Chapter 1 Page 82

193 14 1
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 8⃣2⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*

*FATIMA MUHAMMAD SANI (ZarahArkel)*
*HALIMA MUHAMMAD SUNUSI (Barrister S@dy)*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*Hakuri da Juriya Online writer's (HAJOW)*✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Dedicated to *Hakuri da Juriya Online writer's Fans* (Allah bar zumunci da kauna)
Wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin masoyan Association din mu wato *HAJOW*

*
Tana shiga gida suka wuce dakin su. Kwance ta samu Halima. Tace
"Tashi kici abinci ki sha magani!"

Ta kalli Sakina tace
"Kawo mata abinci!"
Ta mike ta fita. Tace
"Halima ki rufawa kanki asiri ki cire damuwar wani da namiji akan tunanin yaron nan nasan shi kika saka a ranki duk ya janyo miki haka. Haba Halima shi yana can kila ya manta da ke,  amman ke kun sa damuwa a ranki."

"Anty nima ba shi naket tunani ba."
"Me kike tunani to?"

"Anty nayi babban laifi ga Allah dan gaka dile nji tsoron haduwa ra dashi wannan ke.kara saka min fargaba da tsoro a raina."
Tai murmushi tace
"To naji sai me?"

"Anty a *wannan rayuwar* wa zan aura? Wa zai soni?"
Kai ta gyada tace
"Dole kiji tsoron haduwar ki da Allah domin kowa ma.yana jin tsoran haduwar sa dashi ta yadda zaki ji saukin haduwar ki dashi shine ta tuba da yawaita istigifari abinda kikai ki roki Allah ya yafe miki sannan ki tsarkake zuciyar ki ki mike da bautar Allah. Allah gafuru haramin sai kiga ya yafe miki.
Abu na biyu in har kika mika komai ga Allah a sannu komai zai zo miki da sauki,  kina zaune Allah zai kawo miki miji na gari wanda zai rufa miki asiri. Ba a cire rai da rahamar ubangiji."

Hawaye ne ya zubowa Halima. Fauziyya tace
"Dan haka ki daina saka damuwa in damuwa tai miki yawa kika mutu baki gama rokar Allah yafiyar ki ba. Kina rokan Allah ya baki tsawon ran dazaki na masa ibada ba ki mutu ba."

Ta dafa Halima tace
" Dan Allah ki daina saka damuwa ina tare dake kuma zan shige miki gaba a komai. Da so nayi a hada dake da Hafsa da Sakina har ma da Hajara ai muku aure amman zamu jira muga me Allah zai yi kila ka lokacin dukka kiga kema Allah ya kawo miji miji na nunawa sa'a. Kiyi ta addu'a da tuba Allah ya yafe miki."

"Nagode Yaya Fauwaziyya hakika samun ki a matsayin Yaya ya fi min komai. Kin zama mana uba da uwa da katanga Allah ya jara girma yasa ki gama da duniya lafiya Allah rufa miki asiri ya baku zaman lafiya ya kawo ya'ya masu albarka nagode Yaya."
"Kada ki damu kanwata. Ba godiya a tsakanin mu in ban muku ba wa zanyi wa?"

"Haka ne amman dole nayi"
Sakiata shigo ta ajiye mata abincin tana fadin
"Ai kuwa dai mungode gashi ta dalilin ki zamuyi aure dan in ta Baba ne ai mu mutu ba aure."

"A'ah ba haka bane gani yake kawai ba mu girma shima rashin zama tare ne yasa hakan."
"Ke bakya ganin laifin babane kawai."

"Mahaifin mune fa."
"Amman shine ya jefa mu ga fadawar ga halaka ko?"

"A'ah fa shine sila dai. Amman wannan jarabawar muce. Kuma a yanzu neman yafiyar Allah muke shi da mukaiwa laifi to dan me bazamu yafewa Baba ba. Dan Allah ku yafe masa"
"Uhmm!"

Suka fada gaba dayan su. Haka ta dinga tausar su har ta bawa Halima abinci taci ta sha magani ta kwanta.

Karfe tara yazo ya dauke ta suka tafi. A hanya ya tsaya ya siya musu Yahuza suya sannan suka wuce gidan su. Suna shiga tayi dakin ta ta cire kaya ta shiga tai wanka. Wasu kayan bacci ta saka masu kyau sosai. Tayi lighy make up ta fito a Fauziyya :eauty din ta. Falo takoma ta zauna tana kallom TV. Wanda azahiri TV take kalla amman a badili ba shi take kalla ba tunanin rayuwa kawai ta.

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now