Chapter 1 page 17

251 13 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 1⃣7⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*
*

Washe gari ma da azumi ta tashinta kasa daina kuka da ta tina abinda ya faru da ita a baya sai hawaye. A haka ta yini daki ko tsakar gida bata fita. Da tasha ruwa ma ruwa kadai tashan ta kwata dan bata jin son cin komai sai can dare taji yunwa ta dan hada tea ta sha.

Tunanin yadda kannen su zasu tashi take sam iyayen ta su basu da kula shin sun manta su amana ce a gunsu ranar gobe kiyama sai Allah ya tambaye su yadda suka tarbiyyar dasu. Yau kwanan ta nawa bata gidan mahaifiyar ta bata damu ba bare mahaifiyar ta da tin da ta dawo kwana biyu ma bata saka uwar a idon ta ba ko ina ta tafi.

Washe gari ma azumin ta dauka tana mai cigaba da kai kukan ta ga Allah. Sam ta fitar da rai da rayuwar komai tsoron yake bata kwana take ta yini sallah da karatun al kur'ani ko falo bata fita iya karta dakin ta.

Da Yamma tana zaun taji kannen ta na ta kukan yunwa iyayen ma basa nan wannan yasa ta kira kanin ta ta bashi kudi masu yawa tai masa list din kayan abinci dan dubu dari ta bashi taje ya siyo tace su daura abinci suci.

A yanzu ta dauki damar yin karatu ko business dan ta tallafi kannen ta kar suma su fada irin rayuwar da suka shiga. Dan haka yanzu ta ina zata fara. Dole ta tsarkake kan ta wannan yasa sim din ta ma ta karya wayar ma ta cilla cikin jakar ta. Mukullin motar ta ta dauko tana juya shi yanzu sam mota ma bata bata sha'awa dan haka siyar wa zati ta samu shago ta siya ta zuba kaya ta maidashi provision store tana taimakawa kan ta a harkar karatun ta da kamnen ta. Bata kawo aure dan tasan ba me auren ta a yanzu.

Satin ta biyu bata ko fita tsakar gida bare falo tana dakin ta ko abinci bata iya ci daga tea sai lemo ko cake shima sai taji uwar bari wato yunwa. Sam Farisa bata shiga harkar ta sai Hafsa ce ta damu da halin da yar uwar tata take.

Kamal yazo gun Farisa amman tace ya kara hakuri yanzu Antyn tata tana wani hali. Duk ya damu donin ya kira ya kira wayar a kashe yazo ya aiko ta ce batazo ba dan bama ta tambayi waye ba tace aje ace bazata zo ba. Wannan yasa ya nufi Farisa dan ta taimaka masa domin Allah ya sani yana son Fauziyya bai taba haduwa da yarinya kamar Fauziyya ba kyakyawa ga kyan diri da ni'ima.

Tana kwance tana jan carbi kanin ta ya shigo dakin durkusawa yayi yace
"Ina yini? Anty Fauziyya!"

"Lafiya lou Amir me kuke so?"
"Babu komai daman wani ne a waje yace nazo na kira ki."

"Kaje kace ba zanzo ba."
Mikewa yyi yace
"Toh!"

Tsaki ta saki tana me fadin
"Sai dai fa ka mutu!"

Muhammad da yau sau biyu kenan yana zuwa yasa ai masa sallama da ita ake fada masa tace ba zata zo ba sai ya juya ya tafi ba dan yana so ba sai dan ba yadda zaiyi. Kwanakin da yayi baya ganin ta ya daga masa hankali dan daman ganin ta kadai na rage masa damuwa ko da kuwa ba zatai masa magana ba. Lallai zuciyar sa ta kawo shi inda aka fi karfin sa har take shan wahala amman duk da haka bai jin haushin ta sai karin son ta da yake ji.

Sakina kuwa ta kware a harkar da kawar ta ta saka ta dan cikin lokaci kadan ta kware a harkar dan yanzu manyan mata ke neman ta dan ya'yan gidan su kyawawa ne suna da sura mai kyau abinda ke rudar masu mu'amala dasu kenan. Yanzu ma Abuja ta tafi dan kawar wata hajiyar ta ce ta neme ta akan tazo tai mata kwana biyu. Bayan taje sun sheka ayar su ta dauke ta ta kai ta shopping daga nan suka biya gidan Hajiya Mariya wacce itama ta kasance tana bin maza a harkar saboda yadda mijin ta ke nuna halin ko in kula dan yadda ya fifita aikin sa akan hakkin aure dan in ya tafi sai yayi wata hudu bai dawo ba gashi ita kadai a gida dan ta yana waje acan yake aiki.

Tin tana bin maza ta daina dan tace kar asirin ta ya tonu dan hajiya Bilkisu ita ta fara kawo mata bin mace har sukai lesbian ta kuma ji dadi taga in mace aka ganta dashi ba mai zargin ta ba, ba kamar in yaga na miji wannan yasa Hajiya Bilkisu ke aiko mata da duk wanda yazo wajen ta yanzu ba gidan Hajiya Mariyar suka nufa da Sakina.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now