Chapter 1 page 67

122 12 2
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 6⃣7⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

Abbah yace
"Ya zancen kafi Muhammad nace za aje a yi a gidan da na baka kace a dakata."

Kai yayi kasa dashi yace
"Haka ne Abba daman ina can nake aiko da kudi ana min gini anan to shine yanzu ma daga can nake an gama komai a jiya shiyasa nace a dakata. Kuma Abbah ina neman wata alfarma dan Allah."

"To masha Allah hakan ma yana da kyau ai. Allah sanya alheri."
"Amin!"

"To wacce alfarma kenan?"
"Abba daman so nake a bani dama na zuba kayan cikin gidan ba sai anje wani kafi ba ni zanyi."

"A'ah A'ah Muhammad haka ma ya isa,  kaya an riga an siyo dan haka kayi hakuri kawai Allah yayi albarka."
"Amin to Abba na gode yaushe zan kai ka, ka gano gidan?"

"Sai wani lokacin Muhammad!"
Hannu ya zura a aljihu ya ajiye keys din yace
"To ga makullin gidan nan sai a fadi lokacin da za aje kafin zan aiko motoci."

"Haba Muhammad ai wahalar sai taimaka yawa."
"Dan Allah Abba kada kace A'ah ka bari kawai azo a akai su."

"To shikenan Allah ya kaimu gobe ne da safe tinda kaga a gobe zata tare kamar karfe tara sai su tafi ayo kafin."
"To Allah kaimu."

"Amin! Su Umma na ciki zan shiga na gaishe su."
"Suna nan muje na rakaka."

Suka mike Abba na gaba Muhammad na bin sa a baya har falon Umma dake zaune suna ta lissafi. Tana ganin sa ta mike tana fadin
"Ah Muhammad an dawo ashe."

Ya durkusa yace
"Eh Umma ina yini mun sameku lafiya?"

"Alhamdulullah!"
"Masha Allah! Yasu Hajiyar taka?

" Tana lafiya. Tace agaishe ku"
"Masha Allah muna amsawa."
Sannan yace
"To sai anjima."

"To ka gaishe ta da yaran!"
"Zasuji nagode!"

Suka nufi dakin Mama dake zaune tana waya. suna shiga ta dinga binsu da kallo dan ita ta kasa gane Muhammad ma. Sai da ya gaishe ta sannan Abba yace
"Muhammad ne mijin Ummu fa."

Fuska ta bata tace
"Oh ashe ya dawo!"

"Ya dawo dazu!"
"To madallah!"

Ya mike yace
"To sai anjima."
"Mujima da yawa!"

Suka fito. Ya dan rissina yace
"To Abba ni zan koma."

"To Muhammad ka gaishe da Babar taka."
"Zata ji."

Har ya juya Abbah yace
"Zo!"
Ya dawo yace
"Baka ga Ummu ba ko?"

Yai kasa da kansa ya kasa magana. Abbah yai murmushi yace
"Tana gidan Zainab nasan gobe zata dawo nima tinda ta dawo sau daya na ganta Zainab ta kwance min 'ya."

Muhammad yace
"Ba komai Abbah nagode."

"To ka gaisa gida!"
"Insha Allah."

Ya fice. Gidan Anty Zainab ya wuce kai tsaye bayan yai parking yaran suka taho suna ganin sa suka hau fadin
"Oyoyo Uncle!"

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now