Chapter 1 page 96

171 15 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 9⃣6⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*



Hannah kuwa sam taki ta kwantar da hankalin ta Mami sai biye mata take yi. Mahaifiyar Hannah ce taje ta fadawa babar su nan tasa Mami da Hannah suje. Bayan sunje tai musu fada sosai. Sannan ta kalli Hannah tace
"In auren ne bakya so ki dawo gida ai wannan rashi  hankali ne dake kadai zai zauna.ko zaki hana sa auren ne."
Sai da tayi musu tatas sannan suka nustu amman Hanna sam bata saduda ba.

*
Ana kai Hafsa Basma tazo da me makeup nan da nan aka farai mata makeup kan kace me an gama amarya tayi kyau aka bata wasu kaya ta saka. Daga nan Basna ta dauki Hafsa suka tafi wajen Partyn. Tana mota Basma ta fita bata jima ba sai ga Ahmad nan cikin manyan kaya kalar kayan jikin Hafsa ya shiga motar ya dago fuskar ta.

Wani murmushi ya saki yana fadun
"Masha Allah kinyi kyau ma'ul ayn!"
Ta saki murmushi. Ya kamo hannun ta suka fito. Basma tai musu jagora zuwa cikin wajen taron. Manyan yan mata ne da samari haka suka karasa inda aka tanadar musu.

Aka fara gudanar da partyn cikin kwanciyyar hankali aka gudanar da komai har aka gama aka tashi suka fito aka maidasu gida.

Ahmad kuwa bakin sa ya ki rufuwa ya shigo dakin fuskar sa dauke da sallama ko yan rakiya bai nema ya shiga dakin. Hafsa na zaune a kan gado zuciyar ta sai bugawa takr ya shigo dakin.

Kallon ta ya tsaya yi tana rufe cikin mayafi ta. A hankali ya karasa ya durkusa a gaban ta yace
"Amincin Allah ya tabbata a gareki amarya ta."

A hankali ta amsa ya saka hannu ya bude fuskar ta bai san lokacin da ya zame ya zauna ba. Ya kura mata ido ita kuma tayi kasa da kanta. Mikewa yayi ya dago kan ta sai yaga tana hawaye da sauri yace
"Me ya faru Ma'ul ayn?"

Kai ta hau girgizawa yace
"Fada min menene?"
Hannun sa ta kamo tace
"Ka yafe min Deedat!"

"Baki min komai ba Ma'ul ayn!"
Ya jata jikin sa ya rumgume yana fadin
"Menene?"

Kai ta hau girgizawa tace
"Zan fada maka wani abu amman ban san tayaya zaka amshe shi ba."
"Baki da matsala komai daga gunki mai kyau ne kuma zan amsa hannu biyu,  amma kinsan me?"

Kai ta girgiza yace
"Ki daina kukan nan yana tadan hankali!"
Kai ta gyada.

Yace
"Kan komai ya kamata mu fara alwala muyi sallah ta godiya ga Allah sai mu zauna ki fadan ko menene ko?"

Kai ta gyada yace
"Muje muyi alwalar to!"
Ta mike ta shiga tayo shima ya shiga yayo alwalar. Yazo ya jasu sallah bayan sun idar yai mata addu'a sannan yai mata tambayoyi akan addini duk ta amsa masa. Murmushi yayi yace
"Alhamdulillah. Yanzu ina zuwa."

Ya mike ya fita tabi bayan sa da kallo hawaye ne ya zubo mata. Yana fita ya dauko ledar hannun sa wayar sa yaji tana kara alamar shigowar sako. Zaro wayar yayi yana fadin
"Waye a wannan lokacin?"

Ya bude yaga sako ya bude yaga an rubuto
"Kasan wa ka aura kuwa? In kana son karin bayani ka hau whatsapp ka ga wani sako na turo maka."

Data ya kunna ya bude app din yaga sako ya shigo yana budewa yaga Hafsa kwance a jikin wani namiji daga uta sai inners a jikin ta. Ledar hannun sa ce ta zame ta wadi ya wara ido. Layin ya fara nema ana dagawa aka sheke da dariya aka ce
"Hhhh kai kana ganin ka auri kamila ko? To saura nace. Ba wanda ya isa ya auri Hafsa sama dani. Hafsat tawa ce ni kadai kaji ko dan haka kasan inda dare yai maka."

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now