Chapter 1 page 49

205 17 4
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 4⃣9⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*



*
**
***
****
*****
******
Yana wasa da gashin kanta ma bai san har tayi bacci ba sai da yace
"Bae! Bae!!"
Yaji shiru sannan ya leka fuskar ta. Baccin ta take sosai hankali kwance. Murmushi ya saki ya gyara zaman sa yadda zata ji dadin baccin nata.

Sosai tayi baccin dan tun wajen karfe biyu sai hudu saura ta farka. A jikin sa taji ta. Dagowa tayi tagan ta kwance akan sa shi kuma yana kan kujera. Mikewa tayi wanda hakan ya farkar da shi.

"Har kin tashi?"
Ido ta zaro ta kalli agogo tace
"Har kuma? It's almost time for asar fa."

Agogo ya kalla ya mike da sauri yace
"Tab ai kam gashi kuma sai nayi wanka ba."
"Wanka kuma?"
Ta tambaya.

Murmushi yayi yace
"Ai indai zan jini jiki a jikina sai kin haifar min da wani abun."
Ido ta zaro sai kuma ta mike tayi daki da sauri tana fadin
"Kaii dan Allah!"

Mikewa yayi yana murmushi ya bi bayan ta. Zaune ya same ta a gefen gado. Zama yayi yace
"Ko zaki taimaka min?"

"Dame fa?"
"Wankan mana."

Ido ta zaro tace
"Wayoo ni dai dan Allah kayi hakuri wallahi kunya nake ji."
"Naga alama but wannan kunyar zan cire ta in ajiye ta gefe saboda naga alama in na bar ta zatana cutar dani."

Ya fada yana zare rigar sa. Da sauri ta mike ta fice falo. Tana zaune ya fito daure da towel kan ta tai sauri tayi kasa dashi tana wasa da yatsun hannun ta.

Fita yai bai jima ba ya dawo kallon sa tayi ta gefen ido taga yana goge kansa da karamin towel Daki ta mike ta shiga ta fito daure da xani da hijab a jikin.

Wankan ita ma tayo ta dawo taga har ya canja kaya zai fita dan ana kiran sallah.
"Wankan me kikai?"
Ya fada yana kallon idon ta. Kanta tai saurin daukewa tana fadin
"Daman wankan kala kala ne?"

"Baki sani ba?"
Ya tambaya. Kai ta dauke zata shige yace
"Kema kin sani ai!"

"A'ah!"
"Au haka kika ce ko? Shikenan zan saka ki yin wani daban ba wanda kike son kice min kin sanin.
Yai murmushi ya fice.

Shiryawa tayi tai sallah sannan ta zauna tana tasbihi tare da godiya ga Allah sannan ya kara neman yafiyar Allah akan abubuwa da ta aikata a baya.

Tana zaune har biyar da rabi tai mamakin to ina Muhammad ya tafi har yanxu bai dawo ba. Tagumi ta zuba tana Addu'a Allah yasa lafiya domin kuwa da an idar da sallah yake dawowa. Sai karfe shida ya dawo ya zauna yana maida numfashi daga gani ya sha yawo ne. Da sauri ta dauko masa ruwa a kula mai sanyi ta bashi. Amsa yayi ya sha ya sauke ajiyar zuciya sannan ya kalle ta yace
"Allah miki albarka."

"Amin. Amman ina kaje?"
Ta fada cike da damuwa. Kallom ta yai ya dan saki murmushi yace
"Kudin hannu na ya kare naje na samo bashi ne kinga ba komai a gidan ko?"

"Amman meyasa baka fada min ba akwai kudi a guna in baka kana juya su muna rufawa kan mu asiri."
"A'ah ba zan amshi kudin ki ba."

"Haba Mijina abu na ai naka ne. Dan Allah ka amsa dubu dari shida ne akwai wani store da na bude me zai hana ka amsa kana kular mana dashi kudin kuma in akwai wani abu da ya dace sai ayi me kace?"
Kallo ta ya tsaya yi sai kuma can yace
"Ni bana son in amshi kudin ki kuma su zo su dulmiye ne...."

