Chapter 1 page 18

269 16 1
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 1⃣8⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*Not Edited*

Farisa da Hafsa ayar su suke shekewa bame kwaba bare harara. Wata rana Hasfat ta dawo daga gidan saurayin ta da ta dawo tin tana titi taga wata mota ta faka a bakin titi, da ido tabi motar sai kuma ta dauke kai. Nan ta tsaida Napep ta hau ta tafi amman abin mamaki tana sauka ta kara ganin motar ita sai abin ya bata tsoro dan in har da irin mazan da take kulawa ne a take zai nuna abinda yake so in tayi niyya ta bishi amman wannan bata ga ko wake cikin motar ba ma bare ta kai da sanin waye. Gida ta shige.

Yana daga cikin motar ya saki murmushi yana cije baki ya tada motar yayi gida. Tin daga lokacin kullum sai yazo kofar gidan yaga fitar ta. Sam Hafsa bata shigar banza ko zatayi zata daura katon hijab abinda shi kuma abinda ya ja hankalin sa da ita kenan. Dan ko gidan samarin nata zata bata zuwa ba hijab sai taje can take cirewa ta sheke ayar ta. Gata a fuska kamila wannan yasa yaji ya kamu da son ta.

Yanzu ma yana tsaye cikin wata mota daban dan ya gane ta gane dayar motar duk da tint ce a ciki wannan yasa ya canja mota yana tsaye ta fito ta tsaida Napep ta shiga binta yayi har gidan saurayin ta da suke masha'ar su. Kullum yana ganin shigar ta gidan wannan yasa ya kawo ko gidan yan uwan su ne.

Parking yayi ya jingina kan sa a jikin kujera yana sake ajiyar zuciya, A ransa yana fadin tayaya zai tunkaro yarinyar nan sannan tayaya zai jewa Momyn sa da maganar ta bayan ta makale sai ya auri yar ya kanwar ta Hannah.

Hannah kyakyawa ce amman kuma shi yana da kishi yana son mace mai kame kai da suturta jikin ta abinda yaja hankalin sa ga Hafsat din ma kenan har ya kamu da son ta dan sau dama yana ganin ta tazo wucewa sanye da hijab har kasa. Hannah kuwa tai ta saka kaya damammu abin shi kuma ke bashi haushi kenan dan baya son maza na kallan masa abinda yake so.

Ahmad kenan 'da wajen Alhaji Aminu Babban likita ne a AKTH kuma shi kadai ne 'da namiji gun iyayen sa, sauran duk yayen sa ne mata har su hudu sai kanwar sa mace, wannan yasawa iyayen son sa bama uban sai abinda yake so yake masa kanwar sa daya mace. Momyn sa ba tin yau ba take fada masa ya auri yar kanwar ta Hannah wacce yanzu ta dawo gidan su Ahmad din ma dan yadda itama take son sa amman duk abunda take masa na kyautatawa a banza domin kuwa shi ba son ta yake ba. Yadda take shige masa tace zata rumgume shi na kara bata masa rai.

Shekarun sa talatin da biyu yayi degree har master din shi a bangare tattalin economic wanda yake aiki a bank na can Abuja. Dalilin ganin Hafsat yazo unguwar wucewa ne idon sa ya sauka akan ta lokaci daya yaji yana son ta da gaske abinda yaja hankalin sa kuma shigar ta, wannan yasa kullum yake hanya unguwar su ganin ta.

Ajiyar zuciya ya sauke ya bar unguwar. Gida ya nufa yana shiga ya nufi bangaren sa. Part din sa yayi yana shiga kanwar sa Basma ya shigo dakin tace
"Yaya ka dawo ashe?"

Mikewa zaune yayi yana dafe kai. Tace
"Yaya baka jin dadi ne?"

"Basma mikon ruwa"
Mikewa tayi ta dauko ruwa a firij sannan ya koma kan kujerar da yake zaune ta bashi amsa yayi ya sha sannan ya koma ya kwanta ba komai yake gani ba sai Hafsa cikin shigar ta mai kyau da burge duk wani 'da mai hankali.

"Yaya Momy fa ta saka ranar bikin ka kai da Anty Hannah nan da one month!"
A zabure ya dago yana bin Basma da kallo.

Basma ta ce
"Wai yaya meyasa baka son Anty Hannah ni sam ban ga aibun ta ba wallahi."

"Basma ba Hannah ce bana so ba sm halayar ta ce bana so. Ni mutun ne ma kishi wanda bana son kaya na ya zama kowa yana iya ganin min su ina son sirri da boye tsuraici amman ki kalli Hannah da kalar kayan da take sawa sam bata da kamun kai."
"Haka ne Yaya amman fa kar ka taurara nuna kyamar dabi'un ta dan Allah sai ya jarabce ka da samun ta. Ni dai nasan Anty Basma na son ka dan haka nasan zata bi dukkan abinda kake so dan haka ko kunyi aure ba zaka samu matsalar gyara ta ba."

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now