WANNAN RAYUWAR Book 1 page 1

1.4K 57 4
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Book 1
page 0⃣1⃣

*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*ABINDA YAJA HANKALIN NA WAJEN RUBUTA WANNAN LITTAFIN MAI SUNA WANNAN RAYUWA💐💐💐_ SHINE IRIN RAYUWAR DA MUKA  TSINCI KAN MU A CIKI, YANZU WATO WANNAN ZAMANIN KO A INA ZAKAJI MAGANAR AKE, DAGA GIDAJEN TV, RADIO, DA ALUMMA. BA AKAN KOMAI BA SAI AKAN MATSALAR DAKE DAMUN MU A WANNAN RAYUWAR TAMU TA YANZU SON ABIN DUNIYA, RASHIN GODIYAR ALLAH, RASHIN HAKURI, ZARGI, RASHIN TAWAKALLI, ZINACE-ZINACE, BARACE-BARACE, DA DAI SAURANSU. TO WANNAN LITTAFIN  ZAI YI DUBA YAYI BINCIKE AKAN WAƊAN NAN ABUBUWA DA WASU DA YAWA MA INSHA ALLAH. INA FATA DA ADDU'A ALLAH YASA WANNAN RUBUTUN NAWA YA ZAMA SILAR SHIRIYAR DA GYARUWAR RAYUWA MUTANE DA YAWA DA SUKE AIKATA MAKAMANCIN WAƊAN NAN ABUBUWAN. AMEEN*

******************************************************

Zaune yaran suke sun kai su goma sha a tsakar gidan, ko wacce ta hada kai da gwiwa ƴan yaran kuma sai kuka suke, saboda yunwar da suke ji. Uwar gidan su ce ta fito daga bandaki tana kallon su tare da girgiza kai ta rasa yadda za ta yi.

Dakin mai gidan ta nufa tare da yin sallama a falon ta samu matar sa ta uku tana jiran ya fito, muryar sa suka jiyo daga bedroom din sa yana fadin
"Kinga Haule ni Bani da kudi yanzu fita nake son na yi na samo kudin, ku kenan kullum a bani-bani shin wai kudin debowa ake yine ko me? Haba Don Allah."

Muryar Haule suka jiyo tana fadin
"Gaskiya Alhaji ni ba zan iya ba, wallahi yunwa nake ji tun jiya fa rabo na da abinci ai ko baka tausaya min ba ka tausayawa abinda ke ciki na."

Baro ta ya yi ya fito falo nan ya samu Samira da Sa'adatu wani kallo ya bisu da shi kafin ya ce "Lafiya?"

Uwar gidan ce wato Sa'adatu ta ce, "Alhaji gani muka yi har sha daya ba a daura sanwar safe ba ga lokacin na rana na yi..."

Bata karasa ba ya katse ta, ta hanyar cewa "To me zanyi?"
Samira ce ta ce "Alhaji amman kasan dai kayan abincin duk ya kare ko, ko kwayar hatsi babu a gidan nan."

"To uwar ci, yanzu ni ya kike so in yi ne, ni me na ci? ita ma waccan ga ta can ta saka ni a gaba yunwa take ji to da wanne zan ji ne? Na fada miki bani da kudi bari na fita naga ko zan samo wani abu."
Sun san in har ya saka kafa ya fita to sai dare zai dawo, kuma su a yadda suka san Maigidan nasu bai da rashi Sam sai dai mammakon sa, da aure zai yi zai kashewa yarinya kudi ita da iyayen ta amman da an shigo gidan ba cin yau bare na gobe ba kudin ne bai dashi ba fitar dasu ne bai son yi.

Wanda in ya ajiye kayan abincin a shekara sau daya anci sa'a, kullum sai dai ya jefe su da dari biyar ko bakwa yace suyi girki bayan ya'yan gidan sun doshi su ashirin don wasu iyayen su basa gidan. Haka kullum suke fama shi ya sa wani lokacin har gwara sun siyo garin kwaki su sha da suce zasu yi wani abincin saboda kudin shinkafa ma kadai kudin ba isa zai yi a siyo ba, don a wannan zamanin namu yar hausar ma kwano ta doshi dubu daya, to kudin da aka basu ko dubu dayan baya kai wa, wai nan kuma tin safe, rana da dare.

Sa'adatu ce ta ce "Toh Alhaji ko Auwal zan aiko ko garin kwaki ne a amso mana a shagon Bulama yaran nan su samu su sha kan a samo abinda za'a girka don sai kuka suke mana tin safe."

Shi kansa yasan 'Babban Alhaji ne don haka kunya da nauyi yake ji a ganshi yaje yace a bada garin kwaki wannan yasa ya ce, "Alhaji Imran ya bani ajiyar wasu kudi bari na dauki aron dari biyar na baku ku yi girkin."

"Amman Alhaji kasan dai dari biyar ba abin da za ta yi mana a gidan nan ko?"
Samira ta fada.

