Chapter 1 page 75

136 4 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 7⃣5⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

Karfe uku da Rabi an gamai Mata kwalliya amarya tayi kyau cikin peach kala material Wanda akai wa Dinkin doguwar riga sai mayafin kayan da aka dauro Mata a ka aka makele shi. Shigar Tai Mata kyau Kuma Bata nuna tsiraicin ta ba Dan dogon hannu ne Kuma ta bude. Su kansu masu makeup din Basu ta kwalliyar da ta burge su kamar ta Ummu ba. Tayi kyau har ba a magana.

Sallah tayi tana zaune aka ce anzo daukar ta lokacin hudu da kwata. Mai makeup din da kanta ta rakata har bakin wajen. Wata sabuwar mota ta gani fara tas a wajen tsayawa sukai zata Kira number ya bude motar ya fito.

Sanye yake cikin milk din shadda wacce take kyalli ta Masa kyau ya sa bakin takalmi sau ciki ya daura hula Mai kyau da tsada a Kansa. Hannun sa daure da agogon azurfa sai zuba Kamshin yake.

Tin da ta daga Kai ta kalle shi Bata Kara dagowa ba Dan yai Mata kyau ba kadan ba. A hankali ya karaso ya kamo hannun ta. Suka wuce wajen mota.

Shiga tayi Shima ya shiga sai ya tsaya kallon ta.
"Baby Mie Kinga yadda kikai kyau kuwa!"

"Ka fini kyau Yaa Muhammad!"
"Wa ya fada miki ban taba ganin make up din da Tai kyau kamar Taki ba. Komai naki da ban ne Habibty nah."

Murmushi tayi yazaro waya yai musu picture ya nuna Mata yace
"Kinga fa?"

Amsa tayi tana kallon yadda sukai kyau suka Dace da juna. Mika masa tayi yace
"Ibrahim Kai mu Ai Mana pictures kan mu karasa wajen!"

"To Yaya!"
Yace
"Ina yini Anty?"

"Lafiya Lou! Ya kake?"
"Alhamdulillah!"

"Masha Allah!"
Ya tada motar suka bar wajen. Gun hoto ya kai su mai kyau da tsari nan akai musu wajen kala goma aka turo masa sannan aka basu copy din suka fita.

*
Karfe biyar suna compound din wajen har an fara lectures. Anty Zainab ce ta karaso itama taci kwalliya cikin wani rantsatsen less tayi kyau sosai. Motar ta leka tana ganin Ummu ta saki mutmushi tana godiya ga Allhah.

Fitowa sukai akai musu jagora zuwa wajen da aka tanadarwa amarya da ango zama sukai aka daura faga inda aka tsaya a lecture din. Lecture ake mai ratsa zuciyar mai sauraro akan aure da biyayya ga miji. Kowa yai shiru yana sauraron lecture din.

Gefe na kalla naga tawagar su Mamah ce da su Rukayya da Sailuba sun ci kwalliya sun cakare ba laifi sai buda hanci suke gaban su plate ne na abinci sai bowl na pepper soup dayan kuma snack ne da lemo da ruwa an ajiye musu kowa abinda ke gaban sa kenan.

Can kuma su Umma ne da wasu daga kawayen ta suma sun ci kwalliya mai kyau kowa da mayafin sa akai. Sai gefe kuma dagin Abba da Umma ne sai wasu daga kawayen Ummu tin na isilammiyya har da wanda sukai university ma. Daya bangaren kuma dangin Hajiyar Muhammad ne da abokan sa daga can gefe. Kuma kowa an ajiye masa abincin sa a gaba.

Sannu a hankali kuma aka fara rabon kayan da Anty zainab ta bayar ayi. Shima dai lemo da ruwa ne a jakar sai cake da springroll da donot sai memo da aka rubuta suna  su da kur'ani da jaka. Kowa haka aka dinga bashi.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now