Chapter 1 page 27

256 13 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 2⃣7⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*




Muhammad ta kalla tace
"Tin lokacin na cire rai da rayuwa na tuba nai nadama na koma ga Allah. Wannan dalilin yasa ko ka aiko naje bana fitowa dan ciwo nayi sosai naki naje asibiti ne na kwamace Allah ya cigaba da azabtar dani. Muhammad na fitar da rai da zan aure ko zan auren nasan ba zan samu kima da daraja agun wanda zan aura ba.
Farisa taki ta shiryi sam Hafsa ma sanadin mutuwar Anty Haule ta tuba.
Hakika rayuwar dana zab'arwa kaina ba rayuwa ce ta abun tutiya da tak'ama ba. Rayuwa ce tamkar ta dabbobi, inda mutum yake da damar yin kowane kalar sab'o ba tare da tunanin makomarmu ba. Na tafka kuskure a rayuwata Muhammad. "

Ta karashe tana mai sakin wani kukan. Muhammad baisan sadda ya janyo hannunta ba ya sanya cikin nashi, a lokacin hawayensa sun kasa tsayawa sai zuba sukeyi. Yana son cewa wani abu sai kuma ya fasa gami da sakin hannunta ya janyo handkerchief data rike ta kasa goge hawayen dashi ya mka mata.

"Kiyi hakuri."
Ya fada murya a dusashe.

Ta dago kwayar idanunta tana dubansa, yayi amfani da wannan damar ganin bata da niyyar karb'ar handkerchief din ya kai hannu zai share mata fuska,ta rike hannun tana girgiza masa kai kafin ta mayar mishi da hannun kasa. Dariyar bakin ciki ta saki tana mai kauda kanta

"Kada ka wahalar da kanka ga fidda hawayen da bazasu taba daina zuba ba a rayuwata Muhammad. Banajin zan daina zubar hawaye. Banajin ina da sauran dama na jin dadi a rayuwata. Don haka kabar sharemin abokan rayuwata, na tabbata su kadai sukafi kusanci dani, banason suma a rabani dasu. In nai kukan ina jin sauki a rai na bani da wanda zan kaiwa kuka na ya lallashe sai Hafsa wacce itama kanwa ce ya kamata na rarrashe ta itama."

Fauziyya ta fadi cikin sheshek'a kuka. Ya sunkuyo yana duban fuskarta sannan yace
"Nayi maki alkawarin idan har ina raye Bazan barki ba Fauziyya. Daga yau inaso ki bani damar kasancewa mai share maki su, idan ina raye Ni Muhammad bazan k'ara barinki kiyi rayuwa makamanciyyar wannan ba zan baki gata da baki taba samun irin......."

Sai kuma yai shiru yana kallonta itama shin take kalla. Kai ta dauke yace
"Kin tafka kura kurai da yawa a rayuwarki Fauziyya ciki kuwa babban shine cigaba da rayuwar bariki maimakon ki kame kanki da mutuncinki, a'a saima zuciya data kwasheki kika maida kanki karuwar gaske. Kinyi ganganci kin manta da dokokin addininki daya hanemu aikata zina. Ki godewa Allah ma a gefe kina da iyayenki da yan uwa, wasu fa basu da ko daya, wasu rayuwarsu har su mutu cikin kunci da bakin ciki sukayin ta amma basu fada karuwanci ba, illa sun kasance masu tawakkali da mik'a zuciyoyinsu ga Allah."

Fauziyya babu alamar jin haushin maganar da Muhammad ya fada a fuskarta saima kallo da take binsa dashi tana murmushi kafin daga bisani hawayenta su zubo. Ganin hawayen ya sanyashi tsayawa da maganarsa

"Ina fatan ban b'ata ranki ba Fauziyya?"
Ta girgiza kai tana dan murmushi hawaye na kara zubowa a idon ta.

"Wallahi baka b'atamin ba Muhammad. Asalima burgeni kayi ,dadi nakeji a kasan zuciyata. Tunda na soma harkar barikanci, babu wanda ya taba yunkurin gayamin gaskiya sai Almajirar nan Na'ima da kai. Tun farko haduwarmu saida na fahimci kai din daban kake. Ban kara sakankancewa da lamuranka ba saida na hadu dakai a karo na biyu. Wanda anan son ka ya kara shiga ta. Tabbas Muhammad kai mutumin kirki ne wannan ne yasa nayi mamakin yanda kazo kake so na da aure"

Murmushi Muhammad  yayi ya numfasa ya gyara tsaiwa kafin ya dubeta
"Ki amshi soyayya ta kila Allah ya amshi tuban ki ne ya aiko miki ni. Ina son ki Fauziyya."

Murmushi ta saki tace
"Ai na fada maka tin gani na da kai na farko na fara son ka, sai jiya da ka tafi na kara tabbatarwa da kai na ina son ka. Amman..."

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now