"To menene ai shikenan haka Allah ya tsara."
"Baby ni dai bana so na amshi kudin ki."

"Saboda baka yadda dani ba. Ko saboda kana ganin zan maka gori ko ince ka ban abu na wata rana?"
"Ba ko daya Baby amma....."

"Amman me? Ni dai in har ba dan abinda na fada bane ka amsa."
"To shikenan!"

"Yauwah yau me xamu yi to? Me kake so kaci?"
"Komai my queen ta bani ina so."

"Sure?"
"Yes!"

"Ok yau babu girki anjima muje resturant kawai muci abinci hakan yayi maka?"
"Indai yayi miki nima ya min."

Fuska ta bata tace
"A'ah ban yadda ba gaskiya. Ka daina yadda da komai xan fada ka sani ko ban yi dai dai ba."

"No Zabin Fauziyya shine nawa?"
"To ni kuma naka shine nawa!"

Yai murmushi ya dan ja hancin ta yace
"Kin ganki nan ko akwai wayo."
Murmushi kawai tayi.

Bayan sunyi sallah isha'i suka shirya tsaf. Fauziyya sanye da riga da siket na material cotton ne sun mata kyau sai Muhammad dake sanye da bakin wando da blue black t-shirt.  hijab ya dauko ya mika mata. amsa tayi ta saka ya saukar mata har kasa. Murmushi yayi yace
"Yauwah."

Ta kalli kan ta tace
"Me?"
"Kinyi kyau mana."

"A hakan?"
Ta fada tana fita falo. Yace
"Ai ni a ko yaya ma kyau kike min. Wannan shigar kuma kinga tana miki kyau bame kallon min mata sai ni kadai."

Murmushi tayi ta mika masa ATM din ta ya amsa suka fita. A kasa suka karasa titi suka hau napep suka karasa wani wajen cin abinci mai kyau. Suna sauka suka biya mai napep din ciki suka shiga suka samu waje suka zauna.

Waitress tazo ta basu menu amsa yayi ya mikawa Fauziyya ta kalle shi tace
"Ka zabar mana man."

"No abinda kike so shi zanci."
Amsa tayi tai selecting ta mika. Nan da nan akai serving nasu.

Shi ya dinga bata tana bashi a haka suka dinga cin abincin kamar ba za a gama ba dan suna yi suna soyayyar su. A haka suka gama suka mike suka je ta fada masa pin din ta aka tura kudin suka fito. Zasu tsallaka titi kenan taji ance
"Fauziyya!"

Da sauri ta juyo. Shema ce daya daga cikin kawayen ta na bariki kallon ta ta tsaya tace
"A sannu ya gida?"

"Baki ganeni bane Fauziyya?"
"Na gane ki mana."

Kallon Muhammad tayi dake nesa dasu kadan tace
"Wannan handsome din fa amman gaskiya yayi gashi yaro dashi."

*
**
***
****
*****
******
*******
*Am sorry it's too short but akace da babu gwara ba dadi ko. Please manage in na samu chance gobe zan kara muku typing*

*Sai kuma ban hakuri da zan yi duk da baku san meya rike ni haka ba kusan kwana goma sha no update but wadan da suka kira ni duk na fada musu ban da lafiya da masu bibiyar WA NAKE SO? ayi hakuri nima ban so hakan ba amman haka Allah ya tsara bani da lafiya ne amman Alhamdulillah am ok now. Sai kuma biki da muke na daya daga cikin assocition din mu wato FATIMA MUHAMMAD SANI ZARAHARKEL (HABIBTY NAH) ina me rokar ku sa mata albarka ku mata addu'a Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a mai albarka Allah kore duk wata fitina da abun ki. Amin.*

*Bayan shi kuma ku saka kanwa ta Nusaiba S Indabawa a addu'a akan Allah ya bata lafiya yasa kaffara Allah tashi kafadun ta. Amin*

.*Nagode da kaunar da kuke min. Wanda suka kira ban dauka ba kuyi hakuri wanda suka kira kuma mukai magana da masu text duk nagode Allah saka da alheri.*

_Antty_

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now