Chapter 1 Page 87

173 12 1
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 8⃣7⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*


Tana idar da sallah ta koma gaban mudubi tana kara gyara kwalliyar ta. Sanya take da milk kalar less wanda akai wa ado da coffe kalar zare yai mata kyau dinkin riga da siket ne sun amshe ta sosai  tayi light make up daga hoda sai jan baki sai kwalli da ta sakawa idon ta. Ta gyara girar ta dake a cike ta fara dauri. Fauziyya ce ta shigo tana fadin
"Kai wannan kyan fa kada kisa bawan Allah ya zauce fa."

"Kai Yaya Fauziyya."
Ta amshi dan kwalin tai mata dauri mai kyai. Turarukan ta ta bata ta shafa tace
"Ina Sakina ne?"

"Wanka take."
"Ok!"

Karfe biyu dai dai ya iso bakin gate yai horn mai gadi ya leka ta kofa sai da ya tambaye shi gun wa yazo sannan ya bude masa gate din. Ya shiga yai parking ya fito. Wayar sa ya dauka ya fara neman layin ta.

Wayar ta ce ta hau kara ta dauko ta kai kunnen ta.
"Baby gani na karaso ina cikin gidan."
"Ok gani nan"

Ta kalli fauziyya tace
"Yazo"
"To agaishe shi. Ki kula da kanki."

"Insha Allahu Yaya."
Zata fita kenan Sakina fito daga wanka tace
"Kai amman kinji kyau kanwata."

"Nagode. Yazo ne zan je."
"To."

Ta fita. Sakina ta shafa mai itama.ta shirya cikin irin kayan da Hafsa ta saka tayi kyau sosai dan sosai suke kama da Hafsa dan yan gidan su Sakina dukka kyawawa ne masu kyau da diri.


*
Tin da ta fito yake kallon ta bai taba ganin ta da mayafi ba sai yau dan haka tafi da hankaln sa. Dan har ta karasa wajen sa bai sani ba. Sai da ta tafa hannayen ta sannan ya dawo hankalin sa ya sauke ajiyar zuciya yana fadin
"Masha Allah Baby daman haka kike?"

Tai murmushi tace
"Bana son tsokana."
Shima murmushi yayi yace
"A yanzu nasan ana so na a da ko hoda ba a shafawa in nazo amman yau an min kwallyya. Gaskiya Hafsat ke me kyau ce ki godewa Allah ga sturucture."

"Ka Deedat ni bana so."
"Ni ina so dan na fadi gaskiya."

"Uhmm ni muje!"
Tayi gaba yabi bayan ta. Suna shiga hadaden falon ta nuna masa kujera ya zauna yana fadin
"Nagode!"

Ta dauko lemo da ruwa ta zuba masa, amsa yayi yana fadin
"Godiya nake amarya ta."

Tai murmushi tace
"Deedat taho kaci abinci please!"

Ta zuzuba masa komai ta jere masa akan table din dake gaban sa. Kallon ta yayi ya kalli plates din dake gaban sa da abinci kala kala.

Kallon sa tayi tace
"Bismillah"

"Baby ina zan kai dukka wannan!"
Fuska ta bata tace
"Cikin ka."

"A'ah saki fuskar zanci ko cikina zai fashe amman dai kinsan sun min yawa ko? Ina zan kai dukka."
"To ni dai kaci."

"Taho muci tare."
"A'ah ni na koshi."

"Oh ai kuwa nima na koshi."
"A'ah!"

Ta fada tana make kafadar ta. Yai murmushi yace
"Yau ba abinda naci tin safe tea kadai nasha dan ina saurin nazo na ganki."

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now