Chapter 1 page 107

160 10 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 1⃣0⃣7⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*



Karfe shida da mintina ya shigo unguwar bai shiga gida ba yai parking yayi a compound yayi alwala anan ya juya ya tafi masallaci.

Halima kuwa na gida ta ci kwalliya mai kyau da daukar hankali kamar ka sace ka gudu haka bangaren Sadiya ma.

Bai baro masallaci ba sai da yayi isha'i tare da shafa'i da wuturi sannan ya shiga. Bangaren Halima ya fara kalla ya saki murmushi yayi sashen Sadiya. A falo ya same ta tana kallo a TV da sallama ya shiga ta dago ta amsa ta mai da kanta kan TV. Ya shiga ya xauna tace
"Sannu da xuwa."

"Yauwah me yake damun ki ne?"
"Ba komai."

"A'ah fa."
"Ba komai me ka gani?"

"Naga kin canja ne."
Tai murmushi kawai. Yace
"Ko da abinda kike so ne?"

Kai ta girgixa ya mike yace
"Shikenan bari naje."
Ya juya ya fita yana girgixa kai ya gane kishi ne ko rashin son rabuwar shi. Allah sarki Sadiya shima yana son ta kuma ya bata waje a zuciyar sa ko dan abinda ta bashi da son da take masa da kulawa dashi da kishi dashi.

Yana shiga bangaren Halima wani kamshi ya daki hancin sa. Ido ya lumshe yana mai tasbihi a zuciyar sa. Kan ya bude yaji an rumgume shi tare da jin wani nutsuwa a jikin sa. Ido ya bude ya sauke akan ta, tana masa murmushi,  bai san lokacin da murmushi ya sauka akan fuskar sa ba. Ya dauke ta cak sukai kan kujera ta rungume shi tace
"Sannu da zuwa!"

"Yauwah My Love na same ki lafiya?"
Ya fada yana shin shinar wuyan ta.
"Alhamdulillah my Happiness ya aiki!"

Bai masan me take ba yana lallubar ta,  ganin yana son ya wuce wani gun ta dakatar dashi tana fadin
"Ka bari kaci abinci mana."
Murya na rawa yace
"Wane abinci ina dake."

"Please My happiness,  bana son yunwa ta taba min kai."
Dagowa yayi yana kallon ta yace
"You means you care for me?"

"Haba Kai kuwa dole ai na kula da kai "
"Halimatus Sadiya!"

Dagowa tayi ta kalle shi,  ya kura mata ido sai ya saki murnushi ya saukar da kansa, kallon sa ta tsaya tace
"Ya dai menene? Baka taba kiran suna na kamar haka ba!"

Fuskar ta ya shafa yace
"Kinyi kyau Baby na."
Hannun sa ta kama tana fadin
"Ba shi zaka fada ba ka fada min."

"Yaushe kika sanni haka Baby?"
Murmushi ta saki tayi kasa dakai,  ya saka hannu ya dago kan ta. Suka sakar wa juna murmushi sai tace
"Tell me!"

"Baby u never said you love me."
Gaban ta taji ya fadi ta dago da sauri tana kalllon sa. Munyi rayuwa mai tsayi ina fada miki ina son ki but baki taba cewa kina so na ba."
Mikewa tayi tace
"Muje kayi wanka ko?"

Hannun ta ya janyo ta fado kan sa dagowa tayi kan ta da nashi suka hadu,  kallon juna suka tsaya yi, na mintuna sannan yace
"Ki fada min My Love me kike ji akai na?"

Ido ta lumshe,  ya ce
"Please Baby nah."
"Muje kai wankan ko tukkuna."

"No Baby tell me first!"
"Uhmm kai masoyi na ne wanda ban taba zaton ina da wanda ke so na kamar ka ba. Hakika kai jigo na ne farin ciki na rayuwa ta kuma aljanna ta rasa ka tamkar rasa rayuwa tace."

WANNAN RAYUWARDove le storie prendono vita. Scoprilo ora