Chapter 1 Page 56

219 20 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 5⃣6⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

"Ummu ki fito me kike yi ne? Ko so kike mu rasa flight ne?"
Anty Zainab ta fada.

Ummu dake daki tace
"Anty gani nan!"
Ta fito sanye da dogowar riga yar saudi maroon kala. Wacce ta amshe ta ta kara fito da hasken fatar ta. Yadda Ummu tayi kyau fatar ta ta kara haske da taushe saboda gyara da ta samu.

Nikaf ta fara kokarin sakawa Anty Zainab tace
"Wato shi kika tsaya nema zaki makarar da mu ko?"

"Sorry Anty!"
"To ba zaki saka ba. Ai kinsan facemask zasu ce ki saka dan ki sa su tsaida mu suna magana ko? Maza ki cire malama!"

Fuska ta bata tace
"Kai Anty dan ai ta kallo na?"
"Menene dan an kalle ki to?"

"Haram dai gashi kin sa na kara kyau!"
Ta kara magana tana turo baki!
"Au haka kika ce ko?"
Tayi kwafa tayi gaba.

Ummu ta bita a baya tana turo baki. A compound suka samu su Yaya Suleiman a mota. Kan Ummu ta karaso Anty Zainab har ta shige mota.

Yaya Suleiman dake zaune kusa da driver ya juyo yana fadin
"Ya kuka dade?"

"Ga yarinyar da ta zaunar damu nan!"
Ummu ya kalla yaga yadda take turo baki ya saki murmushi yace
"Yau ina Nikaf din nata."

Dai dai zuwan Ummu ta bude mota ta shiga ta zauna.
"Wa ya taba amarya ne?"

Yaa Suleiman ya fada idon ta ne ya kawo kwalla tace
"Ba Yaya Zainab bace."

"Yaya Zainab baki kyauta ba me kikai mata."
"Wai sai ta saka nikaf sai kace wani zai kalle ta ita kadai ce mai kyau da za a kalla akan neman nikaf fa duk ta zaunar damu kuma ta fison muje ai ta magana ta cire nikaf tinda yanzu abun facemask ne ba sai ta saka ba dan Allah!"

Kai ya gyada yace
"Yi hakuri kanwata rabu da Antyn nan taki ita da zata lallabaki zaki barta shine take miki haka ko? Rabu da ita ai zata zo tana missing ne."

Driver ya tada mota suka fice suka nufi airport suna zuwa kowa ya fito. Facemask kowa ya saka sannan Ummu ta ja mayafin ta ta rufe fuskar ta ruf. A haka ta fara tafiya a hankali Yaya Suleiman ne ya kalle ta ya saki murmushi ya karasa ya kama hannun ta yai mata jagora. A haka suka shiga akai screening sannan suka wuce dan shiga. Sai da suka shiga suka zauna sannan ta sauke rufe fuskar ta bar facemask din kawai.

Suna sauka kano ma a haka ta fito tana rurufe fuska driver da yazo ya dauke su ne ya wuce dasu gidan su Yaa Suleiman dake nan kano dan in sun zo in zasu dade a gidan suke sauka.

Suna shiga ta wuce dakin ta tayi wanka sannan ta kwanta dan bacci take ji. Tana kwanciyya wayar ta ta hau kara dauka tayi taga mai kira ta saki murmushi tana fadin
"Ba zan baccin ba dai kenan."

Dagawa tayi tai sallama. Ido ta lumshe tana fadin
"Yanzu muka sauka!"

"Sannu ai nasan daman by now kun sauka shiyasa na kira naji ya kuka sauka ina fatan baki gaji ba dai ko?"
"Eh!"

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now