Chapter 1 page 38

226 39 0
                                    

*WANNAN RAYUWAR💐💐💐*
Based on true life story

Chapter One
page 3⃣8⃣

By
*MARYAM SULEIMAN INDABAWA (Antyy)*


*_WA NAKE SO?_ Kayataccen labari mai cike da salon soyayya kala kala. Ni me ma zance ne ta ina zan fara ne? Hmm kawai kuje ku neme shi dan jin wane kalar sakon. yake dauke dashi.*

*
Bayan kwana biyar Fauziyya da Hafsat na zaune Arfat ya shigo da gudu ya kalli Fauziyya yace
"Anty Wai kizo a waje?"

Kallon sa take da alamar mamaki dan ita har ta fitar da rai da zuwan Muhammad dan haka bata kawo shi bane shiyasa tace
"Je kace wanene?"

Ya fita ai jima ba ya dawo yace
"Wai Muhammad ne."

Ai bata san lokacin da ta mike ba. Kallon ta Hafsat tayi sai ga hawaye a idon Fauziyya mikewa Hafsat tayi ta dafa tace
"To menene na kukan Anty?"

"Hafsat yau fa kwana bakwai ba shi ba alamun sa. Hafsat tsoro nake kar yace ya...."
Sai kuma tayi shiru.

Hafsat tace
"Anty ke fa kike bani kwarin gwiwa akan irin wadan nan abubuwan dan Allah Anty ki daina kuka ba abinda zai faru sai alheri."

Hawayen ta fuskar ta Hafsat ta hau goge mata nan ta dauki Hijab din ta ta saka ta fita.

Tsaye ta same shi cikin wata maroon yadi dinkin riga da wando ne yai masa kyau sosai kyan sa da hasken jikin sa sun kara fitowa. Yai wani fresh dashi alamar bai da damuwa yana cikin jin dadi. Fuskar sa dauke da murmushi. Hannun sa sakale da golding kalar agogo kan sa ba hula gashin kansa ya kwanta luf luf dashi.

Kallon sa ta tsaya yi Muhammad kyakyawa ne dan yana da manyan idanu sanan yana da dogon hanci siriri kuma bakin sa madai daici ne. Yana da saje da ya zagaye fuskar ya dada mata kyau da kwarjini sai sheki yake yi. Dogone bashi da kiba. Ganin shima cikin kwayar idon ta yake kalla yana murmushi yasa ta dauke idon ta daga kallom sa.

Matsowa yayi kusa da ita yadda har suna jin fitar mumfashin junan su. Kan ta a kasa ta kasa dago shi. Hannunsa dake harde a kirji ya zare ya dago fuskar ta. Hawaye ya gani yana gangarowa daga cikin idon ta nan da nan cikin tashin hankali ya fara magana.
"Ya salam Fauziyya me ya faru ni na bata miki rai?"

Cikin kuka ta daga masa kai. Shiru yayi yana kallon ta yace
"Naji amman dan Allah daina kukan nan ki fada min me nayi? Amman ki daina kukan wallahi baki ji yadda nake ji ba a cikin zuciya ta."

"Ba kai bane ka tafi ka barni ba ko waya bare kazo?"
Ta fada tana turo baki. Murmushi Muhammad yayi yana shafa sumar kansa yace
"Ba zan baki amsa ba sai anjima da dare in kina jiki na."

Ido ta rufe da hannayen ta dan ya bata kunya. Hannun sa ya saka ya zare hannayen ta yace
"Menene na kunyar yanzu fa ni mijin ki ne. Ina fatan kin shirya tahowa waje na da soyayyar ki kala kala."

Shiru tayi ya kalle ta yace
"Nayi kewar ki Fauziyya yadda baki ba zai iya furtawa ba sai zuciya ce tasan halin da na shiga kawai! Ina fatan kina lafiya?"

Baki ta turo taki magana yace
"Naji anjima zanzo na amshe ki dai daga wannan gidan!"

Dagowa tayi tana kallon sa. Yai murmushi yace
"Eh mana ai na dada miki kwanaki ma inajin ko?"

"Wai yau zan tare!"
Kai ya gyada tace
"Amman ai ban sani ba."

"In kin sani me zakiyi."
Juya masa baya tayi tace
"In maka ado mana!"

Murmushi yayi dan yana son Fauziyya da kunyar ta. Yace
"Wane irin ado kuma? Fauziyya ni a haka ma kin ishe ni fadan wane irin ado?"

"Lalle da gyaran kai fa."
"Kizo min a haka ma ni na fiso da kai na zan kai ki inda za a gayara min ke kinji ko?"

WANNAN RAYUWARWhere stories live. Discover now