Juyowa ya yi yana kallon ta yana fadin "To uwar ci, da ya ke, ke runbu ce a ina dari biyar tai muku kaɗan, kuna dai godewa Allah wallahi wani gidan ma kalar dari biyar din ma basu samun damar ganin ba. Kina ji dai nace ranta zan yi tin da haka ne bari na fita in na samu na aiko muku da shi."

Sa'adatu ce ta ce "Kayi hakuri Alhaji bada dari biyar din Allah ya sanya albarka a ciki."

"A'ah da ku bari mana."
Ya juya ya yi cikin dakin. Haule ce ta fito tana tura ciki ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun falon tana fadin
"Ina kwana Yaya Babba?"

"Lafiya Lou Haule ya karfin jikin?"
"Alhamdulillahi!"
Ta fada tana dafa cikin don ji ta yi ɗan cikin nata yana zillo don shima yunwa yake ji.

Sa'adatu ce ta kalli Samira ta ce
"Kina son ki ja mana a ƙi bamu dari biyar din da yaya zamu yi da waɗan can yaran dake ta kuka kenan?"

Tsaki ta yi ta ce  "Gaskiya Yaya Babba ni na gama gajiya da halin Alhaji, kalle mu fa don Allah duk mun rame mun yi baki ba cima me kyau ba sabulu mai kyau haba don Allah."

Murmushi mai ciwo Yaya Babba ta yi ta ce
"Samira kenan, sai hakuri ai."

"Ina wallahi hakuri na ya kare, ƴa daya gareni don haka ba zan zauna a gidan nan in mutu ba gwara tin wuri nasan inda dare yayi min."
Yaya Babba da bata son ko kaɗan wata a cikin su ta ƙara cewa zata tafi don tasan kula da wasu ya'yan za'a ƙara. bar mata duk da yanzu ma ita ke kula dasu ko iyayen na nan.

"A dai ta cigaba da hakurin wata rana sai labari."
"Kullum haka kike fada Yaya Babba yanzu kusan shekara ta hudu fa a wannan halin."

Can karkashin gado ya duka ya dauko wani akwati pin ya saka ya bude bandir din kudi ne cire a cikin akwatin, dubu d'aya ya dauko a ciki don duk ƴan dubu dayan ne a ciki, rufewa ya yi, ya yi addu'a sannan ya tottofa a jikin akwatin ya maida karkashin gadon wanda haka yake yi duk lokacin da zai dauki akwatin.

Falon ya dawo ya tadda su suna maganar su, suna ganin shi suka yi shiru, dubu ɗayan da ya dauko ya mikawa Sa'adatu ai nan da nan Samira ta ce
"Amman ai nice da girki ko?"

"Na Sani amman kar ki manta ita ce uwar gida na wacce take zaune dani duk da babun nan, kuma take rike min ya'yan na wanda nasan ke da wuya zaman da muka yi da ita ki jure mu zauna tare."

Ya kalli Yaya Babba ya ce "Ki bawa Auwal ya siyo garin kwano biyu nasan zai ishe ku har dare ko? Watakila har gobe da safe ma, sai a siyo muku siga in kuma kuli kuli zaku siya dai gashi nan dari biyar na yadda a dauka a ciki Dan na fada muku itama bashi na ciyo."

Karba Yaya Babba ta yi tana fadin
"Allah Kara budi."
"Ameen!"
Ya fada ya saka kai ya fice.

Bayan sa Yaya Babba tabi a tsakar gida ta tadda Auwal ɗan shekara goma sha biyar ta ce
"Auwal zo ka siyo mana garin kwaki kwano biyu sai ka taho da kuli kulin saba'in da gishin ashirin  sai a baka canjin dari biyar da tamanin."

Amsa ya yi da gudu yaje ya siyo ya dawo nan da nan Yaya Babba ta hau hadin kwadan wanda, daga zallar garin sai dan 'kuli-'kulin da kamar ba a saka ba sai dan banzan gishiri kanar zai yi magana ko arzikin mai bai samu ba haka ta gama ta zubawa yaran a 'Babban faranti sanna ta zubawa iyayen su hudu kowa nashi, haka ƴan matan yaran ma ta zuba musu kowa nashi.

Zo kuga yadda ake cin wannan kwadon wanda daba kuli kuli sai gishiri kamar zai magana ne a ciki amman ci suke kamar suna cin kaza har da loma da abincin ya kusan karewa kowa sai ya hau dunbuza a hannun sa wanda har fada akai aka dau katon farantin aka kwadawa ɗaya daga cikin yaran akai akam take ta fara ihu don wajen lokaci  guda ya kumbura.

Yaya Babba da ta zama uwar kowa a gidan ita ta lallashe ta. Ƴan matan kuwa duk suna daki suna ci sai mita suke su wannan abin kamar suyi amai amman haka suke tura shi don in basu ci ba basu san yadda zasu yi ba.

*Wannan kenan, ba kullum zaku samu update ba sai  dai a sati sau ɗaya asabar ko lahadi ne  in kuma mun na samu dama zan na yin sa asabar da lahadin, ayi hakuri. damu*

Antty

WANNAN RAYUWARWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu