Chapter 1 page 98

223 17 2
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 9⃣8⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

Tunda ya fara magana take kuka, can ta mike tace
"Am sorry Kabir ba zan iya zama da kai ba."
Bai san lokacin da ya mike ba yace
"Whay?"

Kai ta girgiza tace
"Kayi hakuri amman ba zan iya ba."
"Saboda me?"

"karka manta ka san wacece ni kasan me na aikata. Nasan ba zaka taba manta wacece ni ba kuma a duk lokacin da kace zaka kusance ni zaka tuna wacece ni wannan zai sa ka tsane ni. Tayaya kake son zama dani bayan ban dace da kai ba. Daban kake ba zan lalata maka rayuwa da zuria ba."
Tana fadar haka ta fashe da fashe wani irin kuka mai cin rai.

"Halima!"
Ya kira sunan ta amman bata amsa ba. Yace
"Halima abinda yafaru dake fa kaddara ne ,kina nufin ke kika tsarawa kanki rayuwa, ni nasan badan Isma'il shu'umi bane Yakuma yi amfani da San dakike masa ba, da ba yadda za ayi yaci galaba akanki, saboda haka karki damu, badan kin tuna min ba ma yanzu namanta da komai a tsakanin ki. Na dauke shi a budurwa ta ne,  burina arayuwa in ganki cikin farinciki da walwala, kuma duk ina wannan abun ne danke."

"Tayaya tayaya? Ina tantamar wai kana so na. Gani nake kayi haka ne dan kana tausayi na."
Durkusawa yayi yace
"Wallahi Halima a magana ta babu karya. Wallahi ina son ki "

"Ita kuma amaryar ka fa?"
"Itama ina son ta."

"Wa ka fara so a cikin mu?"
"Ke!"

"Dan me ka so ta daga baya dan kaga na rasa mutunci na "
"Ki daina fadar haka na fada miki zan iya rayuwa dake a haka ba tare da munyi sex ba ni ba shine a gabana ba na kasance dake shi nafi kauna. Sadiya kuma ganin na rasa ki yasa na fara son tai tama kamar ki take tana da sanyin hali dan haka ki nutsu ina son ki manta da komai,  ki manta da kin taba haduwa da Isma'il, ki bani dama na shiga rayuwarki, kisoni ko yaya ne mu gina rayuwarmu cikin so da kauna please!"

Dagowa tayi tana kallonshi. Ya hade hannaye yace
"Please Baby! kin amince?"
Kai ta gyada masa. Baki ya washe, ya karaso ya rumgume ya a jikin sa wani bakon abu suka ji dashi har ita.

"I love you my love!"
Ya fada yana kissing wuyan ta. wata kunya ce ta kamata ta fara sunne kai. Sakin ta yayi tai saurin juyawa yai murmushi yace
"Oh yau ni ake jin kunya Baby!"

Ta make kafada yace
"Zama ki daina ne. Muje muyi alwala muyi sallah ta godiya ga Allah."
Ya kamo hannun ta yana shafa cikin ta yace
"Wannan cikin ba abinda yaci."

Ya kamata sukayo alwala. Wanda suna dawowan sukai sallah ya zauna ya ciyar da ita. Sannan suka haye gado. Ya rufe ta take bacci ya dauke ta. Shima yayi alwala bacci ya dauke sa. Cikin darr ta tashi da wani ciwon kai da zazzabi ga ciwon ciki saboda rashin abincin da bata ci ba na kwana biyu.

Haka tai tayi masa kuka wanda wajen asuba sai da suka je asibiti. Karin ruwa akai mata har asuba bai kare ba. Sai karfe shida ya kare aka kara saka mata wani wannan yasa Kabir ya kura Sadiya ya fada mata suna asibiti. Tace to gata nan.

Kan ta gama shirya musu abinxi ma an sallame su an bata magunguna. Sadiya na kitchen taji dawowar su  kan ta fito har sun shige dan haka ta koma ta karasa komai ta shirya musu tai wanka ta nufi sashen nata.

WANNAN RAYUWARМесто, где живут истории. Откройте их для себя