Chapter 1 page 9

280 22 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 0⃣9⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

Washe gari haka Jummai ta fice ko tsayawa ta kan Sa'adatu (Yaya Babba) bata yi ba. Yaya Babba kuwa daga nan gidan Hanne taje wata unguwa suka isa ta masu kudi anan suka fara bin gida suna fadin
"Dan Allah a taimaka mana da sadakar abinci ko kayan sakawa."

Haka suka dinga bi gida gida cikin hukuncin ubangiji kuma Allah yasa ba laifi sun samu sadaka don sai da suka cika wani ƙaton buhun shinkafa har biyu da kayan sawa hadi da kayan abinci wani gidan kuma a basu dari biyu ko dari uku. Sai da suka dawo gida da dubu hudu Banda shinkafa kwano biyar da taliya guda ashirin da kayan sakawa daga na yara har na manya.

Tare suka raba da Hanne inda Hanne ta barwa Sa'adatu kayan ƴan matan ta ce ta kaiwa yaran ta.

Sai da suka yi kwana biyar suna bin manyan unguwanni suna bara sannan suka yanke shawarar yanzu yaran su kananu zata debo don sun gane suma ana samun alheri dasu sosai.

Jummai sun kulle ita da Hajiya Kaltum don har tace mata ta kawo mata yaran nata.
Sa'adatu kuwa yau yaran ta ta deba da ɗan shekara biyar da ɗan shekara hudu ta fita da su sauran ƴan matan suna fadin
"Baba ina zaki?"
Ta ce "yanzu zan dawo."

Tana fita gidan Hanne ta isa tana zuwa suka fita can wata unguwa suka isa a hanya suka koyawa yaran in sunje gida me zasu ce.

Ai kam suna zuwa gidan farko da yake gidan kato ne na dai dai mai rufin asiri ba gate sai kofa don haka su Hanne suka tsaya a waje, yaran ne suka shiga cikin da sallama da maganar ba da ko gama kwari ba ta yi ba.
Matar gidan dake tsakar gida ta amsa tare da fadin
"Daga ina haka."

Dan shekara biyar din ne ya ce
"Hajiya don Allah a taimaka mana da abincin da zamu ci ko kayan sawa."

Kallon su Hajiya ta tsaya yi duk tausayin su ya kama ta don haka ta shiga daki ta debo kayan yaran da zasuyi musu dai dai sannan ta isa gun mai gidan ta fada masa abinda ya faru ya ce ta basu shinkafa ko kwano ce da dari biyar. Haka ta yi ta kai musu da kyar suka fita da kayan Sa'adatu ta karaso ta amsa tana fadin
"kai mungode amma."
Nan ta zauna suna bude kayan da aka basu suna murna ɗayan gidan ma yaran suka tura nan ma akai musu alheri don taliya aka basu guda biyu da sabulun wanka. Ranar dai yaran suka dinga aikawa cikin gidajen mutane sun kowa samu musu kayan abinci da dan kudin da baza a rasa ba daga nan gun barar su na jiya suka nufa.

Jummai kuwa daga gida gun bara suka isa acan suka tadda Hajiya Kaltum har tazo tana ganin ƴan matan Jummai ta hau yabon su domin kyawawa ne sun fi yar tama kyau. Jummai ta bari agun ta dauki yaran ta isa can gidan karuwai dasu ana ganin ƴan mata masu jini a jiki aka hau rubibin su Fauziyya dai fuska ta hade Farisa kuwa sai rawar kai take yi a haka ta samo musu manyan Alhazawa yadda daga nan suka fice dasu don suna da gidan da suke hutawa da ƴan matan.

Fauziyya dai bin Alhaji da aka hada ta dashi kawai take yi har suka isa gidan sai da suka shiga falon gidan sannan ya janyo ta jikin sa da sauri ta janye jikin ta.

Dariya yayi ya ce
"zauna ina zuwa."
Zama ta yi tana bin ɗakin da kallo.

Cikin kitchen ya shiga ya dauko wata kwaya a cikin lokar kitchen din sannan ya bude firij wani lemo ya dauko ya saka magungunan da ya dauko guda uku ya cilla ciki, daya na feeling ne dayan kuma saka bacci ne, sai da ya tabbata sun narke sannan ya fita zuwa falon nasa.

A zaune ya sameta ajiye lemon ya yi  ya dauki cup ya zuba mata. Mika mata ya yi yana kallon ta yana lashe bakin sa kamar wani tsohon maye, ya ce
"Bismillah!"

Amsa ta yi ta kafa kai dadin lemon yasa ta shanye shi dukka. Suna zaune a haka ya fara mata magana ji ta yi jikin ta ya yi sanyi tare da Jin wata matsanaciyar sha'awa wacce bata taba Jin ta ba. Idon ta taji yana rufewa, hannu ta saka a tsakanin kafafun ta tana cije baki. Hannunta ya kamo amman duk abinda take ji na tana bukatar namiji ture hannun sa tayi tana kokarin mikewa amman kafin ta mike sai ta fada kan kujerar tana mai bingirewa da bacci.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now