a baki".

Murmushi tayi dama tasan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya, ludayi ta ɗauka ta motso sannan ta debo tana kaimai saitin bakinshi ƙara maƙale kafaɗa taga yayi cewa tai "to ya kuma akai baby?".

"Da bakinki zakina ban in kika sa a bakinki sai ki samun a baki" ya faɗa yana mata demostrating da hannu.

Murmushi tayi tace "kai babyna duk wani salon so kasan shi".

"Ai dai kin fini sani sabida ke ke koya mun son ai".

Dariya tayi ta shiga bashi kamar yadda yace a haka suka sha furar har suka ƙoshi nan suka ƙara bajewa suna kallon *Sarƙatil hubb* a tv, can Abdallah yace "yauwa beauty na tuno wallahi" ya faɗa tare da ɗago kanshi daga cinyarta da ya kwantar da kanshi tana masa wasa da gashi, kallon shi tayi tana juya ido tace "babyna mai ka tuno?".

Taba kai yayi yace "ɗazu da zaki fita kince zaki sayo mun baby, to tana ina?".

"To Allah ya kamani ya tuno kenan" ta faɗa a ranta a fili kuma tace "babyna dama mace kake so?".

"Ay ai kin suyo mun ko?".

"Ahhhhh ahhhhh" ta faɗa tana ɗora yatsa a kumatunta tana kaɗa harshe.

Bubbuga ƙafa ya fara yana faɗin "ni mai yasa baki sayo mun baby ba?".

"Ishurunka babyna, ai ba sayo baby ake ba samowa ake".

"To taya ake samowar".

Hawa tai kan cinyar shi tana jawoshi gareta, ta riƙe fuskarshi kusa da bakinshi tace "kana so mu samo baby?" sai da ya manna bakinshi a nata sannan yace "dayawa nake son babies ɗin".

"To sai munyi wasa da yawa zamu samu babies" ta faɗa tana haɗe bakinsu waje ɗaya a ranar Asmah ta nuna mashi ita ma gwanace ya koya mata tafi shi, dan sai da Abdallah ya fita hayyacinshi sosai ya rasa a wace duniyar yake a haka suka farantawa juna rai, Abdallah ko har yai bacci bai dawo hayyacinshi ba, ita ko Asmah data runtse idonta sai ta buɗe
kwata kwata bata son bacci yaɗauketa ta tashi taji mafarki ne Ammie ba ƴar uwar Ummanta bace, habibtyn Abdallah ba Ummanta bace, muryar da taji ta Ummanta mafarki ne, tashi tayi ta faɗa toilet tayi tsarki kana ta dawo ta tofe Abdallah da kanta da addu'oin da ta saba masu da daddare sannan ta kwanta bayan tayi ma Ummanta add'uar samun nasara yanzu ji take kamar ta jawo sati biyu su dawo gobe.










fiamanillah

👸🏼QUEEN BK👸

Continue Reading

You'll Also Like

181K 17K 79
"Sickler gare ta, kuma ku kuka ja mata." Ta yi shiru daga nan, dafe da goshinta, tana jin yadda kanta ke sara mata. "A kullum dad'a wayar wa mutane k...
Alina By ihidethisapp

General Fiction

1.5M 40K 80
The Lombardi family is the most notorious group in the crime world. They rule both the American and Italian mafias and have many others bowing at the...
3.9K 187 11
Labarin wata ba fulatanar budurwa mai suna FANTA! Da matashin saurayin ta MAHBUB dan birni😉 Written by MISS XOXO and NAFEE ANKA😍 (2016...)
3.6K 285 44
labari me cike da darasi, kudi ba Shi ba ne komai Wanda Kuma kake ganin Bai isa ba sai kaga ya isa, labarin yarinyar da ta taso cikin kwazzabar mutan...